Sashe 221
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
turai din bamu da labari ko ku kunsan da zancen ne baku fada min ba ? Tana tambayan yayan nata cikin mamaki Rukkaiya ta kalli kayan kafin tayi magana tana fadin mama ina zamu sani muda ba shiga part dinsu mukeyi ba daga inda Aisha take zaune tace mema ya tafi yine turai ? Kilama fa ba turai yaje ba wani kasane nan kusa yaje yawo buga bugansa in bashi ba uban wa zai kaishi kasa turawa kiga tani din nan mai aiki karkadin tsiyane da ita wallahi. Nasani ai duk wani shige shige da kutse kutse itace keyiwa Salmashi a garin nan don nasan a banza sukeyi yasa ban damu da haukan su ba don sawun giwa ya take na rakumi ko ba abinda zasu iya yi dani maimuna. Meko zasu iya mama gata nan kullun wai ita musulma sai kayan hijjabi da takeyi wai ace mata saliha nan ko muguwace ta karshe wallahi. Kai haba Rukkaiya barta da hijjabinta kinsan fa bakauyace dama ummah ni wanan fa bata gabana don banga abinda suka tare min ba a duniya. Baki ganin ko buki akeyi yyanzu Zahra ta daina zuwa ba irin wanan kauyancin na uwarta wani kauyanci kodai ba abin daurawa a shiga kunya dai bai bari ta taka gidan buki kawai. Hakane kuma jifa kayan datasa kwanaki da sunan yar nan da Rukkaiya ta haifa zarban kunya ita ta saka nikejin kunya koda yake suma ai hakan zasuso ganin mu a ransu. Kai dole na bincika ina ya tafi da wanan tsaraban haka wai mama kin kira Abba kuwa zancen kudin nan ina son nayi manyan dinkuna ne na fitan bukin Nusaiban da za ayi tunda nasan Man bazai munsu ba yanzu Aisha ta fada daga inda take kwance. Ke Abban nan naku kwanan nan bansan abinda ke damun shi ba ko ka kirashi sai fada zai hau mutum dashi kamar wanda kare ya ciza yake. Zan dai kara kiranshi inji don ya turo min da kudin yanzu bai bambaruwa wasan dadi sai rayuka sun baci kafin kudi ya fito hannunsa . Yama dade baizo gida ba wanan karon Rukkaiya ta fada sai uwar tace waya damu da zuwa nasa yanzu tunda in zaizo sai ya kwaso wanan bakar kilakiyar matan nasa sun taho tare. Niko naki jinin in bude idona inga yar banza a gidan nan kuma nasan da gaiya take zuwa garin nan don kawai ta nuna muna ita din issasa ce a wurinshi. Bari ma na kira nasan yanzu basa tare ta fita office yar iska ta labe ga aiki tana aikata alfasha a gari wanan kuma ita ya shafa dashi mu dai kada ta dauko muna ciwon wahala azo a mana muna muna zaune kalau. Kai don Allah mama ki bar wanan zancen ai Abba yana da hankalinshi bai yarda insha Allahun hakan ya faru yar iska taga tana samune a wurinsa yasa taki fita gidan ai. Amma tasan kowa bai sonta inba wa yancan munafukan ba ai zahra taban mamaki wai harda zuwa abuja wurin su fa lokacin. Ai kinji yan iyan nan sun tare a lokacin wai Abbane ya saka taje gwalmodiya,i da ya saka dayan ku zuwa mana idan gidan nan bai tashi ba akan fitina. Bin kayan daya aje a gabansu tayi da kallo kafin Dije tace wanan abin arzikin haka daga ina kuma muka sameshi yana zama gefenta yace daga mahaifiyar zahra ta aiko min dashi na tariyana. A, a a duk wanan hakan ikon Allah su dai yan binni sai su nuna sufi mutum wayau ko yaushe wanan abin kaida gani ai kasan da biyu akayishi badon Allah aka kawoshi ba gidan nan. Don ki aka kawo koda baya gari kannen yarinyar nan basuzo muna gidan nan da abin arziki ba mai yawa kuma kowa yaci ni har da goro kursa kursa aka dauro min lokacin har yanzu shi nake dan bantala inaci gidan nan. Inna watau dai na kula ba zasu taba burgeki ba ke nan kinko ga nida zan aje abina inci a daki zahra ta matsa saina diban maku kuma shine na debo dan wanan din na kawo maku. Ciki ciki tace ai dole ta matsa don a mallakemu duka gidan ni yanzu na gane wayau mutanen nan a haka ake kama mutum a rufe mai baki karshe baida katabus ga komai. Ikon Allah kaga miko min nan nikan naci kaga saisu mallakenini da tushe daga can bayan inna Aisha tace nikan abani nima zanci wani mallaka inna kullun kina cin abin gidansu Asmau ta fada tana mikawa Dije roban kusa da ita duk sun matsu a basu. Don ya karawa inna takaici ya dauka yakai a bakinshi ya mikawa kannen nasa guda guda cikin alkakin tana kallo taja tsuki ya dan zauna suna hira da Dije na irin halin ummah tana ji bata tanka masu ba. Nagama komai na gyaran part har lokacin bai shigo ba saida aka kusa kiran sallah ya shigo yayi alwala zai fitane suka hade da wasu yan uwana da sun dade basuzo gidan ba wurina. Sai ranan suka gaisa yasa kai ya fice daga gidan ya barmu dasu bayan mun gaisane suke fada min ai sun kawo min iv ne na bukin Nusaiba na karba ina masu fatan alheri na debo masu wanan alkaki da abinsha na kawo masu. Mun dan dade dasu muna fira kafin suyi min sallama suka tafi na kara gyara dakin naje nayi sallah kafin ya shigo muna da abin sanyi da zamusha. Muna zaune muna firan tafiyan shine wayan shi yai kara ya dauka naji yana fadin baba kuna lafiya ya kwana biyu ya wajen su umma shatu. Yana kokarin dagani saman jikimshi nayi saurin dagawa ya mike ya bar gidan suna magana saida ya dade bai shigo ba don haka nikan na kwanta barci ya daukeni don gajiya. Koda ya shigo banma sani ba saida ya gama abinda yakeyine ya kashe muna haske ya kwanta lokacin ne nasan da shigowan shi dakin. Washe gari ya rigani tashi saida zai tafi masalaci ya tayar dani na tashi nayi wanka na dauro alwala bayan na idar da sallah ta na mike na fara fitana kunna wutan abinci na dawo ciki na fara gyaran daki har na gama na shiga wanka bai shigo ba. Ina mamakin dadewan shi a ranan har dai na kawo komai akan dan table din cin abincin mu na ajemasa na koma na shirya don gaskiya bana son nayi wasa da karatuna. Don shekaran karshe nake duk da ban shiri da Abba kan auren Ahmed amma hakan bai hana ya biya min kudin school fees ba da lokaci yayi sai wanan yasa banson naja abinda za hadani da Abban ya sake bata rai dani kuma. Gashi a yadda naji wai saida yaja kunnen ummah kan kada ta gayawa kowa zancen kudin daya bayar din lokacin daya bata tabani hakan ta kara jamin kunne. Shiyasa a yanzu nake dan fahinta duk da ummah bata yarda in dauka hakanen cewa Abban yana tsoron a gane yana kula mahaifiyan mu damu . Kuma wanan dalilin yasa ita ummah din bata fita gidan Abba ba don yana nuna mata kulawanshi a boye yadda ya dace baidai fitarwa filine wasu sun da hakan tsakanin su. Haka ta koya min hakkurin da muka tsunci kanmu ciki agidan mu ta bangaren mahaifin mu da bangaren kishiyarta mama da kuma mahaifiyan Abba din watsu kakan mu hjy.