Sashe 201
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
fa itace amma suka gargadeta da yin hakan don sun san zai iya bultse masu yace ya fasa idan yaji wanan dokan data kawo na cewa. Sai hjy murja ta koma gida Gembo da zama kamar yadda suke zaune a da can tun bayan aurenta dashi din amma sukayi saurin kwabbonta da hakan dole haka ta hakkura ta dawo gidan akan zasu zauna tare su biyu a gidan kamar yadda ya tsara yanzu din. Yau yai mata dadi don hjy murja zatayi girki amma kuma yayi tafiya zuwa sokoto kamar yadda ya fada masu a gidan da cewa zasu daurin auren wani dan abokinshine a sokoto. Hakan yasa taji dadi don a yanzu duk wani hanya da zata kuntatawa hjy murja na fili dana boye shi tayi dammaranyi a gidan da ita har sai ta gaji ta bar mata gidan da mijinta. Don ita ba zata lamunci wata kishiya ba can idan kuma taki a shirye take data salwanta da rayuwanta gaba daya tabar duniyan kowa ya huta wanan shine kudirinta na karshe a yanzu din . Da wanan plan take kwana dashi take tashi tana kullawa tana warwarewa a zuciyar ta taga wanan ne a yanzu hanya mafi sauki a gare a daidai wanan lokacin Asabe mai aiki tayi sallama tashigo dakin ta duka tana gaida ita. A wullakance ta dago kai tana kallonta tare da fadin lafiya kika shigo min daki haka ko wani abin kike nema kuma ni banson irin hakan na fada maki tun farko da banson ana shigo min daki idan bani na nemi mutum ba. Hjy a gafarceni dama Alh ne ya dawo yana falo yana cin abinci naga baki fito ba shine nazo na fada maki don kije ku gaisa. Alh ? Alh fa kikace mutumin daya tafi dazun da safe yace sai zuwa jibi shine zakice ya dawo yanzu don Allah ki dai duba da kyau ki gani idan ba wani kato ta kawo muna a gidan ba. Dan dago kai Asabe tayi a hankali kafin cikin rawan murya ta kara fadin wlh Alh ne don har mun gaisa dashi da isowarshi. Zubur Asaben taga ta mike tsaye a yadda taken haka ta fita daga ita sai dan rigan barci mai karamin hannu duk suran hammatanta a waje suke. Ya mika hannu ya dauki ruwa a cup din da hjy murja dake gefenshi zaune ta tsiyayya masa zai kai baki ta fado masu dinning erea din kamar a firgice. A hankali ta tako zuwa inda yaken tana fadin ashe tafiyan dama bana kwana bane kace zaku kwana biyu a can yace eh abinda mukaje yi an fasa don haka na dawo. Ta danyi shiru tana kallo cup din ruwan dake hannunshi kamar tana son ganin wani abu a ciki lokacin kafin can ta dago kai ta kalleshi tana fadin Allah hutar da gaji ra juya zuwa part dinta sai a lokacin ta fara data sanima da bata fito ba garesu. Daki ta koma zyciyarta yana azalzala lokaci guda kishi ya rufe mata zuciyanta harta fara anyana abubuwa mara kyau a garesu kafin taji wayanta yana kara ta dauka yarta salima ce data koma ghana inda take karatu a lokacin. Takai hannu ta dauka murya ciki ciki take fadin salima kece da wanan daren haka tace eh mum haka kawai na kiraki inji lafiyan ki dana yan uwa daddy fa komai normal dai ko ? Amsan data bata a lokacin yasa salima din tambaya da sauri mum kina lafiya kuwa naji muryan naki a slow mana lafiya ta fada tana jan tsuki tace daddy ku daine yake son kasheni akan matar shi. Daddy kuma har yanzun dai mum na fada maki ki fita zancen shi kibarshi da wanan matar tunda ita yake so a yanzu sai suje suyi tayi da sauri ta katse yar nata da fadin. Salima kina da hankali kuwa ta yaya zan fita zancen shi in barshi da ita har wani tsufa nayi da zan kyaleshi ina kallon shi da wata mace ranta ya baci bata san lokacin data fadi hakan ga yar nata ba. Sorry mum kiyi hakkuri zan kira ya yasir ko zaiwa daddy din magana nima zan kirashi in masa masa magana muji abinda zai fada i promise you zamu ciwo kansa ki bamu gobe da jibi don Allah. Jin yarinyar kawai takeyi don ita bata iya ciwo kansa ba sai sune zasu iya masa magana yaji da haka sukai sallama ta kashe wayan nata takai kwance ranta a bace har barci ya dauketa. Yau sosai yake jin kewan gida dana matarshi hakan yasa ya kebe kanshi tun safe a daki tunda ba wani gwajin da zasu fitayi a ranan. A haka barci ya daukeshi yana cikin yanayin tunanen gida yssani Allah ya dora mai son Zahar a zucjyanshi sai dai bai taba tsanmanin abin ya kai har hakaba a tare dashi. Ya gane hakanne a yanzu da sukai nisa da junansu don tsanani yayi sati biyu ya juyo zuwa garesu tun bayan da sukai aure yau sai gashi yana neman share sati hudu ba tare dasu ba. Yake jin kewansu na shiganshi hakan musanman ita zahran dake debe mai gajiyan shi yanzu rashinta a kusa dashi ya fara saukar mai da wani irin yanayi na daban. Falkjn da yakeyi ne har sautin muryanshi yana fita a zahiri yana fadin na fada maku kada ku tsaya sauearen shi don babu abinda zaice damu yanzu tunda komai yakai karshe. Ganin Dije da su inna basu saurara mashi ba yasa ya fara kwalawa zahra din kira da karfi har sautin kiran na fita fili a zahiri dakin na amsawa lokacin. Hakan yasa shi tashi a zabure yana zufa tare da dan waige waige a dskin ko zai gansu ganin inda yake yasa ya gane mafalki yakeyi a lokacin ke nan haka yasa ya zauna yayi shiru na dan lokaci yana tunane. Wayanshi ya jawo yana duba kudin dake ciki a lokacin ba zasu isheshi kira ba har yaji komai don haka ya rubuta sako ta whatsff ya bar mata daga haka ya mike yaje yayi alwala ya fito. Dabi,an shine duk lokacin dayayi wani mumunan mafalki yakan kyautata alwala yayi raka biyu ya roki Allah sauki akan abinda yai mafalki akansa din tunda ba wanda zaibawa sadaka a kasan yanzu yadda dabi,an bahaushe yake da zaran yayi mumunan mafalki zaiyi sadaka don neman kariya da abinda yayi mafalkin dashi din. Shida ba masu karban sadaka a kusa shine yayi nafila raka,a biyu yayi sallah ya roki Allah akan ko menene ya zama mashi sauki a rayuwanshi. Wajen haraban masaukinsu ya fito ko zai dan samu sa,ida a zuciyarshi ya daina jin yadda yake ji din saidai abin kamar ana karawane lokacin ga mamakin shi wayanshice tayi kara ya tura hannu a aljihun shi ya dauko wayan yana dubawa. Unknown number ya gani kuma daga Nigeria ake kiran nasa don lokacin cikon dan shakku da tsoro ya dana karbawa yana maiyin sallama ga meshi yana fadin . Hello Salamu Alaikum kamar ba za a karba mashi ba sai yaji maishi yayi ajiyan zuciya yana fadin wa,alaikum sallam a bangareshi. Sai kuma akai shiru lokaci guda ya daga wayan ya kalla kafin ya sake fadin hello waye ke magana a cikin harshen turancin tare da sauraren abinda za,a fada a dayan bangaren lokaci guda. Sunanshi yaji an ambata full kamar yadda yake karbawa da Ahmed Abubukar ya sake amsawa maishi din again . Sai yaji yace kana magana da Alh Abubakar dan gaskene mahaifinka daga nan Nigeria aka fada a cikin gadara da isa da izza irin yadda manyan da kafansu ya kama kasa suke magana da mutum wani lokaci.