← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 286

Sashe 19

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

duk yadda kake ganin kanka kafi wani don wani na can bai kaika ba don nasa irin talaucin sudake cikin gida har da siminti a tsakar gidan tana ganin talaucinta ga wa yanan su dan dakunane kamar madafi suke rayuwa a ciki. Nan yaiwa Dije dan bayani a gurguje ya barta da Tani su karasa maganan tunda shima itace ta karbo mashi don haka ita tasan yadda zasuyi bashi ba. Nan ne hira ya barke a tsakanin su har take labartawa Dije komai har kudin dayaki karba hannun ummah din duk a cikin dadin hira Tani taba dije labarin komai. Tare sukaje aka karbo malam Tanimu yayi masu bayanin komai yadda za,ayi amfani dashi har dana tsarin jiki da sauransu duk ya bada ta bashi dubu daya ya amsa yana ta godiya. Hakan yasata makara da zuwa aiki koda tazo ta samu ummah tayi nisa ga aikin hada breakfast ummah taso tayi fada sai ga leda ta fito dashi tana fadin aida zancen ku na kwana a raina hjy. Shiyasa na makara ga wanan na karbo dana uwar dakina wanka zakiyi har yaran kuyi hayaki wanan kuma yace kusha tun da asuba na neman sa,an makiyane da makarun su. Kallonta ummah keyi kamar da tuhuma a zuciyar ta sai Tani din tace hjy ko baki aikeni ba ni mai zuwa na karbo maki wanan din don koba ki fada ba mai hankali yasan zaman da akeyi a wanan gida. Ba wani abin muni na karbo maki ba kariyane da tsari ance ko kana da kyau kara da wanka don ni gaskiya ciwon nan da uwar dakina keyi kwanan nan da ayar tambaya a cikinsa. Ciwo bai tashi sai lokacin da yarinya zata je daukan darasi kan abinda zai amfaneta a rayuwa kinga wanan alaman wani sherine dake faruwa a wani kulli dake faruwa a wani wurin. Kome ke faruwa da ita da sanin Allah nasan ina iya addua na kan zuri,ata koda yaushe ina neman kariya gun ubangijina da ya tsare mu kan abinda bamu sani ba mai cutarwa zuwa garemu. Kwarai kuwa hjy nidin shedace kan hakan nasan baki wasa wurin ibadan ki don shine ma har yau ba a ci galaba a gareki ba amma kuma ki sani. Yaran nan zaki duba idan ana harin ka ba a sameka ba za a iya samun yaran ka ko wani abin ka shine dadin kiwon dabba da kikaga mutanen kauye sunayi. Sun san ma,anan hakan shiyasa ba kauye bai rabuwa da kiwo koda ta kazace kuwa don sai ya fadawa dabban naka don ansan naka dinne. Kiga ko dole a tallafawa rayuwan yaran nan don maganan gaskiya hjy maimuna bata kaunan yaran nan ta yadda har bata iya boye hakan a gaban kowa saboda kishin ki daya shafesu. Nisawa ummah tayi kafin ta kai kallonta ga kullin maganin da Tani din ta karbo mata tace bawai ban sanda hakan bane na dade da sanin akwai kiyayya har ya shafi yarana saidai bana son na raja,a gun irin wa yan nan abubuwan ne har ya bata maka imanin ka. Amma na gode in sha Allahu zan gwada zanyi muna amfani dashi da yardan Allah musanman kan ita maamah din don wanan matsalan nata ya fara damuna gaskiya. Ciwo haka daga sama Allah na tuba ni wanan matsalan haka ta ina zan soma taron shi hjy haka na faruwa kana zaune da yaron lafiya da rana tsaka ya sauya ma . In sha Allahu maamah tafi karfin duk wani shedani da shedanci ki dai dage kiyi masu amfani da wanan maganin koba komai ba a san inda kizo ke saka ba ai shiyasa akewa yara tsari da adduoi a yanzu sosai.
Chapter 19 · 0% Book details