← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 286

Sashe 56

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowana ke nan daga dakina zuwa falo muryan ummace ke fadin ki dauki kayan abincin nan ki kaiwa su Abban ku a falon shi daga nan ki tambayeshi idan suna bukatan wani abin ki kai masi. Ja nayi na tsaya a wuri daya ina kallon ummah din dake magana dani lokacin kafin nace da ita ummah wani abincin kuka girka masu a nan kuma ? Ina su gwaggo sunce an girka masu a gidan hjy ai to Abbah ku yace kada a kawo a nan zamu girka ai kinga ni yaune kawai zan basu abinci daga gobe hjy maimunace zata basu har su bar garin nan don dole nasan dai ya koma zuwa Monday ai. Badon naso ba na dauki abincin dake a shirye nida Tani muka nufi part din Abba din Tani ta tsaya daga kofa nice na fara shiga da kayan abincin ciki da sallama a bakina. Suna zaune saman kujera daya zaune a hade jin sallamana yasa Abba ya dan gyara ga yadda suke zaune din na nufi wajen dinning dinshi yace kawo muna nan zaifi. Na juyo nazo gabansu a kasa na aje saida na aje abinci kafin na dago ina gaida Abba da ina wuni Abba mama kuna lafiya ina ita umman nakune nace tana side dinta na juya wurin matar data kafeni da idanu nace mommy ina wuni ? Lafiya kalau yan mata wanan mamatace itace na sakawa sunan hjyn mu Abba ya fada na mike nafito na karbi na hannun Tani ta juya ta koma ita. Na kai gabansu na aje ina jin Abba na mata bayani take fadin wanan na ganta dazun a part dinsu su wa yancan ne ban samu ganin su ba. A nan na gane sunki yarda data gansu ke nan son nasan suna gidan dai weekend bamu fita zuwa ko ina ki turo min umman taku Abba ya fada. Na koma na isarwa Ummah da sakon Abba na dibi abinci na koma saman doguwar kujera na zauna na fara ci ina kallo ummah tace kina da dabi,an son zama a nan kici abinci ga wurin cin abinci can ki bari. Hakan baisa na daga ba naci gaba da kallon da nakeyi din tare da kannena naji ummah tace min dazun da kukaje gidan hjy abinda takewa ke nan ashe ta nuna maku jan ido ga zuwan ku. Bansan meya yasa hjy take wanan halin ba haka ko kudin da ku nazo daga gidan mu oho barta kawai na iya fada ai dole tunda tasan gaskiya take takewa duk abinda mutum yayi don kansa ai. Can naga ummah tamike ta fita ni dai har muka gama kallon mu muka shige ban fito wajen ba ban kuma san lokacin data dawo part din ba don na kai kannena daki na rufo kofan daga ciki data shigone ta rufe kofan. Washegari misalin tara na safe wayana ya dauki kara ina kwance lokacin ban tashi daga barcin safen da nakeyi ba na lalubo wayan na kara a kunnena bayan na dauka. Muryan Ahmed naji yana min sallama na karba mai muka gaisa yake fadin badai baki tashi ba har yanzun daga barci ba zarah ? Murmushi nayi ina fadin yanzu dai aikatashe ni brother yace manya ke nan har wana lokacin mutum yana kwance yana barci ? Nayi murmushi yake fadin zahar don Allah idan ba damuwa zanzo gidan kune na karbi kudin nan dake hannun ki zamu shiga kauye ne mu sayo wake da gero don azumi daya kawo jiki. Nayi shawara na sayo su da kudin tunda lokacin sayan su ke nan yanzu nabi wanan riban da zan samu OK na fada kudin suna nan yadda ka bani su ban taba ba ai. Na sani yace min nazo ba matsala na karba kazo mana idan kazo saika kirani nafito na fada yayi min godiya ya kashe wayanshi a lokacin nima na mike na daga gado inda na boyesu sunan yadda na barsu na dauko tare da bude wardrobe din na na ciro wani envelop na ciro kudi a ciki na hada dasu na mayar da sauran a ciki. Bandaki na shiga na kewaya na fito na daura gyale akaina lokacin wayana ya dauki kara wata kila dama yana kusa da unguwar tamuce dama. Na dauka ina fadin gani fitowa ina daga wajen get ya fada nace ka shigo kawai ciki zan fito yadda nake dagani sai dogon riga da gyalen dana daura a kaina na fito. Na hangoshi a cikin shiga irin na kauyawa da suke shiga daji da wani hula aja akanshi saidai yana hangoni ya fara cire hulan a kanshi ya nufoni fuskanshi dauke da dan murmushi. Muka hade muka kara gausawa na mika mai kudin zakace wani takardane yadda ledan suke don yadda na shiryasu a ciki. A daidai lokacin su Aisha tare da Rukkaiya suka fito daga cikin gidan namu ko su san sunga mutane a wurin basu nuna muna hakan ba. Daga inda muke yake fadin ina kwanan ku Rukkaiya ta wani kalloshi tasa kai ta wuce mu yace toh ga manya gaisuwan ma sai angadama ake karbawa a gidan ku. Murmushi nayi nace yanzun kauyen zaka ke nan yace dana bar nan mota nacan mun fara taruwa sai mu daga Allah ya tsare na fada naji karan bude kofan fitowa again. Mamace ta fito naji gabana ya fadi ras na juya ina gaida ita tayi dan jim kafin ta amsa tana wucewa zuwa wurin motar dasu Aisha suke shiga ko ta shiga baya sukaja suka fice a daidai fitan su naga duk sun kallo mu suna magana. Yai min sallama shima ya tafi na juya na koma ciki a falo na samu ummah tsaye suna hada abin karyawa ita da Tani nasan sun makara ko kuma aiki yayi masu yawa lokacin. Ummah ta juyo tana fadin yaushe kika fita daga nan nace yanzu wani ne yazo amsan takarda a wurina nakai mashi . Amma kinsan Abban ku yana gari kika fita haka ko ai yanzun na fita na bata amsa kizo ki kai kayan nan falo nasan kila sun tashi suna jira yanzu. Nace to na fara daukan kayan zuwa falon Abban mu nayi sa,a babu kowa a falon har na gama jerawa na juya zan fito naji an bude kofan matar ce ta fito na juya ina gaida ita tace. Aa kece ashe ina jin mitsine ina ciki na leko nace eh da kara fadin ina kwana ta amsa min cikin murmushi tare da fadin sannu da kokari ki gaida ummah taki kafin na shigo gaida su. Wanka na fito duk da ina jin zuciyana a wani irin don ba dadi ko farin ciki a zuciyana mai na zauna ina shafawa naji wayata ta dauki ringing na duba Ahmad din ne ya kirani na dauka. Yayi sallama na amsa ya fara fadin nazo na bude kudin naga sunfi wanda na baki a jiya yawa eh na sani nima bansan me zanyi dasu ba na baka ka kara don naga kana bukata . Amma zarah hakan zai iya hadani dake don kudi ba ayi mai haka Allah dai ya bada sa,a na fada yace amin yanzu kim aramin dai na kara ke nan nace eh aro din na baka. Amma kuma ban faye son kudin wani a cikin sana,ata ba abin dan uwa aibana aani bane na bashi amsan na kashe wayata naci gaba da shirina rana shigar atampa nayi dinkin riga da buje. Har na kwanta na mike na nufo waje kitchen na wuce na dauko goran ruwa na fito ido muka hada da amaryan Abba dake zaune a falon ummah tana fitowa daga bedroom din ta. Matar yar kwalisace sosai don shigarta kawai zai nuna hakan kamar na shareta saidao na daure na sake gaida ita ta amsa itama a cikin fara,a tare da fadin hjy ki bani yar nan taki mu zauna tare da ita Abuja . Ayi hakan tana karatu a nan ai Dear ya fada min ai a can kuke kuka dawo nan yanzu wallahi ummh ta fada mun dawo gida saboda yara su saba da yan uwa da al,adun mu na nan din ta fada kamar yadda Abba da mama suka tsarata a lokacin. Abinda ummah ba ta sani bashi don mama dake son dawowa gida da yaranta a lokacin yasa muma tasa aka dawo damu kusa da ita don kada mu zauna birni suna gida su. Don dama Abujan tace zata dawo Abban yace bai yarda da hakan ba shine tayi makarkashiya wurin hjy inno kakarmu Abba yasa kowa dawowa gida. Murmushi matar tayi kafin tace nayi mamaki keda kike da yara kanana haka kika yarda kika dawo nan ba tare da yaranki sun samu wadatattacen ilimi ba kamar yadda yan uwansu suka samu a can su. Nan ma ai sunayi ba laifi bawa duk baya wuce kadaranshi ai in Allah ya nufa zasu zama wani abu a rayuwa zasu zama din aiko mahaifinsu a nan din yai karatu har ya zama wani abu yau a rayuwan shi. Hakane Allah ya raya munasu ummah ta amsa da amin sai sukai shiru gaba dayan su don matar ta kula da ummah bata da yawan surutu yasa taja bakinta itama tayi shiru . Waya Abba ya bugo mata zata gaisa da wasu abokan shi yasa ta mike zuwa falon na Abba tavarwa ummah part dinta duk ina dakina ban fito ba yinin ranan. Mama ko tana can a family house din suna kwasa dasu gwaggo don takai karan gun hjy saita samu da sanin tsohuwar da aka toshe wa baki da abin arziki akai auren ashe. Wana yasa suka hargirse a wurin ta fara fadan bakaken maganganu garesu suma suka shiga ramawa tafito hasale ta juyo zuwa gida. Dije ce ta leko daga daki sukai arba da akuyanta datayiwa suna da uwargarke da yau uwargarken ta juye ta komawa dije wani abu na daban da Dije ta kasa fassarawa lokacin. Yauma tun fitan Amadi gidan suke takon saka a tsakanin su dalili kuwa shine ruwan kasarin da ya kwana Dije ta gyara masu don Amadi yau sakkon fita yayi bai samu tsayawa yadda ya saba gyara masu ba. Ita kuma ganin ai ruwan baiyi komai ba yasa ta gyara masu shi ta aje tana kokarin juyawa ta bar wurin
Chapter 56 · 0% Book details