Sashe 136
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ta lafiya da yardan ubangiji. In har ana gason hakkuri a duniya ai Zahara ta gaji hakkuri a wurin uwarta meya rage na hakkuri yanzun wanda bata sani ba kuma ai saidai wanda ba,ayiba a duniyan nan. Kowa yayi shiru sai cewan da gwaggon mu daya tayi ku tashi mu karasa gidan hjy kuyi mata sallama daga can zamu wuce daga can baya wata ke fadin su angwanan zahra sun kawo motan daukan amaryan sune. Aminiyar ummah hjy kubura ta bude baki tace ko basu kawo ba mota ba matsala bane ai shima angon yanzu ya zama dan mu da akwai motoci sai mu kaita fatan mu dai Allah ya basu zaman lafiya aka amsa da amin. Haka suka rikomu zuwa waje muka taka da kafa zuwa gidan hjy din nan ma irama tayi muna nata hudu ban mai kama da jurwaye tare da fatan lafiya gare mu aka kwasa akafito wajen gidan . Ina jin mommy kubura na waya cewa sauran su fito idan an shirya motocin tafiya ba afi yan mintuna ba sai gasu gidan sun samemu da motoci hudu muka shiga gwaggo shafa tana cikin mu tare da wasu yan uwa da basu bamu baya ba marasa tsoro ke nan su. Tunda muka shiga motan muna tafe suna fada min naja Tawakhaltu illallah lahaula wallakuwatu ina billahi aliyal azeem sau uku sai na dinga jan, Hasbunallahu wani imal wakil har zuwa shigan mu gidan shi na dinga ja a bakina ina hawaye. Ba zan iya fadan ko hawayen me nake sakewa ba har wanan lokacin asalima ba bace ina cikin hayacina ba gaskiya don sai yadda aka juyani kawai nasan dai ina dan picking din wasu abubuwa dake gudana dani lokacin. Jin mota ya tsaya lokaci guda ga guda da ihun yaran yana tashi lokaci guda yasa na lumshe idanuwana a hankali naji mommy kubura dake gefena zaune ta dan kwanto min tana fadin yawaita karfin zikirinki a wanan lokacin ki fara da ya Rabbi ya rabil ya rabil alamin ya Allah ina rokonka a ckkin kyawawan sunan ka daka baiyana suga bayin ka ya Allah ka suturani a dakin mijina har Abada ka kawar da duk wani shedan da shedaniya a tsakanin , , , , , , , Nasan ina maimaita abinda mommy din tace in fada daga haka na rikice masu har zuwa cikin dakin nawa saisune suka san halin da nake ciki kan gadon dakin ta kaini ta zaunar dani da bissimillah tare da adduan koran shedan gareni. Anyi adduoi daya dace ayi a lokacin kafin manya su fara watsewa bisa umurnin mommy kubura dama suna sauri su koma suje kai sauran amaren gidajen su haka yasa bata samu wani matsalaba wurin sallaman mutanen. Muka rage daga mu sai su su hudu sai yan matan dake falo su hannatu sai zuwa can na fara gane inda nake zaune duk da ban sheda a dakin da nake zaune ba lokacin. Kai gaskiya idan Allah ya hadaka da mutanen arziki a rayuwanka ka godewa Allah don sai ka daukama sunfi wani dan uwanka na jini wani lokacin. Don ko ni naga hakan a wurin uwata don ko yan uwa da abokai sun nuna mata gata sun fitar da ita kunyan kishiyoyi dana mutanen gari tare da bakin cikin mahaifin mu. Yan kawo amarya sun koma cike da mamaki tare da labarin abinda idonsu ya gane masu a gidan kowa saidai ashe mu munbar baya da kura don Aisha dai ba a samu kaita nata gidan mijin ba. Saboda mijin nata yana nan aka bakan shi naya fasa auren nata tunda har tai sanadin data tozartashi a gaban mutane ya baiyana halinshi a cikin rashin sanin kanshi lokacin. Wanan yasa ya rufe gidan shi ya juya zuwa portakut inda yake aiki ya fita zancen su ya kumabar sakon cewa ya fasa sai ya dawo suzo su kwashe kayan su. Mamakan da yarta ranan sun kwana da bakin ciki ita kuka yarta kuka ga zagi da Abba ya dinga surfan su dashi na tozarci a bainan jama,a kowana jinsu. Tsab hannatu ta gyara dakin ko ina duk hjy kubura na tsaye har aka saka kamshi kafin ta kara lekani inda nake kwance mukayi sallama ta fito tabar su hannatu su uku a dakin tare dani. Tana jin daga dayan lungun da akace na iyayyenshine ana fadin wai Dije mutanen nan sun tafine basu kawo muna amaryan nan dakin ba ko meye ? Ato ina muke da kimar da zasu kawo muna yarsu nan ai bai nuna masu cewa muna da wanan matsayin ba gareshi aiko zanga yadda zaiyi yau yace zai shiga lungun nan. A,a ki barshi ai yana da hankali koma meye dalilinsu nayin hakan zamuji ai daga gareshi suna hakan sukaji sallaman hjy kubura duk sukaja bakin su sukai shiru. Su biyune suka shigo ta gaisa dasu take fadin kun jimu shiru ko wallahi mun kawo yarmu sai ya kasance bata da lafiya tana can kwance kafin mu fito saida akai mata allura amma kuyi hakkuri idan Allah ya kaimu gobe zamu kawota gareku. Yanzun ma na shigone in fada maku don kada kuga kamar an raina makune anki kawota nan wurin kune ayi hakkuri don Allah lalura ya kawo hakan. Nan take su Dije aka shiga fadin jam Allah ya bata lafiya daga jigilan buki sai kuma ciwo haka Allah ya sauwaka. Tayi masu sallama ta tafi mahaifiyar Ahmed dake tsaye tana jiran kaucewan ta tace aiko ba gidan nan ba dama nasa badon Allah aka aura mashi yar nan dole da wani dalili a kasa da yaron nan yake boye muna.