Sashe 75
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
maki ko falo zan kai maki abincin naki ? Da kyat na iya budan bakina da yai nauyi lokacin nace a barshi zan fito falo in karya a nan na fada mata ta juya zata fita nace nagode tace kai ba komai uwardakina ai muna tare ina bayan ki har kullun don mu hjy tayi muna komai wallahi dolene mugani ko mu maganta a zancen. Ta fita na sauke ajiyan zuciya ina tunane don a gaskiya ba zance ga dalilin kukana ba saidai abinda nasani shine yin hakan da Abba yai min a yanzu zai iya jawo min matsala a karatuna nishi nake ganin dalilin damuwana a lokacin. Mikewa nayi daga zaune din na nufi falo kai tsaye wurin daning na nufa tun kan nakai zaune kannena suka rufa min da taimakon hiran da suke min har na samu na dan sake . A wurin Abban mu ya sameni zaune muna hira da yan uwana suna ganin shi suka nufeshi suna fadin yaushe za,a kawo muna keken mu. Daga inda nake zaune nake fadin welcome Abba ya amsa min yake fadawa yaran cewa yau idan na koma zan sayo maku na aiko maku dashi. Hakan yasa na fahinci cewa a rana zasu koma ke nan ashe bedroom din ummah ya nufa yaran suka dare don ba mai shiga idan Abba din ya shiga nan din. Muna zaune tare dasu suna murna ya dan jima sai gashi ya fito daga dakin a tsakiyan falo ya tsaya yace maamah zo nan na taso da sauri daga inda nake din zaune nazo na sameshi tare da dan rage tsayina gareshi . Hannuna ya riko ya dagoni ya fara fadin ki kula da kanki mamana bana son yawan shiririta ki natsu kiyi karatu yadda ya dace kamar kowa ni da kaina zan zaba maki abinda ya dace dake in sha Allahu. Na amsa da to Abba na gode in sha Allahu zan kiyayye ka yafe min abinda kake zaton inayi a bayan ka wallahi Abba hakan ba gaskiya bane. Is OK ya fada yasa hannu a aljihunshi ya ciro kudi masu yawa ya miko min yana fadin ki kula na fada maki ga wanan ki mayar da hankalin ki sosai abinda baki dashi ki kirani ko ki fadawa Hjy salma ta fada min. Nagode Abba na fada yace wa kannena suzo suka taho yake binsu yana sallama haka muka rako shi har kofan part din mu don ya nufi part din mama yasa muka tsaya a nan muna masa Allah ya tsare. Koda muka juyo zuwa ciki ummah ta fito falo a lokacin nan yaran suka rufeta da fadin Abba ya bamu kudi ummah tace kun gode ai na muka fara mika mata kudin an kawo kaina tace ki rike naki a hannun ki tunda ba tambayana kudi kikeyi ba. Sallaman mommy ce hjy karima ta shigo da fara,a a fuskanta tasha kwaliya sosai a jikinta tana fadin to uwargida rangida mu zamuyi maku ta baki fa don Allah a gafarce mu. Tare suka shigo da wanan matar suna sallama ummah din kafin ummah ta kakaro murmushi a fuskanta tana fadin muma ai ku gafarce mu zaku juya ke nan yau ashe ? To ba dole ba tunda kun hana mu zama lafiya a nan din kunce bamuyi daidai ba ai dole mu juya kada azo rayuka suna baci a banza ni wanan matar da ace garin nan nake zaune tare da ita da mun kwashi yan kallo a tsakanin mu kullun. Mace haka ba tsoron Allah sam a zuciyarta sai son kai da son zuciya kamar kowa ba mutane bane sai ita ai bata cika yar sheri ba tunda harta kasa hanashi kara aure takuma zauna da kishiyoyi aishe bata isa ba ke nan ? Murmushi ummah ta kara sakewa tare da kallon matar da suke tare tana fadin baabba zaku koma ke nan ashe yaune tafiyan naku ? Gashi dan tsaraba ba a hada maki ba zaki tafi hannu sake babu komai wallahi ko wanan fuskan da muka samu ai kin bamu komai sai kuma wani lokacin idan Allah ya kaimu. Aita hakkuri kiji yar nan me hakkuri shike da riba wata rana in sha Allahu wata rana sai labari haka rayuwa take wani lokaci ga bawa mai tawakkali da Allah. Nagode baabba ummah ta fada ta mika hannu ta dauko wani leda da tun shigowan mu yake aje a gefenta tana fadin hjy karima ga wanan a rikawa baabba ba yawa bamu sanda tafiyan ku ba yau ban hada mata komai ba. Kai haba dai ba zamu karbi komai naki ba gaskiya haba dai bafa ke nabawa ba baabban mu nabawa don haka ki bar zancen nan don Allah. Gaskiya ni banda bakin magana don ko hakan ai mun gode da karamcin ki garemu Allah ya kara bamu hakkurin zama tsohuwar ta amsa da amin. Hjy kariman tace to ni ina skn naje nayiwa wanan sallama bansan da wani ido kuma zata tarbeni ba a yau don idan tayi min ba kyaleta zanyi ba. A,a a rabu a gana alherine kada ki biyewa wanan aikin zama tare ne hakan don wanan zance ai ba kyaki zuwa kuyi sallama ba musanman ma ba da zata tafi. Ke ke nan kika san wanan din bari dai din muje sai munyi waya in sha Allahu kuma suka fara tafiya don barin falon kafin ta juyo tana fadin daughter sai na aiko ke nan ko nidai nayi murmushi kawai na mike na dan rakasu zuwa fita part din mu dagani har ummah muka juyo muka dawo. Hankalina na mayar ga tv da ake wani film din yara a cikin sa tani ce ta shigo tana fadin ashe yau zasu koma shike nan har sun tafi ? To meye a ciki yanzu bagashi sun juya sun tafi tare ba kuma ba a isa a hana hakan ba don kwanan ni wallahi suyi ta kwana bashine a gabana ba. Mazan nan da zaka mutu a kansu su kasa suma maka su wanan hauka hjy maimuna keyi tace wai bata yarda don sunzo nan din tare ta amshi girki ba tunda a can tare suke dashi. Yanzu kinga ya barta da kunya kuma girma ya zube kan abinda baikai bai kawo ba an tafi an barta da bacin rai da takaici ga banza. Ta dauka irin kine ai data saba takawa tana hawa yadda takeso a kullun tani ta fada yoni ina ruwana da wanan bakin haukan ? Hjy ke wake daka ta taki keda ke barin mutum da wutar shi ta konashi ai zama da irin ku yana da wuyan sha,ani sosai idan mutum bai gama ganeku ba. Ina zaune ina jin abinda suke fada gaba daya dana tattara sai na gane cewa abinda mama take son fada min ke nan da safe dana shiga wurinta yaranta suka hanata fada min komai. Koma meye matsalansu ce ta manya hakan don su hakan ya shafa ba zancen mu bane mu yara wanan maganan tasu. Mikewa nayi da niyar barin falon Tani ta kalleni tace dani uwar dakina komai ya wuce ke nan da alaman haka ? In ma bai wuce ba ai itabta sani yanzu da muka kyaleta da shirinta ba gashi abin ya koma a kanta ba an watse a baram baram tsakanin su sheri ai dan aikene dama. Nayi mamaki matuka da wanan zancen har yazamo hakan wani irin abune yaran nan basayi a garin nan amma saina wanan kawai aka gani a gidan nan har ya zamo min abin fade. Yanzun dai ai intana da hankali tagani ke nan sai ta shiga hankalinta idan zata shiga don abin kulin sheri yanzu baida kadan ta dai rabu da yaron nan shima tunda har Alh ya iya kiranshi yayi mai warning nasan zai rabu da itane . Haba hjy ki rabu da aikin so yana da wuya ace an rabasu haka farat daya yadda kuke nufi din nan sai dai ku bisu da addua shine mafita don uwardakina tana da saukin kai sosai don gashi dan maganan da nayi mata dazun yasa ta sake harta fito yau din waje. Kuma fitowan ai ya zama mata alheri tunda uban ya shigo ya samu ra sake naga aisun shirya kafin su tafi hakan itama bai mata dadi ba yanzu ? Darene gabanin asubahi lokacin sanyi ya sauko kowa najin dadin sanyin masu ibada a lokacin suna jin dadin yanayin dije dake kwance tana barci a cikin yanayin da kowa keji ta fara mafalki. Sai dan juyi takeyi tana dan mutsutsuka kamar yarinya kafin ta mike zubur daga kwancen tana sakin salati lokaci guda tare da fadin Amadi ?