← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 286

Sashe 6

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don Allah kada kiyi gangancin maryar da novel din nan audiovisual na riga da na sayarwa S ZARIA HAUSA TV idan wata ta karanta audio din shi hukumace zata rabasu da maishi nagode. Da sauri ya biyo bayan maishi don jin dalilin aika mai da abincin da kudi duk da baya raba daya biyun cewa fadan da madam tayi mai a bainan jama,a ne ya jawo hakan. Tunda ta fada a kunnen kowa cewa ba zata biyashi kudin aikin ranan ba haka kuma yasan da sanin baida abinci a ranan hakan na iyasa mai tausayi da imani ya tausaya mashi duk da bayau aka fara mai irin cin fuskan nan ba ai. Aikin wahala kowa yasan da yana yin shi a shagon madam tun baikai hakan ba saidai kuma haka bai hanashi ci gaba ba ga karatun shi don kusan shine kurun ajinsu dake zuwa na daya aduk jerabawa idan suka zana. Wanda yasa mutane da yawa ke mamakin hakan saukin shi daya baya shiga harkan kowa kome yakeyi wanan ya jawo mashi saukin wullakanci a idon mutane da basu gani basu maganta ba. Ita kanta madam ta sani cewa zai iya dakatarwa da komai da zaran lokacin daukan darasinshi yayi yaje aji sai ya gama ya dawo bakin aikin shi. Dan adam da keta da farko taso hanashi hakan amma ya jajirce yaki yarda da nufin ta don ya gane bata son cin gabashi saidai tayi ta more mashi ita wanda yasan karshe zai tashi a tutar babune ta gama moranshi a karshe kuma ta koreshi. Mutane da yawa suna mamakin hakan gareshi ace saurayi kamarshi baya jin kunyar zama yana wanan aikin ko macece shi abinda kunya ace yana dan jami,a yana wanan aikin zubar da kiman shi. Sam shi bai dauki hakan wani abu ba tunda burin shi yana cika da sanu da sanu don idan ba hakan yayi ba ba wani wanda zai tausayawa rayuwan shi yace ya daukin laluran karatun shi a halin yanzu. Gashi a zamanin nan na rashin taimako kowa kanshi ya sani ba taimako ga al,umma ko tausayawa tallaka saidai ma kokarin ganin bayan ka koda baka kai karfin mutum ba zai iya hassada ga al,amarin ka ayanzu. Kallon kudin hannun nasa yayi dubu ukune da dari biyar ta bashi canji wai kyautane daga wace bai sani ba duk da yasan akwai na Allah har duniya ta nade nagari basu karewa a duniyan nan. Haka yaja kafa ya koma ciki zuciyar shi cike da zargi da kuma mamakin yin hakan dukda dai yana samun dan canji wani lokaci saidai basu kai haka din ba . Tun dawowana gidan ina kwance a dunkule dakina wanda ciwon kai dake damuna ya kaini ga kwanciya haka har baya magariba ummah taga ban leko ba yasa ta shigowa da zuman min fada. Saidai yadda ta sameni ne ya daga mata hankalinta a cikin dan tashim hankali take kiran sunana da kyat na iya bude idona da suka kade sukai wani irin ja kamar garwashi. Subbahanallahi maamaa meke damun ki haka kuma kai na nuna mata na mayar da kaina saman filo fada ta fara min da cewa wai meyasa kike wasa sa ciwo hakane maamaa ? Baki da lafiya ba zaki fadawa mutum ba sai kishige daki ki dunkule a ciki haka sau nawa zan fada maki bana son haka din. Fita tayi daga dakin sai gata tadawo dauke da magani da ruwa a hannun ta tana fadin tashi kisa panadol ko zaki samu relief amma ana zama da ciwo haka a jiki ? Ko motsi banyi ba ayadda nake hannu takai ta dan girgizani da sauri ta dauke hannunta saman jikin nawa tana min wani irin kallon mamaki. Fita tayi dakin ta nufi part din mama a rude tayi sallama mama na zaune da wata kawarta suna hira suka amsa mata tare da binta da kallo don tasa bata damu da shigo mata daki haka ba. Hjy maimuna mutumiyar kice ba lafiya tunda ta dawo school din yau take kwance bata fito ba shine yanzu na lekata don in bata magani ai jikin yayi zafin da ban taba jinshi ga wani mahaluki ba yadda jikin yayi zafi. Subbahanallahi mama tace tana mikewa tsaye tana inane ta fada a dan rude tana dakinta a kwance bari na dubata kafim na kira likita mama ta fada don itace mai kiran likitan mu gako waye baida lafiya a gidan. Ida mai karatu baki manta ba na fada maki komai na gidan mu yanzu mamace jan gaba dashi kasancewa mahaifiyar mu batayi boko ba. Kuma bata samu haihuwa da wuri ba yasa mama ta amshe duk wani ragaman gidan ya koma hannun ta hakan kuma bai damu ummah ba duniyace taje tayi ta kayan shi. Ina zuwa hjy karima mama ta fadawa kawarta dake zaune tana kallonsu kafin kuma ta juyo tana fadin taso dai mu tafi mu ganta ai dake. Dakin suka shigo lokaci guda ina kwance yadda ummah ta barni mama ta fara kiran sunana da maamah maamah meke damun kine tana kai hannunta a jikina taji zafin jikin da ummah ta fada. Da sauri ta jaye hannun tana fadin meye haka kuma jiki ya gashe kamar garwashi haka lokaci guda ta fada tana kallon su ummah da hjy karima dake gefenta tsaye. Hjy karima ta matso ta kai hannunta da sauri ta cire tana fadin meke damunta hakane jiki yayi wanan zafin kamar ba jikin mutum ba. Ku bata maganin maganin tasha mu gani mama ta fada dole ummah ta matso kusa ta tayar dani zaune ina kokarin komawa na kwanta cikin daurewa Allah ya taimaka na karbi maganin ina hadewa na koma na kwanta. Duk suka kura min ido na lokaci kafin hjy karima tace dasu anya yar ba iskokaine a kanta ba kuwa da sauri mama ta tare da fadin a a maamaah bata da komai ciwone kawai ya ziyarto ta., Allah ya sauwaka ta fada ta farayi gaba mama din tabi bayanta bayan ta dan kara yi ummah bayanin cewa idan maganin ya sakeni inyi wanka inci abinci kada ummah ta bari nakwana da yunwa ta juya tana sauke ajiyan zuciya. Godiya ummah tayi mata ta fita tana tambayan sauran yan uwana ummah tace suna dakinsu suba assignment ta fice daga part din namu ta nufi part dinta ta samu hjy karima. Kai mutumiyar kin dai tare gaba kin tare baya a dole wanan matar da diyanta su biki batace komai ba tayi murmushi kawai tana kaiwa zaune. Hjy karima ta kara fadan wanan yar taku tana girma kyauta na dada karuwa haka wanan ai da gudu wani kusan gwaunati zai bullo ya dauketa lokaci guda. Kun kusa zama sukan gwauna ko wani hamshakin maikudi a garin nan rass gaban mama yayi amma sai ta daure ta sake murmushi a fili kawai bata furta komai ba koda amin din munafuncine kuwa. Saidai ta dauko wani hiran suka somayi da kawar nata har zuwa goman dare data mike tana mata sallaman zata tafi dare yayi ta rakata har wurin motanta ta dawo. Zan iya fada maki cewa ke mai karatu gidan mu gidan rufin asirine gidane da mahaifin mu nada rufin asirinshi iya gwargwado da Allah ya bashi don tsonhon ma,aikacin hukuman kwastom ne na kasa da yai ritaya . Yanzu kuma ya fada harkan kasuwancin kasa da kasa tare da rike siya da karfin Allah yana da tittle a zamfara da ake kira da MAYANA. Wanda asalin yan garin suke kiran duk wani dan gidan mu da wanan tittle din na mahaifin mu tundaga waje zaki fahinci naira ya zauna a gidan namu. Duba da irin ginan gidan namu da irin motocin dake haraban gidan wanda duk wata mace da yarin gidan daya kai munzalim jami,a ana mika mai mota don bukatanshi na yau da kullun . Mahaifin mu yana da gidaje a garuruwan anan gida Nageria har wasu na fadin yana dasu a wajema saidai ni shekaruna bai kaiga nasan wanan zancen ko gaskiya ake fada ba a nan. Kamar yadda na fada ummah itace matsrshi ta farko daya aura saidai ummah batai boko ba wanan yana cikin dalilin koma bayan da umma din ta samu a gidan mu. Sai mama da kamar yar uwa take a wurinshi don suna da dangantaka da ita wajen ubananan su ita tayi boko har ta fara FCE a lokacin da sukai aure. Mahaifin mu ya hadu da mahaifiyan muce yar katsina lokacin dayaje bautan kasa a kaduna tana wurin kanwar mahaifiyar ta dake tasheta nan ya ganeta a unguwar rimi ya nuna yana sonta aka bashi ita lokacin tana da shekara goma sha shidda batai wani girma ba sosai ya aureta ya ajeta Gusau shi yana tafiya wurin aikinshi a can Lagos saidai ya dan kawo masu ziyara a lokacin. Amma shigowan mama gidan namu da kuma samun rabo da tayi gata kuma da alaka da mahaifin mu sai asanu da sannu komai ya koma hannun mama din da yanzu ita ke mulkin komai. Tun yan gulman gefe na magana kan yadda ake mulkan mama din har suka daina ganin ita bata dauki hakan a komai ba don ko haihuwa mama tayi itace ke kula da yaran har girman su sai idan sun fara wayone mamake rabata da yaran nata a cikin hikima irin na wayayyu kuma ta haifo wani ta danka mata raino bai hana ummah ta karba da zuciya daya ta rike matasu inda duk wani wahala da yaro zaiyi na goyo itace wahalan su a lokacin. Amma halin dan Adam lokacin da mama ta kyala ido taga ummah da ciki a fili ta nuna mata bakin cikin hakan saida wata yar uwanta ta fadawa uwanta ta tsawata mata tace . Amma idan kikai wa salma haka bakiwa kanki adalci ba matar da a tare kuke wahalan ciki da goyo agidan nan tare da ita don yau Allah ya tuna da ita ya bata nata rabon zaki nuna fushi gareta. Wallahi ki janye wanan gabar taku kada duniya tasan da kinayi a zageki don salma ta gama dake maimuna ta rikeki dake da diyan ki rikon Allah da Annabi me kuma kike nema gun kishiya wanda salma batayi maki ba a yanzu. Ai idan kinyi haka kamar kina fushi da ubangijin kine don
Chapter 6 · 0% Book details