← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 286

Sashe 82

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iya duba duniya Amadi yayiwa uwargarke a cikin daren nan don dai ya ganta amma ko mai kalan uwargarke bai gani ba haka ya gaji ya dawo gida karfe daya da wani abu ya kwanta. Da asuba ma hakane ya bazama cikin garin don tun fitowansu daga sallah asuba yake yawon nemanta sai karfe daya da rabi na rana kuma ya shigo gida a wahalce daga wurin neman akuyan. Iya tashin hankali sun shigeshi kan batar uwargarke don na farko ga sabon da sukayi da ita sai na biyu zaman amana da akuyan keyi a wajen su yanzu gashi ta bata daga hannunsu. Duk da dai ba alaman cewa mai ita din daya saye daga hannunsu zai biyo sawunta amma in son samune ai ya sameta awurinsu tunda sun masa kiwo na tsawon shekara da wani abu. Tun suna mamakin hakan har suka gaji suka fara sabawa da batan nata a gidan don kowan su saida ya danyi rama kan hakan daga bayane suka fara warwarewa suna zama daidai. Mun samu munyi jerabawa a dadafe don zafin da kai ya dauka na karatu don haka yanzu zamu shiga hutu munyi sallama da hannatu cewa zata hutu garin sokoto wurin mahaifiyar ta da yanzu take aure a can. Don ita hannatu tun rabuwan mahaifin nata da uwarta a lokacin ya karbe diyanshi dama su biyu ta haifa a gidan ita da yayan ta wanda take yawan kira da ya surajo. Wanda shima yake karatun sa a ABU zaria lokacin don akwai lokacin da nina bata kudin makaranta ta aika mashi don a gaskiya mahaifin mu da yanan basu barin mu zauna hannu babu kudi a wurin mu don tsaro. Wanda sai daga baya na fahinci cewa suna muna hakane don kada mu hanga a wasu ko mu shiga sahun yan matan dake rokon samari. Wanda hakan bai hana komai ba sai dai ya tare wani wajen gaskiya don a bangarena dai ba yabon kai ba zan iya cewa alhamdullahi. Don ina samun kudin ina wa nakasa dani da muke tare laluransu dashi daidai karfina hakama ban karba daga ummah ba don ko yaushe abinda aka girka min a gida shi nake ci haka kayan da Abba yai min dasu nake amfani a jikina. Wanda hakan yasa halin mu yasha bambam da yan uwana dasu kulun sai irin kayan karya din nan suke son sakawa mai matse jiki da nuna hali da son asani ga duk inda suka shiga. A nan ma gida ya suke balle ance zasu fita zuwa cikin gari don ko mutocin su abin kallone gasu da samari manyan mutane ni saima in rasa a ina suke haduwa dasu haka ? Yanzu hutune dole muna gida muna hutu sam na manta da zancen cewa zan tafi abuja gun hjy karima ashe ita zancen yana ranta har lokacin. Ina zaune a falo tare dasu ummah naji ummah na tambayana da cewa ashe zaki tafi Abujane hutu wurin hjy karima ? Ni ummah na fada kafin ta aje ayyah zancen ke mana ta bani amsa tace kunyi maganan hakan da ita kafin ta tafi ? Ni tambayana tayi a lokacin na fada mata nan da wata daya to zaki tafi Alh yace zai aiko a daukeki zuwa Abuja ranan jumma,a kinga ba yadda zakiyi ga hakan yanzu. Idan kinje dai ki iya kanki a zamaki dasu don ba halinta muka sani ba ki iya mutuncin kanki kiyi hutun ki dawo lafiya duk da nasan cewa kedin ba mai rigima bace amma dai ki kula. Naji ance tana zaune tare da yan uwanta ne a gidan yanzu don hjy jesmi ta fada min tana ganin fuskoki a gidan suna kuma gidan suke da zama suma. A nan kuma nasa cewa zansha zagi a gidan nan dama wurin wasu to amma ya zanyi tunda shi Alh ne da kanshi yace hakan dole in barki kije can din na dan lokaci don haka ki kula. Raina ya baci sosai da jin hakan kamar yadda ummah tace ba yadda muka iya kan hakan dole mubi umurnin Abba din kamar yadda yace din. Tunda har hjy karima ta nuna son hakan ya kasance wanda tayi hakan ne don kawai wani manufa nata da ban sani ba amma nafi danganta haka da son ta bakanta wa hjy maimuna tayin hakan dake. Don ko yayane sai hakan ya tabi zuciyan hjy maimuna din itama ta sani don hakane tayi hakan nan don cinwa manufanta ga hakan da zatayi amma dai mu zuba mata ido muga iya gudunta a nan din. Na dade a zaune duk bayanin da ummah takeyi a lokacin ban fahince ta ba ina dai zaune ina kulla dubaran da zanyi don kar naje wanan tafiyan. Naso in nunawa Alh cewa ba zaki ba don kada karatun ki na islamiya ya tsaya tunda wanan lokaci kike samun yin karin karatun ki ina fada yake fadin so nake yace da ita ba zaki zoba kome ? Shike nan umma zan tafi din Allah ya tsareni ya karemu daga duk wani abinki daga wanan tafiyan da zanyi din zuwa Abujan tace amin . Sai gashi na fara shirin tafiya har naga zan wuce ban shedawa Ahmed ba na dai fadawa hannatu da mukai wayan zancen tafiyan nawa. Ta ban mahaifiyar ta mun gaisa take min godiyan taimakon da nakewa yarta din don ta fada mata komai a karshe take fadin cewa idan zata dawo zata ba yarta sako ta kawowa mahaifiyata nima ina kusa da ummah a lokacin na bata waya suka gaisa ta kara jaddada mata zancen sakon. Ahmed din na kira a wayana muka gaisa ya fara min kame kamen cewa wallahi a dadafe ya karasa exam dinshi don uwargarke data bata suna yawon nemanta a cikin gari har yanzu. Uwargarke mutum ce yace no akuyar Dije da na taba fada maki cewa mun sayar kuma ta dawo muna gida wanan dai akuyar taki da kika sani. Nace ai gara data tafi yanzu kaga zan dinga zuwa gidan naku wurin kaka dake tambayana a kai kai ke nan dama dontane ban zuwa wurinta. Dama n akirakane in fadama cewa gobe zan tafi Abuja insha Allahu a can zan karasa hutuna cikin mamaki yace dani Abuja dai zahra nace eh ai kasan a can Abban mu yafi zama yanzu. Anya ba Abba ya shirya zuwan ki bane don kada mu hadu dake ko yasan muna tare har yanzu dakene ? Ban tsamani bayan hannatu akwai wanda yasan da zancen nan yace to shike nan zahra Allah ya tsare min ke nayi murmushi na amsa da amin. Abin mamaki mungama waya na kwanta sai gashi nayi mafalki da wanan bakar akuyan mai bani tsoro ta gidan su Amadi. Wai ina kwance a wani gida mai kyau sai naji motsi a waje nafito don ganin wake motsi wanan akuyan na gani tana kiwo a wani waje mai yawa dausayi mai kyau dan nau,in wurin zakace ba a cikin wanan nahiyar tamu take ba don sanyi da kamshin furannin dake tashi ga iska mai dadi yana kadawa ko ina na wurin. Kallon akuyan nake cikin mamaki kafin ta dago kai daga cin ciwan wurin da takeyi tana kallona nunata nayi da yatsa alaman bake bace ake nema ashe kina nan kina barna. Murya naji a bayana ana fadin kingata nan lafiyanta kalau don kawai mu cirewa Amadi damuwa akanta muka kawota nan ta huta amma ya kwantar da hankalinshi ai zata dawo gareshi nan bada jimawa ba. Ki rike alkawari tsakanin ku shidin alherine gareki kamar yadda kema zaki zamo masa alheri a cikin rayuwanshi amma sai kun daure ga baki dayan ku. Na juya banga kowa ba a bayana saidai muryan dan uwana naji a lokacin watau ya musa don muryan shi sak naji a cikin mafalkin na juya zan koma inda na fito a daidai lokacin na falka daga barcin. Wani sanyine ke dukan jikina lokacin wanda nake jinshi har kasan raina hakan yasa naja bargon rufa na gyara kwanciyana da kyau saidai barcin kuma yaki daukana a lokacin. Har akai sallah ban koma barci ba idona biyu sai bayan nayi sallah ne barci ya daukeni kuma gashi ranan zan bar gusau din zuwa Abuja wurin su Abba yin hutun dole a can. Wanda ni bansan dalilin da zasu nace akan sainaje wanan hutun wurin su ba lokacin tunda yanzu ina da yancin kaina da zan iya zabawa kaina abu kamar kowa. Karfe takwas ummah ce tsaye a kaina take tadani daga barcin cikin fada nasan akwai tafiya a gabana na koma na kwanta kuma to na tashi ga drivers da zai kani sokoto in shiga jirgi har yazo. Gabana ne ya fadi don tunawa da nayi ban fadawa mama ba kamar yadda ummah ta umurce ni inje da kaina in fada mata zancen tafiyan . Dago kai nayi ina fadin jiyan ban dadawa mama ba fa don naje ance sun fita ita da Rukkaiya ban samu ganinta na fada mata ba yau zan wuce. Wanan kuma ruwa ki sai ki tashi kije ki fada mata don kinsan ba zakiyi tafiya baki fada mata ba yazo ya zama min abin magana daga baya bayan kin tafi. Mikewa nayi daga kwancen da nake nabi ummah da kallo don sanin halin mama danayi yanzu a kaina balle naje da zancen zuwa Abuja gareta. Haka na daure na daura gyale a kaina na nufi part din mama din duk da rufe yake har lokacin ban fasa nufar wurin ba a lokacin. Nocking nayi na murda kofan ya bude suna zaune har mama saude da tazo ashe a garin ta kwana na gaidasu da kwana yayin da mama din ta amsa min da kyar ta bangaren ta din. Murya na dan marairaice nace mama dama nazo in fada makine zanje Abuja yau , yayin da mama din tayi wani irin dagowa tana fadin Abujafa ? Yin me kuma nace Abbane yace nazo wai a can zanyi hutu wanan karon wani guntun murmushi naga ta sake a fuskanta lokaci guda tana fadin wata sabuwa. Shi Alh yace kije can kiyi hutun a Abuja kuma bansan da hakan ba sai yanzu da zaki wuce zakizo fada min zaki tafi nace mama nazo jiya ance kin fita da Rukkaiya kuma ban san dawowan ki ba
Chapter 82 · 0% Book details