← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 237 OF 286

Sashe 237

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

zancen nan gaskiyace ko a yanzu yafi kowa don mahaifinshi shahararen mai kudine da yake zaune abuja ashe duk bat da sawu yakeyi a nan din. Haba mama wallahi biri yayi kama da mutum don ni wallahi kamarninsa baiyi kama dana yayan tallakawa ba jifa jiya nan take ya kaso kudi a asibitin nan har muna dariya zai kashe dan jarin nasa wurin son a yabeshi. Ashe yasan abinda yakeyi mune abin dariyan ke nan watau shiyasa ummah bata damu ba ta yarda akai komai tana muna kallon mai a saman ruwa ke nan. Lalai ummah na yarda makirace sosai mama jifa koda wasa bata taba nuna hakan ba gareshi har muna mamakin ita wacan shegiyar data mara akai komai ko itama don a kuntatawa ummah ne ashe tasan komai mu suke kallo uku saura. Ni wallahi tun farko naso nayiwa zahra sinerching dinshi amma sai naji kuna fadin wai fakirine tilis a haka zahra zata tabbata a cikin talauci da tsiya don baida hanyar yin arziki har abada. Kunga da yanzu nice a cikin wanan daulan da kuke fada sai ta mike ta nufi wurin fridge din dake gefe a falon ta bude tana neman abinda zata karya dashi a cikin fridge din. Aisha da mama suka bita da kallo kafin su juyo su kalli junansu lokaci guda Aisha ta fara jan tsoki itama uwar tamere baki kafin tace munafukai don hakan ne ai basu sanar da kowa koshi waye ba a lokacin don wanan salman karshen makircine ita. Duk sukai shiru in ka debe Rukkaiya da yarta dake faman shan wani hura dayayi sanyi a cikin gora a lokacin kafin mama din tayi wani irin nisawa mai kyau tace yanzu meye manufa kun daiji abinda ke shirin faruwa yanzu damu menene abinyi. Me za ayi kuwa mama Rukkaiya dake daga goran hura daga bayansu ta fada duk suka kallota a hasale mama din tace rufa min baki sakarai kawai ke ba abindake damun ki sai bakinci ana maganan mafita kina batunci kina fadin shirme. Toni rabasu zanyi na fada na kara ko zan kaucewa Allah sai nayi na raba tsakanin su muga karshen munafunci indai har wanan maganan gaskiyace wallahi. Lokaci daya duk suka zubawa uwartasu ido cikin mamaki tace kwarai ba wanda keson yaga kishiya ta fishi da ko dingon gashin gira balle na kai. Kai mama don Allah dai ki rabu dasu hakana badai akanki suke zaune ba ai to meye na damuwa tana fadin hakan taci gaba da zukan furanta. Waike halan baku girkine gidan ki ina kula da mun zauna kin fara neman abinda zakici ke nan keda yarki aina fada maku yanzu Faisal baida kudi ko. Yayanshi dake bashi kudin sana,an tundana haifu ya karbe sauran kudinshi a hannushi manejin rayuwa mukeyi a yanzu so ba ko yaushe yake kawo muna abinda zamu dafa ba yanzu. To ba kinji ba irin abinda nakewa gudu ke nan ai yanzu har in zancen nan ya tabbata gaskiyane wallahi kunya zamuji nan gaba sai mutane su fara muna ganin banza. To shine me mama badai mai fadamuna maganan banza badai ga miji tafimu baga uba kome zasu fada su fada Rukkaiyan ta fada cikin rashin damuwa. Kinji shirmenta ko itafa har yanzu bata gane me kike nufi ba mama bata dauki wanan a ci baya ba a wurin mu don Rukkaiya da nake gani zata iya zuwa wurinsu rokoma. Naga alama uwar ta fada tana jefawa Rukkaiya din harara tace wanan ai akwai sakariya a zahirine kawai take fitinanna amma sam bata san inda ke mata ciwo ba ita ko kadan. Zaune yake akatafaren office dinshi dake maitama by pass wayanshi yayi kara alaman shigowan sako ya share sakon don nai faye duba sako ako wani lokaci bashi. Yaci gaba da karanta abindake hannunsa din wanda zasu tura gidan gwaunati don a basu daman gina masana,antan tatse madaran shanu akasa ana ssyar dashi fresh. Sakon ya tuna ya mika hannu ya dauka yana dubawa sskone na tabnatar da shedan cikakken ma,aikaci a kungiyar UNICEF ta duniya daga Ahmed Abubakar Gusau. What ya fada da dan karfi kafin ya tuna shi kadaine a cikin office din lokacin ya maimaita sakon yafi sau biyar yayin da idanunshi ke kafewa ga sunan mai sakon yana mamakin hakan. Tabbas ba karya bane dansane ya turo masa wanan sakon saidai baida layinsa na Nageria wanda aka basa yana gwadawa baya shiga. Kamar da wasa ya danna kira a layin sai ko yayi sa,a ya shiga saidai ba dauka ba har ya katse kira uku ya daina kiran layin nan ya shiga cikin tunane mai zurfi. Haka abin yayi ta damun zuciyarshi sai bayan ya fito office a hanyanshi ta zuwa gidane ya sake gwada sa,an nasa ya kara danna kira da wani layinsa sai yayi sa, a aka dauka. Tare da sallama cikin murya mai nuna cikakken addini ga maishi dan sauke ajiyan zuciya yayi kafin ya amsa sallaman tare da fadin . Yau baba karami ka gama fushin naka ka tuno da mahaifin ka ke nan ina farin ciki da Allah ya nuna min wanan ranan kai abin alfaharine agareni ka gafarce don Allah da mai sunan ka nasan nayi ma laifin laifin da sai ka yafe min zan samu sukuni a zuciyata. Shiru yaji ba amsa hakan yasa ya cire wayan daga kunnensa yana dubawa har lokacin wayan tana a kunne saidai amsawane kawai ba ai masa ba daga bangaren. Jin shirun yayi yawa yasa ya kashe yana sauke ajiyan zuciya don yasan yaron nasa ba zai amsa ba a lokacin ke nan ya lumshe idanunsa yana murmushi a fili. Can yaji sako ya shigo ya dauka suna gab da shiga gidansa ya duba ya fara karantawa kamar haka a cikin sauri da mamakin kalaman dan nasa yasan yana da zuciya shima amma da alaman ta dan nasa ya doke nasa a yanzu. Ban turo maka sako don neman wani abuba a wurin ka face albarka irin ta mahaifa dako wani da yake nema a cikin al,amarinsa na yau da kullun. Zanso ace munyi gaba dagaba irin ta da da mahaifsa sai dai ina gudun dakai da iyalinka ku dauko ina neman wani abune a wurin ku. Zanso kasancewa dakai Abba amma ba a cikin gidan ka ko wani wurin da yake mallakinka ba don kaucewa zargin kwadayin dukiyan ka gareni don dukiyan ka bashi gaba face nasaba kawai ta mahaifi yanzu da nake nema a wurin ka. Inda hali zan shigo Abuja wani satin sai mu hadu a Central Mosque mu gaisa idan hakan yayi maka ko kuma kawai a barshi gaba in Allah ya nufa mu gaisa dakai din . Wani irin yarr yaji alokacin da yake karanta sakon nasa shi kuma ya zauna nan cikin motar ya mayar masa da amsa kamar haka baba karami. Ka gama neman komai a wurina tunda ka nemi nasabata a yanzu gareka kada ka manta nidin daine mahaifin ka wanda a yau jn na mutu dole kana cikin magadan da zasu gajeni. Shima Ahmed din yana karanta sakon mahaifin nasa ya tura mashi da amsa kamar haka masu bukatan arzikin ka su rike don hakane nake gudun zuwa wurinka a yanzu. Idan Allah yai min budi a lokacin zan shigo cikin ku kusandani ba yanzu da ake gudana da arzikin ka ba ka gafarce idan zancena yayi tsaurin karantawa a gareka nagode. Yaron nan ko yana da hankali wanan wani irin zuciyane masa haka har ya kasa cire nufinshi a zuciyarshi duk da yasan abinda ke nan yanzu. Bai mayar masa da amsa ba ya fito daga motan din ya shiga gida a lokacin ne idon shi ya sauka kan motar yasir dake aje ta bugu sosai da gani anyi hatsarin gwajin arziki da ita a ranan. Haka ya wuceta zuwa ciki bai tsaya kula meya faru ba da ace dane can baya zai tsaya ya duba yaji tun a waje ainihin meya faru da mai motan da motan haka . Duk abindake faruwa hjy yabi na tsaye wurin tagan dakinta tana kallon mijin nata da a yanzu suka zama kamar makiya dashi a gidan.
Chapter 237 · 0% Book details