← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 286

Sashe 72

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

mata hannu yana fadin nace banson wani zance kuma ku fice min zanyi magana da hjy. Hjy kiyi hakkuri hjy karima ta fada ta fice daga falon sai ummah ta dan zaudo daga saman kujeran da take zaune tace hjy don Allah ki yafe muna munyi kuskure hakan ba zai sake faruwa ba itama ta fice. Sai mama dake mikewa tana fadin na kula matan nan da sunana tashigo gidan nan wallahi sai nasa tayi nadama fadowa rayuwata a cikin gidan nan. Keko kikan fara maganan ki yanzu me kikaji ance dake kan abinda ta fada hjy tsohuwa ta fada sai Abba ya amsa da zandai fada din hjy yanzu ina dadin irin wanan abinda maimuna tayi ai gaskiya karima ta fada yanzu. Kece da girki a dakin ki kuma hjy take zaune amma kin kasa girka mata abinda zataci don shashanci kuma in anyi magana hjy ki tare kada a fadi. To ai yanzu ga yar gaskiyan nan ta fadakar dakai gaskiyan ko da hakan wanan saurin sanyin hali irim naka har kazo ka sake ta juyama gida daga kai har iyalin ka kuna kallo. Hjy wanan zancen gaskiyane ta fada wanan itace mai laifi kuma baki son a fadi saiki tare mata to kiyi hankali da karima da kike gani haka sosai don nasan da tana daga maki kafane akan komai . Ficewa tayi bata tsaya jin karshem maganan shiba don bai goyi bayanta ta dau fushi dashi tana kulla hjy karima a zuciyar ta don in batayi hankali zata iya kafa gwaunatinta a wurin Abba don irin haka. Shara ya tashi dashi yana gyaran gida da kone konen da bai samu tsayawa yayi masu gyaran sallaba a gidan yazo kusa don haka ysu ya tashi da gyare gyaren cikin gidan nasu. Yazo gurin wanan tumfafiyan daya fito masu a gefen katangan gidasu din ta cikin gidan nasu mikewa yayi tsaye daga duken da yake ya zubawa tsiron ido yana mamakin saurin girman da dan icen yayi lokaci guda. Wurin randan ruwansu ya nufa ya fara debo ruwa yana zubawa icen zakace an shuka icen ne ana son yayi girma a lokacin . Dijece ta fito daga dakinta da niyar tambayanshi ya jikin nasa saidai tana fitowan idonta yai tozali dashi a wurin tumfafiya ya kura mai idanu kaman yana nazarin tsiron ne. Amadi kardai kuma cireshi kake sonyi tanan din bayan ka barshi ya girma ya gama hayayyefa a gidan nan koda ka cireshi a nan din indai tumfafiyace komai daren dadewa wata rana sai ya dawo gidan nan kuma . Ba cireshi zanyi ba ruwa nake zuba mashi don an dade da dauke ruwan sama baya samun ruwa murmushi ta sake tare da fadin kaiya yaro dai yarone . Kai in banda abinka Amadi kataba jin wanda yaiwa tumfafiya banruwa don ya tofu da kyawo shida keda ruwan Allah a jikinshi ina ruwanshi da wani ruwa can. Ganin bai kulata ba yaci gaba da harkokin gaban shi yasa Dije din barin wurin ta nufi wurin murhunta don ta hura wuta ta dora masu abin kari a gidan. Ta gwama dan icen daya saura masu a gidan cikin wuta na karshen take sakawa a murhun mafarkin icen da mutumin dayazo yana mata sallama a na gobe za a fara azumi ya fado mata a rai. Zubur ta dago daga duken da take ta juyo tana kallon jikin nata dake aiki kafin ta kai kallonta gun uwargarke dake tsaye tana kiwon ta sosai gashin jikinta ya dawo yayi kyau yanzu. Ta zama cikkakiyar akuyan data koshi da kiwo tayi bulbul da ita a yanzu kodai sai kuma ta kasa fadan abindake kasan zuciyar nata . Aikin dake gabanta ta fara bayan ta hura wuta ta dauko tukunya ta dora saman murhun ruwa ta debo ta zuba cikin tukunyan daki ta nufa ta dauko Sauran tuwon jiya daya rage masu gidan ta dawo ta zauna tana barewa. Har lokacin mafalkin na mata yawo a zuciyarta tana kokarin tuno da abinda bakon fuskan cikin mafalinta ya fada a ranan saidai ta kasa gin hakan . Bata jin zata iya tunawa da abin saidai nan gaba kila muryan Amadine ke fadin yanzu idan mutum yace zai tafi garin mahaifina nawa zai kashe kudin mota Dije ? Kaita dago tana mashi kallon mamaki don jin abinda ya fada din a lokacin cikin mamaki ta sake tambaysn shi Manbila fa kace Amadi ?
Chapter 72 · 0% Book details