← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 286

Sashe 49

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk juyawa mukayi muna kallon su don wa yanda ke shigowa da kayan da muka sayo masu a lokacin wanda munir ne ya bada shawara haka gare mu aka hada kudin aka sayo. Master munji shiru ne muka biyo bayan ka don mu diba ko lafiya kasan ance ka kula wanda ya kulaka munir ke wanan maganan daga inda uwargarke take tsaye sai kuka takeyi har lokacin tana bubuga kafa a kasa. Jinin jikina nasha don haka kawai naji tsikan jikina yana tashi duk lokacin da wana akuyan tayi kuka, magana yake damu amma hankalinshi na gun akuyan nan. Tabarma tsohuwar ta dauko muna dakinta mu matan tace mu zauna Dije zasu iya zama kuwa ya fada mezai hana mu zauna mu da indan mun mutu akasa za a samu hannatu ta fada. A gurfane nake a can karshe kusa da tsohuwar yayin da take zuba muna godiya da fatan alheri bamuyi aune ba aga wanan akuyar ta balle daurinta ta nufo wajen mu da gudu. Muryan malam tanimu ne ke fadin kai kai kai kada ki soma karki fara wanan ga yayan mutane kaji mun akuya ke baki son bakine a gidan. Amadi din ya mike ya kamata yana fadin aiko na baku abinci da zan fita dazun mana uwargarke ya dago yana fadin abinci ta gani yasa harta ballo a madaurin ta. Kukan nan nata takeyi tana turjewa a wuri daya ya samu da kyar yajata yaje ya daure ta tare da zuba masu abinci saidai takici sai kuka takeyi sosai kamar taga wani abu. Amma ba wanda ya farga da kukan da takeyi sai malam tanimu da akai mai bayanin dalilin zuaan mu yake sa muna albarka da fatan alheri Nikan mikewa nayi daga inda nake tsugunne a cikin tsawala bayan na dan tabo hannatu nayi mata alaman da mu tafi. Sauran suka mike sai anjima mukaiwa tsohuwar wani kuka sosai akuyan keyi da kamar guda na fice gidan ko kafin mazan su fito har na shiga motana ina kokarin tattara natsuwana waje daya. Don harna shiga motar ina ganin kamar wanan dabban zata biyoni ta yakusheni har cikin motar sai waigen kofan gidan nakeyi ina kokarin tayar da motar na kasa saka key din motar da kyau. Wai lafiya kike kuwa Mayana naga kamar a tsorace kike mana hannatu ke fada daga gefena don yanzu itace babban aminiyata ta kut a school din duk inda nake muna tare duk da halin mu yasha bambamda ita sosai. Na samu na tayar da motar ban jira su karasa fitowa ba na fara yin kwana don barin wajen duk suka bini da kallon mamaki a hanya na saukesu nace gida zan tafi nabasu kudin taxis. Na isa gida a firgice dakina na nufa da kyar na samu saita kaina nayi sallah la,asar na koma saman gado na dunkule wuri daya sai ga zazzabi yana neman kamani lokaci guda. Jikin ummah ya bata cewa na dawo sai ta leka dakin ta hangoni kwance hardasu jan bargo na rufa kafana yasa ta gane cewa nice a dakin dai kwance. A,a ke yaushe kika dawo har kika shigo banji shigowan ki ba ummah ta fada saida na yaye abin rufan nace dazun nan na dawo ummah babu kowa a falon lokacin. Lafiya kuka dawo haka da wuri ta tambaya tana kafeni da idanu nace umma sanyi nake ji na dawo subbahanallahi ta fada to kinsha magani nace bansha ba ummah yanzun ne na fara jin hakan. Waike yaushe zakiyi wayaune wai maamah ki tashi kici abinci kisha magani ina zuwa tana fadin hakan ta juya ta fita daga dakin binta nayi da kallo na koma na kwanta. A haka ta dawo ta sameni kwance fada ta fara min dole na tashi nadan tsakuri abincin na hade magani na koma na dunkule sai barci yaso ya daukeni sai naji kukan akuyan nan a kunnena in zabura na bude idona. Yanzun kai Amadi banda abinka ai kowa yasan mu tallakawane a garin nan ko meye abin jin haushi don sun kawo maka wanan kayan haka har gida. Haba Dije ai wanan ya zama zubar da mutunci a gareni yaushe don ina koya masu karatu kawai zasu kwaso wana uban kayan haka su kawo min har gida watau gani mabukaci ko suke ganina . Amma dai akwaika da wani zance Amadi ina kayan nan na dubiya suka kawoma don sun dauka kaine bakaji dadin jikin kaba yasa sukai haka a matsayinsu na aminan ka ? Shiru yayi ya barta tana magana kafin ya mike zuwa ban daki saida ya kewaya ya fitone idon shi ya sauka kan dan tsiron daya fito a wurin katangan nasu. Takawa yayi zuwa wajen tsiron ya kura mai ido na dan lokaci kafin ya juya yana fadin Dije tumfafiyace ta fito a wurin nan haka ? Tumfafiya uwar kwankwanmai baki fita a wurin banza, sirinki sai Allah, mai madaran sihiri, icce kadan da aiki dubu, dama iccen tumfafiyace ya fito a wurin ta fada cikin mamaki. Gaskiya kamar shine nan din ya fada yana kai hannu ga dan tsiron dake tsaye Allah ya kafeshi a wurin cikin hikima irin na ubangiji. Ruwan butan daya rage a ciki ya juyewa tsiron yana gyara mashi tsayuwa kafin ya mike ya nufo wurin Dije din tsaye take tana mai kallon mamaki kafin ta saci kallon inda uwargarke take tsaye. Gani tayi ta kura mai ido zakace mutumce ita ganin ya dago ya bar wurin sai tayi wani girgiza tare da mika ta dona kanta cikin ruwan shansu. Kai Dije ta gyada alaman naganeki wanan tafi karfin dabba shike nan yanzu tabbas akwai wani lamarin boye a gidan su dake shirin faruwa. Zama ya kara yi saman dan dutsen da Dije ke zama tayi sallah yana kurawa kayan dake saman rabarma ido a cikin tunane yaji muryan Dije na fadin ka dibi kayan nan akaiwa malam Tanimu tunda ya shigo ya gansu dazun gidan nan. Hannu ya mika wurin kayan yana mata nuni dasu tare da fadin a diban mai mana Dije abinda kaba wani shine rabon ka ai muma bamu taba zaton samun hakan ai. Allah dai yaima albarka dadina dakai saukin fahintar mutum balle malam Tanimu ai abokim zamane na gaske duk wanda ya damu da damuwanka ai kaima ka damu da tasa. Tana fadin haka ta dago kai tana kallon jikan nata tare da fadin koba hakana ba Amadi shiru taji ta kura mai ido kafin tace wai me kake tunane hakane ko har yanzu akan zancen kake wanan tunane. Ajiyan zuciya ya sauke don shi ba zancen kayan nan bane a gaban shi sai tunowa da sauyin yanayjn da yaga yar mayana a cikin sa wace ta sauke ajinta da daraja ta tako zuwa gidan su yau. Duk da ta zauna kamar yadda yan uwanta suka zauna din saidai alama ya nuna a takure take da irin zamam ko a kyamace da yanayin gidan nasu. Wanan yasa yake gudun yin mu,amula da kowa don gudun irin hakan yayi mamakin yadda suka iya gano gidan har sukazo gaskiya da ake fadan an daina kiwon dabba yanzu sai mutane. Wai ashe dama har wasu a school sun sanda da gidansu shibai sanda hakan ba don yana ganin bai mu,amula da kowa cikin school din ya tsaya matsayinshi da Allah ya ajeshi na dan tallaka. Dije dake kallonshi cikin rashin fahintarshi ya kurawa ido kafin ya sauke ajiyan zuciya a hankali dazun da malam Tanimu zai fita yake magana akan rumfar da zakayi akwai kara da ice ka fara dashi ya baka inyaso alabashin daga baya in Allah ya tarfawa abin nono sai kayi kokarin gina na kasa kona kwano yace saboda damina kasan dai yadda ruwa ke muna unguwar nan ai. Binta yayi da kallo kawai wanda ke nuna alaman ba zaiyi ba ke nan kaiko wataran hutsune Amadi ina laifi da yazo ma da wanan sharan kuma. Dije bana son hada abina dana kowa kin sani dama yace na sayane zan saya din in gwada in gani amma ni kan ba zan dau kayan shi haka kawai na saka a cikin nemana ba gaskiya. Yanzu halinka yaimun kama dana ubanka sak wurin rashin yarda da mutane kana wanan girman kana kara kamanni dashi sosai. Abinda ta fada yasa ya mike tsaye yana fadin sai ana magana ki dauko wani zance kisa aciki na fada maki ki bar hadani da mutumin da baisan nibama. Amadi dole in hadaka dashi don saukin mu ke nan kowa garin nan yasan kai ba shege bane da ubanka tafiya yayi ya barka ya koma kasan su da har yau bao juyo inda muke ba. Ranshine ya kara baci sosai kan wanan zancen da Dije ta dauko a yanzu don shi sam baison a dauko mashi zancen mahaifin shi dukko yadda yake da mutum yanzune zai bata ranshi. Wanan yasa Dije ta daina mai irin zancen nan a gabanshi ko yanzu ma subul da baka tayi ta fada don kamanin mahaifinshi data hango a tare dashi lokaci. Ganin ya doshi hanyar waje Dijen tace ina kuma zaka ba zaka tsaya kaci abinci ba zaka fita da yunwa dadina dakai zuciya kaman kuturu idan kaso. Ko kaki ko kasa kowa yasan mahaifinkane shi garin nan da wayauka ya sa kafa ya wuce ya barmu da sunan zai je duban gida har yau bamu kara jin labarin shi ba kuma. Wajen gidan nasu ya tsaya yana kalle kalle kamar yana neman wani abu aikin dole ya tsiruwa kanshi na gyaran kofan gidan nasu yana tarawa yasala wuta kafin ya koma daga ciki yaci gaba da gyara don yaga gidan ya yamutse kwana biyun da bai samun zama ya gyarashi. Ranan kan a tsorace na kwana don saida hankalin ummah ya tashi don ganin yadda nake firgita da zaran barci ya dan daukeni zan zabura na kadu in bude idona a firgice karshema dakin ummah na dawo na kwanta. Sai washegari bayan na shirya na fito daga daki zan tafi school har lokacin yanayina ya nuna ba daidai nake ba sosai hakan yasa hankalin ummah ya koma kaina. Nafito nake fadin zantafi ummah ta dago ta kalleni tare da fadin kin karyane sai na bata rai ina fadin banjin yunwa sai take tambayana wai meke damun kine haka ? Ko
Chapter 49 · 0% Book details