Sashe 151
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mashin kuma zahra dince ke yawo a gari saman mashi ina motar nata koya lalace ne kuma Abban ya tambaya acikin mamakin jin hakan ? Daga inda gwaggo shafa take zaune tace wace mota kuma yaya motar daka sa a karbe a hannunta tun lokacin auren su kake rambayan mota kuma yanzu ? Ni din nan nasa a karbe mata mota akan wani dalili ya tambayi su gwaggo din sai gwaggo uwa tace ikon Allah wanan ai tsohon zancene mota kan an karbe munyi korafin hakan har mun gaji ai. Allah zai bata insha Allah da yake yaran daga ita har mijin nata ai ba masu rawan kai bane kaga basu damu da hakan ba gwaggo shafa ta fada . Idan yana gari ya kaita da yar mashin dinshi in baya gari kuma tace mai mashin ya nema mata da yake kaita ya dauko ta har lokacin da zai dawo daga wurin nasa karatun. Ni din nan na saka a karbi mota ya kara fada cikin zafin rai da jin hakan ya dora da fadin towama na aiko ya karbi motan a hannunta wai ? Yaya gambo mana tazo ta karba tace hjy maimuna ta turata kace a karbi key a hannun zahra din gwaggo shafa ta fada. Salma salma ya kwadawa ummah data shige kira a hasale saiga ummah din ta fito yace kinsan da wanan zancen cewa Mamah bata da mota a hannun ta dama tunda tayi aure ? Dan murmushi tayi kafin tace na sani mana bani na karbi key din na bayar a kawo maka ba a daudai lokacin mama tayi masu sallama falom itama ta shigo. Dana aikowa a karbi key din motan ko zahra ta auri yaron nan a cikin fushina tunda ta nace sai shi aidai zahra diya tace har yau kamar dukkan diyana a garin nan. Ke maimuna ya akayi har Gambo ta karbi key din motar zahra akan wani dalili waya turata ta karbo key din yanzu kuma ina motar nata ? Wanan kuma saidai idan ka manta don munyi maganan hakan da kai kace baka ga ranan bata mota ba ai don in ya bace ba zaka gyara ba ko mjjin nata ba zai samu kudin gyaran wana motan nata ba. Ok da mukai hakan sai nace a karba a hannunta ko me don ban gane kan wanan zancen ba dama kin fada min hakane don kisa a karbi motan a hannun yarinyar a tozarta ni a gari ko me ? Wanan wani zance ne kuma haka kake min ni zanda a tozarta ka ko yar ka data auri fakiri a cikin garin nan ita bata tozarta kaba sai ni zan saka a tozarta ka ? Na yaushe kuma tunda girma ya gama zubewa a idon jama,a yanzu kowa yasan haka ai tunda hakan baifi karfin ka ba ummah ta fada tana kokarin wucewa cikin dakin kwanan Abba din. Tare da dorawa da fadin ni dai nasan kaddaran mutum baya ketare shi mamah kuma yarkace koka saka ai maka haka abinda na sani dayane shi mahakurci mawadacine idan yayi hakuri ga komai fatana dai ta zauna lafiya a dakinta. Wanda bakiwa fatan zaman lafiyan bama sun zauna lafiya dakunan su ai dama nasan duk wani shege da ficen da kikeyi salma akan yarana ba yau ba na sani. Saidai ki sani haka zaku kare dake da yar naki a wahalce gidajen auren ku yanzu kin fadane don nayi bayanin hakan kome wai ? Allah sarki ni da kika gani nan ban taba bin dan kowa da mugun nufi ba balle diyan ki ga Allah na dogara da komai nawa ba wani ba nasan kuma Allah bai manta da muba ga hakan. Zancen mota kuma a inda akayi ta dagani har mamah din a nan muka bar zancen don haka ki nemi wanda ya tayar da zancen a yanzu gareshi. Tana fadin hakan tayi shigewanta ciki ta barsu a nan Abba din ya bisu da kallo kafin ya hade wasu yawun takaici yana fadin ji nan maimuna kada ki mayar dani karamin yaro don Allah ? Nafa san abinda nakeyi bawai ban sani bane ta ya zan sakaki ki karbi mota a hannun yata bayan bansa kin karbi na sauran yan uwanta ba ? Kedai kawai kinyi hakan ne dan wani manufa taki can na daban sanan abinda ya ban mamaki cikin zancen nan da ba wanda ya fada min komai kan hakan sai yanzu nake jin hakan daga bakin ku wai ? Manufar me kana son ka dora laifin hakan yanzu a kaina kana denarying cewa baka sani ba ya kallota yace maimuna halinki yanzu wanene ban sani ba ? Kedai kinyi hakan dawani manufa taki kuma ki kawo min motar na gani kafin na wuce inda gyaran da za aiwa motar ayi kafin akai mata abinta. Yana fadin haka ya mike ba tare da sunyi zancen daya kawo yan uwan nasa ba wurin shi sai cewa yayi shafa koma meye ya kawo ku inji a wurin hjy gobe in na shigo ta fada min komai koke dake kusa in na shigo ki shigo muyi maganan dake. Wanan zancen nan take ya bazu a cikin dangin mu yan uwa suka fara fadin albarkacin bakinsu kan haka har saida yakai kai ya rabu biyu a tsakanin su. Har yakai labari yazo kunnen mu cewa ai mama itace tayi makarkashiyar karbe mota a hannuna wanda sai yanzu Abba din ke samun labarin hakan da akai min din. Ban san a ina mahaifiyar Ahmed ta tsinto wanan labarin ba na daiji tana yada habaici a tsakar gida da fadin dama na sani ko a gidan ba wata tsiya bane ashe ? Ba a bakin komai mutum yake ba dama ina za a dauki yarso aba mutum irin yaron nan da baida komai dole sai abin banza irin haka ai. Dije ko ta fito ta bata amsa da fadin ai sun zama banzaye ke nan har dan naki da kike shirin aibantawa a yanzu don ba yar mutane kike wa wanan zance ba in kina da hankali dabaki fadi ba. Ai tayi muna komai keda uban dan ya gudu ya barki da dan shekara da shekaru babu waige a gareku me kuka zama a idon jama,a yanzu ? Sai amsan Dije din yai mata zafi tana fadin inna nidai bance ga wanda nake wanan maganan akamshi ba inma ubanshi ya gudu ya barmu ai hakan bayin kan mu bane nidashi. Har dai zancen ya kaisu ga bacin rai wanda a karshe yana dawowa yaji wanan labarin a bakin makwanta suna sheda mai abinda ke faruwa yanzu a gidan ba dadi. Saboda makwabta sun fara gane irin zaman da akeyi a gidan nasu yanzu wanda mahaifiyar shice ke jawo hakan ko yaushe. Nikan na gama duk wani abinda zanyi a ranan na samu wuri na kwanta don ya fita da sunan samo muna shelto a fesa a dakin har barci ya far daukana ina dakon dawowan shi bai shigo ba. Ya dawo yake tayar dani na koma falo ya fesa muna a dakin na mike da kyar na fito falon ya fesa a ciki har bayi can sai gashi ya fito dagashi sai dan boxer na maza a jikin shi. Duk suran jikinshi a waje lokacin saidai kallo daya zaka mai ka fahinci zuciyar shi babu dadi a lokacin na saba da ganin hakan idan wani abu ya bata mai rai. Dan zamana dashi da mukayi yanzu ya zaune kusa dani a inda nake kwance jin hakan yasa na jaye kafana daya dan zauna a kai. Zahra wai sai yaushene inna zata daina halaiyanta irin haka a kan mu wai ace kamar inna tana zama tana sa insa da mahaifiyar ta wanda gaskiya ada can baya bansan ta da wanan halin ba haka? Tayi wani abinda ba daidai bane kuma tayi mana duk daku baku fada min ba duk da nasan kedin ba fada min zakiyi ba har dije din da sukai hakan da ita. Meya shafi inna da zancen motarki da aka karbe a gidan ku har suke sa,insa da Dije akan hakan ?