← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 260 OF 286

Sashe 260

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin wanan watan azumin ya gane ina da ciki na biyu a jikina shine ke sakani wanan shirun da kuma yawan zazzabi kida yaushe da zaran ansha ruwa ko ace dare yayi ban kara lafiya sai zuwa goman safe zan dan ji karfin jikina in dan samu inyi wanka in fito falon mu duk da dai ba bacin komai amma zami gaisa da dije mu danyi hira sama sama da ira.. Don mafi yawan hira ita da Bahnan yata suke abinsu dije na koya mata hausa shi kuma ubban yana koya mata turanci haka yar ta taso da yare biyu a bakinta duk tana jinsu kuma.. Wata rana bau fita aiki ba dukkan mune a falin nasu zaune yana fira da Dije hannu daya kuma yanawa yarinyarshi wasa ta gudu daga wurin shi ta fada min a jikina. Daje tace kai kai kai kada ki jin masu ciwo yar nan uwarki na fama da dan uwanki ko yar uwarki a jikinta katse abinda yake fadi yayi ya kallo Dije din da sauri. Yana fadin dan uwa kuma Dije tace kai baka kula da cikin jikin matarka bane kome ko kana nufin asibitin da kuke zuwa basu fadama ciki bane da ita ? Dan kallon Dije nayi na kawar da fuskana gefe daya ina ci gaba da dunkulewa yadda nake shima ido ya zuba min yana min kallon mamaki. Baki na turo gaba na kawar da kaina gefe daya tsam ya mike tsaye ya nufo inda nake ya tsuguna daidai saitin kunnuwana yana fadin abinda Dije ta fada gaskiyane princess ? Ban sani ba ka tambayeta tunda ta zama likita yanzu daga inda Dije din take tace kasan halin kan matar ka nima dai naga yawan ciwon yayi yawane yasa har na kula da ashe cikine da ita. Wancan karon muna gida haka suka hanna a gane cewa cikine a jikinta wanan karon sai basu kayar da ita sosai ba amma suna bata wahala yadda ba a ganewa. Nima ba wai na dade da fahitar hakan bane a dai yan kwanakin nan na fahinci hakan kasan dole in fahinta tunda ba yau ake ba ai. Zama yayi kasa a wurin dirsha ya kura min idanu na yan mintuna kafin yace Alhamdullahi bini i,mati Alhamdullahi al kulli halin ya ar,rahman rahimin. Allah ka bamu mai albarka daga inda dije take ta amsa da amin ni dai a zuciyana na amsa masu don nima kamar yadda dijen ta fada ban dade da gane cewa ina da cikin ba. Gashi yace da an sallace zai fara shirin tafiyan mu gida mu kai dije data matsu ita gida zata koma don nan din gaskiya ya isheta. Yanzun kuma ga zancen ciki ina zai kaimu gida haka a yadda nake cikina a wahalce gara dai ai ina nan kusa da bakin magani din. Shine wata safiya zai fita wurin aiki yana tsaye bakin mirro ya daura tie a wuyanshi daga cikin mirror ya kalloni yace gaskiya zancen tafiyan nan na dije nayi cancel dinshi ba yanzu ba kuma sai bayan kin haihu zamu tafi gaba dayan mu. Anya kana ganin dije zata yarda da hakan wace kullun zancen tafiyane a bakinta to ta tafi mana hakan zance mata idan ta matsa min mu gani idan zata tafi din ai. Au sheri zakai mata kuma dijece fa kaidai idan ta matsa ka barta ta tafi din shike nan ai yanzu zan iya kula da kaina tunda naga yadda akeyi da farko. No ta bari kawai idan kin haihu daga baya ma shirya mu tafi dukan mu gaba daya mu mu dan kwana biyu kowa ya ganku sai mu dawo ina ganin haka zaifi ai ko ita nasan halin dije idan na fada zata yardane nace idan ta yarda badon taso ba ka kuntata mata. Ya gama shirinsa ya tako zuwa inda nake ya kai mun kiss agoshi tare da shafo marata a lokacin ne dan dake cikina yayi wani motsi yana canza makwancinsa. Allah da ikonsa sai ga Dijen na fadi da kanta cewa ai yanzun kuma ba zancen tafiya gida gara a tsaya har in na haihu daga baya sai mu tafi din zaifi. Tun nan na kara yadda da irin soyayyan dake tsakaninsu mai karfi ko dai ita ta kawoahi duniya ya tsaya a nan don kiri kiri ranan mun samu dan sabani dashi ta goya mai baya. Amma daya fita ta dawo tana lakashi haba matar Amadi ba fushi akeyi ba ai kinsa na goyi bayansane kawai kada abin yai maku nisa amma ai nasan yaro saida kwabo. Idan kuna gabanshi ki daina yiwa yarinyar nan tsanani yadda yake so sai a zauna lafiya amma ai nasan uwa ke bawa danta tarbiya kiyi hakkuri don Allah. Amma kuma Dije ai ya kamata shima ki nuna mai tarbiyan yaro da wuri ake farawa ba sai yaro ya girma kace zaka tankwasashi ya lankwasu. Ni yadda yake son mu bar yarinyar nan ba tarbiya gaskiya tsarinshi bai mun ba ki daiyi hakkuri yanzu ina yake ya fita sai kuma yamma ya dawo. Keko kina gida da abinki wanan lokacin zaki samu ki sakawa yarki tsoron ki a ranta harta fahinci me kike nufi ko zatayi shegantaka a gaban shi saita kalli isanun ki don wanan kulawan da kike bata ai. Shakuwa tsakanin da da uwa yafi karfi bisa na da mahaifi don ita uwa ko yaushe tana gida tare da abinta tana kuma kiwata abinta yadda takeson ya taso mata. Mm a kashe rigimanne don kada shegen zuciyar nan nasa na fulanin ya motsa ya dauki fushi ba gaira ba dalili damu duka a gidan nan kin dai san halinsa ai. Dije idan yayi ya bari ni ina ruwana da zuciyarshi tunda nima ina da zuciyar nawa tace a,a ke dai ba gashi zancen ya wuce ba yanzu. Mafi yawan lokota a yanzu sakacin ubbanne yana cikin abinda ya bata tarbiyan yaran mu na yanzu don babu uwa da zata haifi da taki dorashi kan hanya mai kyau sai sakariya. Wace bata da lokacin yayanta kamar namiji wai tana fita aiki ta bar yaranta da yan aiki a gida suna gurbata mata tarbiyan yaranta shiyasa a yazu din. Mafi yawan yara so ya batasu sun lalace ta sanadiyar rashin kwabo zakiga a gaban kowa uwa taiwa danta tsawa a cikin mutane yaro ya kunyatata don bai saba da hakan ba. A wurin buki zakiso nunawa mutane kece uwa saboda rashin tarbiya da zai kunyata uwarshi kuma kiga uwar na dariya tana wani fadi cikin zaro idanu ai zamu hadu kasan halina baka bari ko. Yaron da wane shi uwa ko uba ya fada sau biyu bai daina ba duk har yanzu akwai irin iyayyen nan amma ba sosai ba masu jajircewa suba da tarbiya bisa al,ada da addini. Kamar yadda kike sonyi a yarki yanzu don ba kyau yaro kan ya dauki abinci ya zubar waishi yayi fushi yana turje turje a kasa yadda kikayin yayi. Amma yadda ya taso yana fada da sai ki kyaleshi yayi ya gama yarki daice ba zaice sam ba zaki mata fada ba shima zan zauna dashi zan fada mai gaskiya. Da baki da tarbiya kina zama dashi hakan ko yar naku a gidan nan zata tabbata daku zaune don haka kiyi hakkuri don Allah. Bai dakyau idan namiji ya taso mace ta taso a karshe ba a maikyau a tsakaninsu don haka ake son mace tayi shiru ba don tsoro ba. MAMBILA su Abban Ahmed ne zazzaune a gaban manyan shi ana sasantasu shi da iyalan sa don hjy yabi data kai karanshi cewa a kwato mata hakkinta na son dauko shegen dansa ya cusa mata a cikin yayanta yanzu. Wanan ya hasala Alh har yayi barazanan sakinta a wanan karon ranan hjy murja ce ta hana hakan badon Allah ya gyara ba shine kuma bata dadara ba ta dauki zancen zuwa gida wurin magabatansu takai maganan. Wanan dalilin yasa suka halarta a gida aka zauna inda yazo da dukkan iyalanshi don zaman ya fadi abinda yake son fadi gaban kowa. Bayan adduan bude taro da yan jawa bai babban wasune ya fara magana yana kallon kanin nasa cikin kulawa yace to Alh mun gaiyato ku nan ne kai da iyalan ka don maganan da matarka yabi tazo muna dashi. Saboda ta zo nan garin ta kawo karanka a wurin mu kan wani zance da ita bata da labarinshi tun a farko sai yanzu kake kokarin cusa mata ra,ayin hakan . Don tace ita bata san labarin zancen yaronka da a yanzu kake kokarin dawo dashi cikin ku son haka ita bata yarda da hakan ba kome zaka fada ? Don nan wasun mu sunso su fahintar da ita bata yarda da hakan ba shine dalilin dayasa muka nemeku nan muji na bakin kowa don mutuwa akewa gudu. Ya dan gyara zama yana girgiza kai kafin ya dago yana murmushi yace aiko da na mutu din a yanzu yabi bata da gadona saidai diyanta su gajeni don na dade da yanke alakan da zaisa taci gadona a tsakanin mu. Lokaci daya kowa ke fadin subbahanallahi meya kawo wanan zancen yace kwarai in dai don gadon dukiyana suke mi haka tsawon shekarun nan ita da su magajiya na yanke wanan alakan da zaisa suci gadon nawa . Amma a yau Alhamdullahi na fada a gaban kowa ba aure tsakanina da ita a yanzu da na barta gidanane ta zauna a zaman diyanta amma yanzu naga abin bai yuyuwa don haka daga nan ta nemi wani wurin da zata ba gidana ba. Kowan ku nan yasan abinda ya faru dani a baya duk a dalilin sherin magajiya dasune hakan ya faru har kaddaran rabon yaron nan ya gitta a tsakanina da uwarshi har nayi aure mukai zaman shekara uku da uwarshi. A lokacin kuma suka karya asirin suka dawo dani gida a haukace tun lokacin dana dawo din ban fada maku nabar iyalina a can ba. Yayi shiru yana binsu da kallo sai wani yayansu daga gefe ya amsa yace kwarai ka fadawa hardo a lokacin amma akace wuri yayi nisa don haka kabar zancensu wata rana za abi bayansu har hardo ya kwanta dama ba a kara wanan zance ba. Kai kuma ka shere baka ko taba tunawa da
Chapter 260 · 0% Book details