← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 286

Sashe 119

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

tsaye ga mijin a zaune bai iya furta komai ba a lokacin don yanayin da yake ciki. Meke faruwa da kaine haka Alh ta mayar da tambayanta kan maigidan nasu dake zaune saye da doguwar jallabiya a jikinshi ya zauna ya mike kafafunshi duk da yana cikin wani hali hakan bai hanashi kamshi turare ba sai dan karamin tasbaha daya rike yana ja a cikin zuciyarshi lokacin. Kai ya dago ya kalleta kafin ya daga mata hannu yana fadi da kyar kije ki huta zaifi ke kuma aje min abincin idan na tashi yanzu zanci. To matar ta biyu ta amsa dashi kafin ta kwantar da murya tana fadin Dan baro na waje yana sallama dakai shida jabbi a kofan falo OK har sun iso ke nan ya fada yana mikewa da sauri kamar bashi ba a lokacin. Kowa part dinshi ya nufa zuciyar shi cike da zargi akan halinda mijin nasu ke ciki a lokacin na tashin hankalin da yaki fadawa ko dan dama ita hjy Indo dake gari abin ya faru. Amma ita hajiya Ni,ima da take wurin tafiyan bata san komai ba a yanzu sai zargin abubuwa da dama da takeyi a zuciyan ta lokacin. Tunane take waye wanan din da Alh ke tunane akansa haka kardai zancen sanda ya zamo ba daidai ba gareta Alh ya sadu da danshine wurin sakaci irin nasu har hakan ya faru ? In ko hakane ashe kashinta ya bushe a gidan nan ke nan don tasanda abubuwa da dama zasu iya faruwa a cikin lamarinta ke nan a yanzu tunda anfada mata ka idan abin kuma ta yarda da hakan . Sam bata taba tunane ko zaton cewa maigidan zai iya sake wanan yaron nasa a ido ba kuma duba ga irin shekarun da aka kwashe babu wanan zancen . Don har diyansu sun taso sun zama wani abu yanzu a cikin rayuwa tana ganin cewa lokaci yayi da zata gaje gidan ita da yayanta da yan uwanta da suka tsaya mata komai ya tafi daidai. Amma yanzu zuciyarta yana bata cewa duk wanan abubuwan suna kokarin wuceta idan ba Allah ne ya gyara lamarin nata ba kam. Alh munyi iya bincken mu mun kasa gano waye wanan yaron kuma daga ina yake wanda ma ya sanshi ko yasan a inda yake zaune bamu sameshi ba gaskiya. Murmushin kasaita mai kama dana takaici ya sake lokaci guda yana fadin amma Jabbi kasan dai yaron nan dana gani ba aljani bane da zakuce ya bata a cikin garin nan. Ba haka nake nufi ba Alh Jabbi din ya fada a ladabce yana sone kai kasa yace muna dai kan binciken hakan in sha Allahu zamu gano komai a kanshi da yardan Allah. Shiru sukayi na dan lokaci kafin Alh ya fara mikewa tsaye saida yaba da baya kamar zai shige ciki yace ina mamaki da jiya zuwa yau za a ce an kasa gano inda wanan yaron yake a cikin garin nan. Daga haka yasa kai ya shige ciki ya barsu nan a zaune suna mamakin sauyin da suka gani wurin aminin nasu kuma maigidansu abokinsu tuna tasowa da har yanzun basu yada junan su ba suna tare. Saidai sun san cewa shidin ba mai fushi bane irin haka alama ya nuna ke nan zancem wanan yaron yana da muhinmanci sosai a wurin maigidan nasu. Nan suka mike kowa ya nufi inda yake tsamanin samun labari akan yaron da sukayi siri da maigidan nasu kan a nemo masa shi kota halin kaka a kawo maishi a gabanshi. Kukan da akuyoyin keyine ya sa Dijen fitowa daga daki don ta dubasu saidai tsoro da tashin hankalin abinda ta gani yasa ta ja baya da sauri tana fito da ido waje tace . Uwar garke kene a gidan nan kuma ni Dije naga abinda ya tsoratani akuya kamar mutum saiki tafi sai lokacin da kikaga dama mu ganki kwatsam kin fado muna gida. Uwar garken da kanta ke done a cikin kaskon da ake zuba masu ruwanshan su tana zukan ruwa zakace tayi tafiyan mai nisa don yadda take durawa cikinta ruwa a lokacin. Kururuwa zatayi ko sulalewa zatayi a cikin gidan taje neman taimako a makwabtansu azo a gane mata abin mamakin datake shirin gani kota gani a gidan. Akuyan da tayi wata nawa bata gidan Amadi kafin shima ya bace yayi neman akuyan bai ganta ba haka ya hakkura da nemanta har shima tashi ibtila,in yazo ya sameshi daga baya. Tasowan ta ke nan kwana biyun nan ta dan fara jin karfin jikinta har tana da fitowa tsakar gidan nata tadanyi wani abu don rashim jikin nata har damuwan hakan takaita kwance a gidan. Wazata kira ta sheda mai yanzu malam tanimune da kunnuwanta ba wani ya tsegunta mata zancen shi ba akan jikan nata da yake sakewa a bayan idonta ita da kantane Allah kawota ta tsurashi yana fadin maganganun da basu dace ba ga jikin nata lokacin. Don haka kuma sai taga ai gara taja bakinta tayi shiru kada kuma a kara chamfa masu sabon zargi bayan wanda take fama acikinsa na batan jikan nata yanzu kuma. Tuna shawaran makwanciyanta tayi kan ba komai ake fadawa mutane ba yanzu don mutane basu da tabbas a yanzu lalaikan ta sheda hakan ita don bata taba zaton cewa Tanimu zai iya sukan ahalinta a wani wajen ba ai. Tun safe muka kama hanya kamar yadda mukazo garin iya mu muka dauki hanya nasamu nayi sallama da maryam munyi musayan lamba da ita. Nan Allah ya taimakeni dana tafi bamu karbi layin juna ba don ba wanda yasan da cewa zamu koma a ranan zaune nake kawai a cikin motan ina tunanen abubuwan da suka faru wanda a yanzu na sani aka mommy din da bansan dasu ba a baya. Tabbas dakan bata san waye wanan matar ba amma yanzu zuwa gidan su yasa ta kara fahintar cewa bata shigo gidansu da zuciya daya ba ashe. Ita kan a gobe zata koma gusau wurin mahaifiyata ba zata yarda ta kara wasu kwanaki ba a gidansu na Abuja din kuma. Ba wanda yai mata magana a motan don kusan duk sun sharetane ma za ace don ba wanda ya nuna ma kulawanshi a kanta kamar yadda itama din suke mata kallon karamar yar iska mai shegen wayau da jin kai da nuna isa da gadara don hakan da take masu sai ya saka wani dan shakunta a zuciyar su. Don da watace tayi masu wanan iskancin dasun nuna mata cewa bata isa ba amma yanzu a matsayin makami take a wurin su don suna sonyin amfani da daman su yagi mahaifinta ta hanyar ta. Wai har yanzu Zahra fushin ake da mommy ne kome hjy karima ta fada acan gaban motan inda take zaune din don ta kawar da komai dake tsakaninsu kada su isa Abujan haka da ita. A bazata zancen yazowa zahran har ta dan juyo tana fadin lah fushi kuma mommy ni bana fushi da kowa wallahi . Kina fushi mana zahra son tun jiya baki sake jikin ki ba kina faman daure fuska ta dan murmusa tace a,a mommy kawai dai gajiyace yasa kika gani haka don ban faye shiga mutane ba ni haka nake ko a gida. Jin hakan yasa ta dan kama janta da hira ita kuma zahra din tana da biyewa tana bata amsa bayan kar take kallonta da mamakin halaiyanta fam a zuciyar ta. Ko ta mata da cewa ya mace tun tana kankanuwa take fara fahintar wasu halaiya na zamantakewa oho. A haka har suka isa gida inda suka samu cewa yaran Alh sunzo maza daga kasan waje hakan sai yaiwa zahra din dadi sosai ganin yayyen ta musa da Jafar a garin har su biyu.
Chapter 119 · 0% Book details