← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 286

Sashe 160

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ko bai kare maku ba ashe don mu ta ishemu gidan nan gaskiya. Ta shigesu tana fadan bakar magana kan akuyan da dan nata ke kokarin dura mata magani a baki amma akuyar tana bin inna da kallo zakace mutum ne ita lokacin. Aiko haka aka wuni da ita yana faman kula da wanan akuyar tasa mai abin al,ajabin sai zuwa rana takai kwance ta bar wanan kukan da takeyi din. Shima din sai wanan lokacin yayi wanka ya fita bayan nayi sallah na samu na kwanta don akwai barci a idona sosai a ranan. Bayan la,asar ya dawo da cafamen shi kamar yadda ya saba kashi biyu nasu da namu bayan nayi sallah na dora muna girki kamar yadda na saba. Har lokacin banji duriyan inna ba na dauka ta fitane a lokacin ashe tana daki ba lafiya tun wanan lokacin datayi wanan maganan ta shiga ta kwanta shine zazzabi ya rufeta zuwa yamma kuma sai ga zawo ya biyo bayan hakan . Ni bansan abin dake faruwa ba har lokacin ina tsaka da aiki a kitchen naji ihun Asmau hakanne ya dauki hankalina da sauri na fito kitchen din hankali tashe. Sai muka hade dashi ya shigo part din da sauri ashe kudi zai dauka su tafi asibiti da ita lokacin nake tambayan shi ko lafiya a gurguje ya bani amsa da innace ba lafiya. Salati na saka na fita da sauri tun dana nufi part din na hangota a yashe kasa tana kakarin amai gwanin ban tausayi na karaso ina mata sannu sai gashi ya iso wurin yana fadin ku kamata a fito da ita. Nan suka kasa kamata din gashi shi kuma ya rigada ya fice a lokacinko ganin yadda suka kasa kamata din dole yasa na yunkura zuwa wurin ina fadin Aisha ta tallaba gefe mu cicibata. Amma kuma sun kasa hakan don inna ba karamar mace bace gaskiya don tana da jikinta ba laifi gashi kuma ta sabe babu lakka a jikinta saita kara nauyi. Ganin shiru ba a fito da ita ba har lokacin yasashi shigiwa yana fadin ku kamata mana sai ya ganni da ita na tallabota a firgice. A cikin tsawa yana kallon kannen nasa yake fadin ba zaku kama mata itaba kun barta da ita haka ina zata iya daukanta ita, , , Aman da inna din ta sharo min a jikina ya dakatar dashi ga fadan da yakeyi da kannen nasa yana fadin subbahanallahi da sauri ya karaso ya kamata daga hannuna ya fita da ita daga gidan. Hankalina duk a tashe yake duk da kyakyamina lokacin ban damu da aman dake jikin nawa ba sai binsuma da nayi zuwa kofa ina kallo suka wuce da ita dukan su zuwa asibitin. Sai lokacin na tuna na koma na gyara jikina a lokacin jin kazanta yazo min Allah yasa dan rigan shan iskane a jikina lokacin don haka na daure na wankeshi na fito ina shanyawa dije ke fadin. Duk ta bata dakin nasu gaau su kuma sun kwasa sun bisu asibitin ba wanda ya tsaya ya gyara dole nice na shiga na gyara dakin nasu na saka kamshi a ciki don ya canza kamshin zuwa najasan datake fitar wa lokacin na fito na koma part dina don karasa aikin dake gabana na girkin dana dora . Basu dawo gidan ba don an bata gado dole abincin da nayi na saka aka kai asibitin tare da wasu kayan bukatu muka rufe gidan har dije muka tafi dubanta. Gaskiya taji jiki sosai zakace ciwon kwana biyu tayi ta zabge haka da zamu dawone muka dawo da Asmau muka bar Aisha can zata kwana a wurin mahaifiyar tasu. Kwanan ta biyu aka sallamota ta dawo gida dole aiki yai min yawa din zatace wanan take so ko wancan haka nayi ta fama da dawainiyar su sai hakan yasa ban samu komawa asibitin dubanta ba wai ashe kuma nayi laifin nan kuma ga hakan. Shine naji yana fada tsakar gida yana fadin in ba,a godewa kokarun yatinyar gaba ai abin ya zama ganin iyaka kuma ? Tana gida tana girki ga wasu aiyukan za ace zuwa dayan da tayi dubuta hakan bai wadatar ba kuma kashe kanta ake son tayine ina part dina ina jiyo abinda suke fadi. Koda ya shigo banyi magana ba don nagama sharan hawayena ke nan ya shigo shima bai dadeba ya fita na karasa abincin rana nakai masu nasu a part dinsu. Tana wani shan kamshi dani nidai na kara mata ya jiki na fito abina ashe wasa sabon girki sai cikin dare bayan kowa ya kwanta ta fara kantara ihun azo a ceceta wata bakar mace zata kashe ta.
Chapter 160 · 0% Book details