← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 286

Sashe 31

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

muna mulkin kama karya haka ? Salma ni kike fadawa hakan yau ke wacece da ba zan fadawa haka ba ke uwatace ko kanwar ubata da ina girmamaki don wasu dalilai amma sai ga hakan ke kin dauka fin karfine hakan ko ? Dana dauka kinsan mutunci yasa nake baki girma da kyaleki a matsayin wace ta girmeni a shekaru sai kuma sanin girman zumunci da nayi nasan ke yar uwan maigidanane daga baya kuma ina girmamaki kan yaran ki. Amma yanzu tunda na fahinci manufarki dakyau a kan mu duk wani girma da kima daraja da nake gani naki na daina bakishi maimuna har abada idan bakin gyara ba. Tana kawowa nan taja tsuki ta juya zuwa kitchen ta karasa aikin da takeyi ta bar mama a tsaye tana yankan sababi a falon mu har ta juya ta fita tana fadin. Zan hadu dashi a waya shida ya baki zaizo ya karba ya kawo min ke har zama bariki kika koya da zaki nuna min kan mage ya waye a yanzu ? Mu zuba dake da munafukan yarki data sameshi da munafuncin an bata motar Aisha tafi karfin shi ita ai ban san tafi karfin shiga wanan motar ba sai data nuna hakan yanzu. Idanuwan mutane aka motana suna duban suga waye ya shigota haka ya haska kowa saidai na dan jima a ciki ina hada kayana kafin na bude na fito . MAYANA wata ta fada wanan ai yar gidan mayana ce wace ke 200 level din nan yanzu maganganu irin na kus kus da jama,a keyi musanman yan makaranta da saka ido shike tashi a wurin har na shige science bluding na shiga department din mu. Kowa na harkan gaban shi don malamin bai shigo ajiba lokacin ba wuri na samu nakai zaune inawa wace na sama sallama muka gaisa a musulunce da ita. Wai naji suna fadin yau malam bai samun shigowa son baida lafiya sai lokacin na kallota ina fadin ayyah Allah ya bashi lafiya gaskiya naga ajin yau a haka. Na dauko wayana a cikin jakkata don in kara tyring din layin ya musa don tun dare nake gwadawa wayan shi a kashe yasa yanzun ma na kara trying. Saidai ban sameshi ba yasani jan tsuki ta kara fadin lafiya nace ba komai yi hakkuri na dameki ko ? Yauwa dama ke nake duba tun dazun banga shugowan ki ba ya kika tashi fuskana na tsuke lokaci guda don ganin mai maganan dani danayi. Ba kowa bane sai wanan guy din da nake ganin yana skn ya matsa min da surutu ko samu kan wanan da bansan komai a kanshi bama. Nace don Allah ko kunyi maganan dashi ya yarda sai mu fara yau wallahi ni nasan zamu samu karuwa sosai a wurin shi wa ke nan wanan dana sama take tambayanshi ? Kinga ga wata member mun samu gaki ga abokina sai mu tafi yanzun tunda muna free ko yaya kuka gani dakata malam don Allah. Kai idan kayi mai magana laifine kaje ka sameshi mana amma ni ba inda zanje na fada ma ya wani kalleni yace but idan nayi masa magana har ya yarda zakiyi joining din mu dai don abin yai armashi ? Jeka kayi na fada a dan fusace yace nikan nasan ba wanda yaki karuwa sai in bai samu ba dai barin dubashi ko yana free yanzu muyi maganan amma fa ki sani da sunan ki zanje in sameshi. Yana fadin haka ya juya ya tafi naja tsuki ina fadin tunda kowa irin kane kada ka tsaya kai karatu ka kwaci kanka ka dogara ga wani. Ganin yadda class din ke surutu rashin malami yasa na mike na fice daga ajin naji muryan wanan tana fadin jirani mu fita tare don Allah dole na tsaya muka fita tare da ita. Wata sister ya tambaya cikin mamaki a,a MAYANA ta class din mu mana wace ka fadawa malam sister dinkace har malam din ya yafe muna mu shiga saboda ita. Ok wallahi so muke mu hadu dakai ka taimaka muna kadan bamu group discussion tace wallahi kunyar ka takeji ba zata iya zuwa da kanta ba. Ina take yau ai bata shigo ba nake gani don banga motar taba a park da sauri munir yace a, a tana nan class zaune ai tazo tun dazun. Ka bari zan ganta muyi magana ya fada a cikin gadara da izza irin nasa na dan tallaka da gadara din nan don haka yake magana kamar dan basarake dashi . To shike nan Done zamu saurareka amma ka taimaka ko don saboda ita please na barka lafiya sai mun jika please. Baidai masa magana ba sai mikewan da shima yayi lokacin don tunawa da kaya gwajonshi dake ajiye a bayan ajinsu ya duba ba abinda ya samu kayan ya kara gyarasu ya dago zai koma lokacin ya hangoni tafe tare da wata muna tafiya a jere muna magana da ita. Tun daga nisa na danna key motar tayi kara daya jawo hankalin mutanen wurin au motarki ke nan ta tambaya na kada mata kai take fadin wai dankari ashe dai ke din yar masu garice shiyasa tun zuwan ki baki kula kowa dama ? Idan nace bata isheni ba farawa da iyawa nayi karya don na kula tana da surutu ita sosai sabanin nida zan iya zama magana saita kama nayi da mutu na bashi amsa daya haka ummah ke shan fama dani a gida. Motar na bude na dauko goran ruwa guda biyu zan dago naji muryan shi yana fadin ashe kinshigo school din yau na juyo da sauri ina dagowa. Yana tsaye a dan nesa kadan damu nace eh wallahi ina ciki tundazun na mikawa wace muke tare roban ruwa daya ta karba tana min godiya tare da jingina jikinta a bayan motan . Dayan Goran ruwa dake hannuna na mika mashi sai ya girgiza kanshi yana fadin Alhamdullahi nagode amma ke baki iya zuwa ki fada min saiki turo min wani. Banina turoshi ba shiyazo da kansa nasan dai da zancen wani kallo yai min kafin yace koda yake nasan kinfi karfin yin hakan da kanki saidai ki turo wani yazo. OK wanan shine dama ake magana me surutu ta tambayeni na gyada mata kai tace malam ka taimaka muna mu dan samu sauki wallahi abubuwa suna da rikita kai yanzu sosai. Idan nace zan dinga tsayawa na koya maku kullun zaiyi wuya hakan saidai lokaci lokaci insha Allah sai mu fara Monday idan Allah ya kaimu don yanzu na riga da na saro kaya ina son in shigar dasu ko Allah zai taimaka min. Kace kai dan kasuwane ashe kana karatu kake da wanan lokacin to yaya za a ayi ya fada ya juya da sauri ya wuce ya nufi cikin department din. Abba dake kwance da kyar ya mika hannu ya dauki wayan irin yadda yaji muryan mama din yasan wani abu ya faru ke nan a gidan ko yana shirin faruwa. Meke faruwane hjy maimuna najiki a hasale dole in hasala Alh tunda yaron nan yana son ya fara jamin magana a wurin ka yanzu. Wani yaro kuma ke nan kike magana ya tambayeta, tace wane yaro kuwa banda baba wai shine harda sayawa Zarah mota mai tsada haka tunda ya isa yanzun yake gani shi. Na aika a karbo key din motar a hannun uwarta don hauka ita kuma ta hana naje da kaina tana son fada min maganan banza wallahi idan salma batai hankali ba zakaji nayi mata abinda ba,a zata ba. Yace ita salma din kwarai kuwa wai yau ni salma ke kallo tana fada min in na isa na shiga dakinta key na ciki koko haihuwanta nayi da zan dinga kawo mata raini irin haka ? Ai gaskiya ta fada wanan ya zama wullakanci da raini wayau a gareta wai ko kin manta salma ma matatace itama kuma tana gaba dake idan ma har wani abune baki kirana kiji yadda akayi. Saiki je mata kai tsaye wai ta baki key koda karba ne aini dana ajeku yakamata na karba a hannunta bake ba don raini saikije mata kai tsaye haka kimkam. Sai zancen motan da kikeyi wai baba ya dauki kudina ya saiwa maamah mota toh ba dauka yayi ba nida kaina na bada kudi ya sayo mata wanan motan kamar yadda na sayawa kowa lokacin fara karatun shi. Ke kika tambaya na bada kudin motan kisaiwa maamah din moto a baya ashe baki sayaba sai kika gyara mata na Aisha tana shiga . Maimuna ina zaki da wanan alhakin haka a rayuwan ki koso kike duniya ta zagemu don uwarta nada hakkuri da zama damu sai mu dinga takasu yadda ran mu keso ? To ki tuna da baba da ita maamah din duk nina haifi abina kuma ina son kowa don haka ki kula don ba zan dauki wanan ba ya kashe wayan. Tabi wayan da kallo ta dafa gado tana zama don da a tsaye take tana shirin zazaga mai bala,i a lokacin sai taji wani abu na daban daga gareshi wanda bata zata ba a lokacin.
Chapter 31 · 0% Book details