← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 278 OF 286

Sashe 278

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe hudu da rabi yana cikin gidan nasa na gusau wanda dawowan shi ke nan lokacin daga tafiyan da yayi Abuja zuwa rakiyan su Abban mu daga can kuma ya tsaya yin wasu aiyuka a office dinsu na nan Nigeria. Waya yakeyi yana fita motar kunnensa na makale da yar wayasan a cikin fada yake fadin gaskiya salisu ban dauka har zan dawo garin nan baku fara wanan aikin ba. Wanda suke wayan dashine ya tsaya masa bayani can yace amma kasan muyi dakai ai zaka duba abin daga karshe kayi min bayanin yadda ya kamata a tsara wajen yanzu. A daidai lokacin ne kuma idonshi ya sauka a dan tsiron daya fito a can manne da jikin gatangan gidan nasa wanda yasha interlock ko ina da akabi akai ado da launin ja a tsakiya. A hankali yake takawa zuwa wurin wanan tsiron yana sauraren salisu din yana kuma bin wanan tsiron da kallo har ya durkusa yakai tsugune yana kai hannunsa daya a saman tsiron yana duban shi cikin mamaki kafin ya sake wani shu,umin murmushi a fuskanshi yana fadin ba matsala kuje din yanzu ku diba ina gida nan gusau din sai kuzo kuyi min bayani idan kun fito. Don banson aikin ya dauki lokaci mai tsawo don Allah don koda yaushe zan iya komawa da iyalina US a yanzu to sai kazo ya fada yana mikewa tare da kara kai hannunshi a jikin dan tsiron yana mamaki a lokacin. Juyawa yayi ya kalli Bala maigadi da sharesharen filin gidan sai ya gansu dukkansu su ukun tsaye bayan shi suna jiran ya gama wayan suyi mai sannu da zuwa yace. Malam bala ashe kana kusa don Allah wanan tsiron kada a kuskura a cireshi a wurin nan a barshi nan don kyautane daga Allah duk inda nake irin hakan yake fitowa a wajen saboda haka kada ka cire min shi don Allah. Duk ma wani kalansa da zai fito a barshi a ciki gidan nan don Allah da sauri isah mai gugu ya karbe da fadin maigida ai kamar tumfafiyace uwar kwankwanmai cireta ma ai gangancine a wuri. To don Allah a barshi kada a cire ya kara fada yana kokarin shiga cikin gidan kai tsaye lokacin ne suka samu daman mika gaisuwansu gareshi ya tsaya ya amsa ya shige ciki. Ya barsu a wurin malam balane ya fara magana yana fadin kai wanan bawan Allah akwai saukin kai sosai wallahi ni kafin yazo yadda na dauka wani mai zafine shi ai yadda ake bada labarinsa . Kai yana da zafi amma sai ka tabashi gashi kuma da ka ganshi nan kana masa kallon yaro ashe babbane wallahi ni shedace don akwai shegun a boye wallahi nunawa kawai baiyi. Ina daki kwance a inda na idar da sallah nabi sanyin ties nakai kwance a kasan don na danji saukin yadda nake jin kaina a lokacin Bannah ta saman gadona tana tsalle tsalenta ita kadai Amir kuma ya haye jikina yana doki hakana dole na kyalesu duk da sun dameni ina son hutu. Amma gudun kada su fita su Asmau na gidan yasa na barsu a nan wajena suna wasan su a lokacin har hannatu na kirani muka buge da wayana muna zancen jikin Abba da ita a cikin wayan. Kamahin turaren sa daya daki hancina tun kafin ya karaso yasa na furta daddy har yaran sukaji suka dauki ihun daddy a cikin murna ya turo kofa ya shigo yana cabesu ya bini da kallo. Kokarin mikewa nakeyi zaune da kyar daga inda yake tsugune ya rungume yaran ya zubo min ido yana fadin yayane madam na ganki a kasa kwance haka ? Ko yau kuma kwanciyan kasan ne ya taso maku kuka zube a nan din murmushi na dan sake nakai zaune tare da jawo gyalen rigan dake jikina dana daura a kaina yake zamewa na gyara ina fadin na kwantane ko zanji dadin jikin nawa nan. Ai naga alama ya fada yana mikewa tare da yi min wani irin kallo a lokacin nace ka dawo lafiya na fada ina dan murmushi don irin kallon da yai min din a lokacin ni kadai nasan fassaranshi a zuciyana. Zama yayi bakin gado saidai ya mayar da hankalinshi ga yaran lokacin hakan ya bani daman samu na mike tsaye fita nayi don in dauko mashi ruwa a falon na samu har su Asmau sun wuce ashe. Dakin Dije na leka ina fadin dije maigida ya dawofa tana kishigide da casbaha a hannunta tana ja tana gyangyadi ta zabura tana fadin Alhamdullahi ya iso lafiya ko ? Na amsa mata sama sama na dauki ruwa da cup a kitchen na nufi daki dashi na kai masa muka hade dasu zasu fito hakan yasa na juya falo na bisu ya zauna a doguwar kujera yaran suka dane jikinshi suna manne dashi har na tsiyayya masu ruwa da kyar suka barshi yasha wai suma zasu sha ruwan yana kokarin basu na hanna ya dago min hannu . Haka yasa na koma gefe daya ina kallonsu a raina nace mugun gado son diya kamar rayuwa shiyasa inna take da matsala ai mutun ya dinga nuna son dansa kamar rai. Yes rainane aiku don wa nake wahala yanzu ba don kuba ya bani amsa yana miko min kofin ganin yadda na hade raina kicin kicin a lokacin. Nasan me nakeyi zahra kada ki dauka ina son yarana da yawa idan ban kulaku ba kema abin bai maki dadi ai ya fada yana kai jikin shi a makarin kujera ta baya ya lumshe idanunshi a hankali. Nace yanzu ni mena fada kuma don Allah bai bude idanun nasaba yace nasan tunanen da kikeyi ai ashe ka iso dije ta fada suna fitowa da Aisha dake masa sannu da zuwa ya amsa da na iso dije kuna lafiya tace Alhamdullahi yaya hanya ya kuma mai jikin can da wurin mahaifin naka koda yake munyi waya ma da ita maman naku tace jiki da sauki ai sosai akwai cigaba yanzu sosai. Dije ai dama rashi kesa a bar mutum har ya halaka a gida amma in kwana bai kareba inda hali magani ai yana inda yake har yanzu ai suna kan masa gwajine su gano ainihin abinda ke damunsa yanzu. Ai an godewa Allah tunda akwai kudin yanzu da haka zai hallaka a banza cikin kasan nan ana masa canfe canfen ciwarwutan banza a kansa da zai kara dagawa mutum hankali. Ke baki koma ba ashe yake tambayan Aisha da take kaiwa zaune tace ina nan ai tare da dije muna kwasa nace Asma ashe sun tafine ina daki ban sani ba ? Tace ai dama gulma ya kawota koma ya akayi ta gano gidan nan oho ni nayi mamaki dana gansu wallahi don ban dauka tasan gidan bama. Au na zata kece kikayi masu kwatance ai tace a a wallahi ban fadawa kowa ba koda naje kwasan kayana inna kamar gaba takeyi dani ma don ko magana batayi min ba har na fito. Ai naji Asmau ta fara sakin magana yasa na koma daki don ban iya magana yanzu ta lauye mutum baida wuya taje tacewa inna ga abinda akai mata kuma yasa na koma daki na kwanta. Wayanshi ta dauki kara ya ciro daga aljihun wandon shi yana fadin ya salisu kaga wurin ko sai wanda ya kira da salisu din ya tsaya yana masa bayanin yadda suka kwasa dasu inna din a lokacin mundai ji yana fadin a,a a,a har ya kashe wayan bai iya magana ba. Sai cewa damu yayi dije yar iskan yarinyar nan Asmau saina karkaryata kita koma gidan ubanta yau wall, , , kai kai kai kada ka rantse don Allah don kasan ba abu bane mai yuyuwa don inna bata bari kadaiyi mata fada kawai idan tayi ma laifine na fada. Dije tace tayi wani tsiyan kuma ko ya dago ido ja yanacewa Dije din wana tura masu aiki suje gidan su duba gyaran da za ayiwa gidan shine Asmau ta fito take gaya masu maganan banza wai su dawo wurin wanda ya turosu suce dashi ba gidan bane don su basu da labarin aiki kijifa dije wai Asmau zata kawo shegan takanta gareni yanzu. Wanan yar iskan yarinyar ai tafi da nan barni da shegiya mai gadon tsiya inba tsiya ba yaya cigaba zai sameki har ki nuna halin tsiya a wurin ga yar banza da son kakale idan an gyara gidan ta samu na karya dashi ke nan. Sai mamaki yakeyi yana fadin a,a yaushe renin nata ya kawo gareni haka niko ina zaune sai mutmushi nakeyi don nasan Asmau zata aika naji Aisha tace. Yaya kaine baka san yadda ta koma yanzu ba kamar kada tayi shegen auren nan nata take ganin a yanzu ita tafi kowa ita wata babbace inna kuma na kamata. Da ita da uwar naku duk sai su bar gidan tunda basu da gadon shi gida na Amadine kowa ya sheda hakan a unguwan nan don ladan a masallaci ya fada in ya mutu gidan sa ya mallakawa jikanshi Amadi gona biyu kuma su yaranshi biyu su raba a tsakanin su sai yan tarkaceshi a bani. Kowa yasan da wanan zancen idan bata sani bane ta sani ni kuma zan tunawa uwarta wanan zancen kuma malam bai bayar dashi gareshi ga banza ba kudin da mahaifinsa ya bar masane da malam din ke juyawa suka karye a kansa ya sadaukar masa da wanan gidan a matsayin kudinshi abu da yake baiyane . Yar banza koba haka zancen yake ba ina take da gadon gidan mu ita da zata kawo muna iyayi a cikin harkan mu yanzu ta koma gidan ubanta na wanzamai tayi iko dashi in ubanta nada daki gidan. Haba dije abar gori mana ai abin baikai na tone tone ba haka itama dai sallontane da shiga maganan manya ko shi aidon ya shafeshine yanzu zai shiga balle ita. Barta yar banza daga ita har uwan nata in karanto masu suji idan sun mantane da zasu kawo muna iko a cikin zance ko yan uwan malam ai sunso suja lokacin aka taka masu burki bayan mutuwan malam din balle ita. Mikewa yayi rai bace ya shige daki saidana dan dade a zaune kafin in mike inbi bayansa na samu yana ban daki
Chapter 278 · 0% Book details