Sashe 205
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dan shirune ya biyo baya a wayan kafin cikin muryan mamaki shi Ahmrd din ya kawar da shirun ta hanyar fadin mahaifina mahaifina fa kace ? Kwarai kuwa ko kana maki hankane dana nine dai Alh, , , , look malam kake ko Alh idan ma ka kiranine don ka zolayeni ko wani abu ka batawa kanka lokaci a yanzu bani Ahmed ba. Don haka ka bari saboda ni na dade da rufe wanan zancen a zuciya don dai ni Ahmed nasan banda uba a duniyan nan ko ina dashi kuma ya dade da barin diniya a wurina. Don kowa yana da shedan hakan kuma a hakan jama,a suke daukana suna min kallon mutum mara asali a cikinsu don haka kada ka zolayi kanka ka zolayeni a yanzu da wanan sunan na kaine mahaifina. Don haka kada ka kara kirana ko kuma layina idan ba haka ba zan maka abinda baka taba zatoba a rayuwanka don hukumace zata rabani da kai.. Yana fadin hakan ya kashe wayan nasa a hasale tare da mikewa daga inda yake zaine din yana shan iska a cikin bacin rai da be taba jin irinsa ba. Tafiya yake zuwa dakin shi na masaukinsu yayin da wani irin mamaki ya lulube ziciyanshi lokaci guda duk da yasan ko waye mai kiransa din a lokacin. Amma abin mamakinsa shine a ina ya samu layin nasa har ya kirashi a ranan shine mamakin dake ci masa zuciya don yasan banda zahransa ba wanda yake da layinsa a Nigeria to a ina yaga zahra din ya karbi layinsa din ? Shima Alh bai taba zaton hakan a gareshi ba don ya dauka dan zaiyi farin ciki dajin shine a ranan sai yaji sabanin hakan gareshi take mamaki ya lulubeshi. A karshe ya gane cewa dan nasa jarumine na sosai don haka akwai sauran aiki a gabasa ke nan da zai fuskanta nan gaba gun dan nasa duk da bai dauki hakan a wani matsala babba ba . Yadai kashe wayansa yana mamakin jarumta irin na yaron a lokacin koda yake kila bai gama fahintar shi bane oho idan yasan koshi waye dole zai dawo hanya yabi ai . Nima dai tun bayan tafiyan nasu na koma wata irin mara lakka dani ina faman tunanen abubuwan da suka faru haka da wanda zai faru din don nasan master ba mutum bane mai saukin kai lokaci guda ba. Bani kadai ba don ko inna da Dije na hango damu a fuskokinsu tun zuwan bakin namu saidai bansan damuwansu ba su na daifi tsanmanin zuwan nasune ya mayar dasu din haka. Don hakanema na shige dakina na kwanta zakice barci nakeyi a lokscin amma idona biyu gidan ne kawai ba dadi a ranan garemu . Shigowan Aisha take fada min dije tana magana dani wurinta hakan yasa na tashi naje lokacin karfe takwas na dare anyi sallh isha,i ke nan na ranan . A tare muka jera da ita bayan na rufo part dina don ban faye fita da dare ba zuwa cikin gida master kuma ya gargadeni idan zan shi cikin gida na dinga rufe kofa hakan yasa na jawo kofata na rufe muka shiga. A tsakar gida na samu inna zaune ita kadai tayi tagumi tana zaune daga ita sai dan farin vest a jikinta mai siririn hannu ta kurawa waje daya idanu jin sallamana yasa ta dago tana sauke ajiyan zuciya ta amsa min a sanyaye. Gaida ita nayi da wuni a sanyaye ta karba zakice wani abin yana damunta lokacin ban tsaya ba tunda ba dogon hira nakeyi da itaba dama na shige wurin dije mm a sameta a zaune daga kofa. Dan buhun abincinsu dake gefe daya a dakin dan dama a dakin nata ake ajewa sai za a dafa aje a diba ya fada don kullun cikin cinsa ake nan nakai zaune ina gaida ita da wuni. Ta amsa min cikin jan zuciya saida naga ta leka kamar bata son aji me zata fada a lokacin ina dai kallonta tace dani karbi kudin nan ki kirga min su kinji . Don ban yarda da yan banzan yaran nan ba suna iya biyo dare suzo su sace min su kuma uwarsu ta hana ayi magana idan taji na mika hannu na karbi kudin na fara kirgawa har nakai karshe. Na dago kai nace dubu darine Dije da sauri ta kalloni tana fadin dari yar nan har kin kirga da kyau ko kin gani nifa dana gansu a haka na dauka ko ashirin ne ? A,a darine na fada ina miko mata tace a, a ki ban goma kawai koshi don inbawa abokan arzikina irinsu mai fura da mukai zaman arziki dasu suma su sheda baiyanan mahaifin mijiki garemu. Murmushi nayi kafin nace ba zaki sayo abin dadi kitaci ba Dije don haka ya baki da yawa fa itama dariya zancena ya bata don naga ta washe baki kafin tace. Wani dadi zanci ai ajesu zanyi har mijinki ya dawo jn mika masa su ko yaji dan saukjn yi muna cefane kinga ai a kara ko tunda Allah ya kawo muna su har gida. Hakane amma dai koshi ya dawo nasan abinda zai fada ke nan ai tace bari yar nan ina tausayin yaron sosai wallahi muci musha muyi tufafi duk a jikinsane kuma baya fushi da hakan. Ga ita wanan taki mayar da yaran nan ga dangin ubansu ta kwaso ta kawo mashi sunan yana bakar wahala dasu yan banzan yara tundai ace Asamaun nan ba ma,u arziki bace sam. Wata kila yarintane ke damunta zata zo ta bari ai ta barme yarinya haka da rawan kai don mashi Amadi ya zamo namijim gaske aida ba karaman tantiriya bace. Duk irin taurin kan uwarsu ta kwasoshi dan haka itama lokacin nan ta kafe sai habu fari take so mutumin da baida komai bai kuma da kowa a garin nan. Ni kin sani ance dare daya Allah kanyi bature ba abinda ya tsaya min a rai sai arzikin bawan Allah nan mahaifin ku don wallahi da can baya ko sadaki saida akai mai tarbace aka hada mashi su. Amma yau shine yazo gidan nan a matsayin attajiri da mutane ke binsa a baya haka duk da ance kudin yanzu basu da wuyan nema amma da alama a yanzu shi din wani hamshakin mai kudine. Dama dije haka Allah kanyi ikonsa ga bawa sannu a hankali za a gane dalilin kudin nasa nan gaba ai amma mutum ya tashi haka ba kudi aganshi dasu da rana tsaka gaskiya abin tambayane ga mai hankali tace aishi nagani. Amma kinga mara hankalin nan tun dazun ganin mijin nata a yau yasa duk tabi ta sukurkuce ga baki daya Allah na tuba a yanzu yadda yaken nan ko a kafa aka daura mai Rashida me zaiyi da ita kuma ? A, a haba Dije inna ba mace bace kuma matarsa aishi zai gyarata tunda akwai kudin aiki mukan ai muna son su koma gaskiya in hakan zai samu su koma din. Wace don ni ina jin ko ganetama baiyi ba don shi a haukace yake da son ganin dansa bai tsaya tambayan wata Rashida ba can don haka wahalan rayuwa kawai take son dorawa kanta. Don itama tasan a yanzu yafi karfinta sau dubu ko makaho ya laluba yasan haka kawai yanzu ni bansan da wani tsiga mijinki zai tarbi mahaifin nasa ba idan ya dawo. Ni Umma bance ina tunanen hakan gareshi ba damuwata damuwatace nina nasan abinda nake tunane muryan innace daga inda take take bamu amsa. Koda muka rabu dashi aiba fada mukayi dashi ba ko wani abu kawai dai kaddarace aita rabamu a lokacin ba wani abu ba. Kinji ko dama aina fada maki kina wani tarewa wai kuma kuna son hakan ya faru take fada min daga can inna din ta sake fadin umma bashi yayi kansa hakan ba yanzu Allahne yayisa. Ko ya tambayeni ko kada ya tambaya duk dayane a gareni don na masa abinda kowa bai masa a baya can to me zai dameni a yanzu kuma ? Mikewa nayi da niyar fita daga dakin ganin inna ta dauki maganan da zafi a zuciyar ta lokacin don yadda take halako ya nuna cewa ranta ya gama baci sosai a lokacin. Nakoma part dina na samu wayata da misscall dinshi nayi shirin kwanciya ya kara kira na dauka yake fadin ina kika shiga waya keta ringing tun dazun baki dauka ba ? Nace ina wuri Dije muna hira nabar wayan a daki waya karbi layina a hannun ki ya tambaya ba tare daya tsaya mu gaisa ba ko yaji ya lafiyan mu take ya jefo min wanan tambayan. Sam na manta da zancen mahaifin shi ya karbi layinsa din nace number ka kuma wa zanba layin ka kuwa sai zancen mahaifin nasa ya fado min take a zuciyana. Nace da sauri oho na manta mahaifinka sunzo yau shiya karbi layin a hannuna da zasu tafi sai naji yace da sauri why zahra da zaki bashi layina ? Mema yazo yi wurina a yanzu da ban bukatanshi ko kadan yanzun ne zaisan dani bayan na gama wullakanta a cikin mutane an gama goranta min da barina da yayi yayi tafiyanshi yanzu ya dawo yace shine ubana kuma. Kai wani irin musulmine da baka yarda da kaddarankane master abin nan ya fada da bakinsa yayi laifi don Allah ku yafe mashi koda ace bashi bane mahaifinka ai ya kamata ka yafe masa din. Ke zahra ya fada a cikkn wani irin murya da bansan yana da itaba yake fadin ki tsaya matsayinki kada ki kyatara layin da baki da hurumin shigansa daga yau sai yau akan wanan zancen. Kayi hakkuri na iya furtawa a lokacin dkn nasan yakai iya hasala da zancen a yadda yake maganan dani lokacin. Daga yau sai yau kada ki kara ba wani layina idan bani nace kiba mutum ba nace naji na kashe wayan na lafe a saman gadona ina tunane a lokacin. Bai kara kitana ba tsawon kwana biyu da hakan ya faru tsakanin mu nima dama ba zan iya kirasa ba sai idan ya kira din Monday muka shiga school. Nan nake fadawa hannatu zancen zuwan mahaifinshi din tare da yadda mukayi dashi ta waya kan numban dana bashi din