Sashe 28
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
nan fa babu me ita har mama kai amma naji dadi wallahi ya musa Allah ya saka mai da alheri. Dan Allah maamah yanzu murnane haka kika dagawa mutane hankali da magariban farin nan haka haba maamah naki kala farin cikin ke nan haka ? Makin ki godewa Allah ta hanyan nafila ko daga hannu ki kara neman kari a gareshi tare da godiya ga ni,iman daya wadatar dake haka a cikin yan uwan ki. Ummah zanyi in sha Allahu don ko a waje nayi zanje nayi sallah yanzu don naga lokaci ya gabato kamin na gama fadi har ummah ra juya ta shige cikin dakin ta ko a lokacin. Sallah na idar a cikin doki don har lokacin kamar a mafalki nakeyi nake ganin kaina wata iri ni fatimatul zara,u nice Allah yaiwa wanan daukakan haka lokaci guda. Don wanan aiba karamin cigabane na samu lokaci guda haka don banyi tsamanin motar mama tafi nawa wani tsada ba don farkon fitowan motar ne lokacin ashe da gaiya ya musa ya zabo min shi duk da uban kudin dakega motan lokacin. Shiga gidan da uwar garke ya fara tozali tana kwance yarda ya barta tano tuka da hakoranta yadda dabbobi keyi idan suna gyaran abinci ya fada masu a ciki. Ikon Allah ya fada a ranshi ya karasa wurin turken da sauri yana fadin Dije mutumin nan bai biyo sawun akuyan nan bane har yanzu ? Sai lokacin Dije tasan da dawowan shi gidan tafito tana gyara daurin kallabin kanta tana fadin tun safe nake zaune ina saka ido naji sallaman shi har yanzu banji kowa ba saikai dinnan daka shigo yanzu. Ina zuwa Dije tace ya juya zai fice daga gidan tace cikin daga murya ina kuma zaka ko kasan gidanshine dama ? Wurin malam Tanimu zan tafi ya bata amsa yana tafiya bai tsaya ba ya fice daga gidan kai tsaye ta figi zani a rataye tabi bayan shi itama. Malam tanimu dake zaune a kasa buta a gefen shi yana shirin alwala ya hango Amadi din ya nufo inda yake zaune kamar hankali a tashe. Hankalinshi ya mayar kan matashin dake tafe wurin shi tunkan ya karaso yake tambayanshi da Amadi lafiya kake tafe haka ? Wallahi malam akuyan nan uwar garke na dije da jiya bakon ka ya saya shine ta gudo daga gida shi ta dawo gida mun dauka zai biyo sawun ta yau sai gashi har yamman nan na dawo na sameta a gida baizo ya dauka ba. Bako malam tanimu ya maimaita cikin mamaki yana kallon Dije dake biye a bayan Amadi din tafe itama a rikice ta karsso tana fadin malam tanimu ka ganmu a wanan lokacin ba. Ina ya fadama akuya dai ta dawo yanzun haka tana gidana nayi bata abinci wunin yau taki cin komai saidai ta sunsuna ta kawar da kai gefe daya. Gaba dayan su kallonta sukeyi lokacin suna sauraren bayanin ta kafin malam tanimu da yaji tayi shiru yace. Bako gaskiya banyi wani bako da kuke wanan zancen ba, eh malam Tanimu gaskiyane jiya yazo nan ya sameni ni kadai a zaune lokacin na dawo daga gidan jabbi mahauci nakai masa tallan akuyan na samu yaje kauye. Na sake zuwa gidan yanka shima bayanan ya shiga gari shine na dawo na zauna nan inda kake hutawa ban dade da zama ba wani dattijo yazo yai min sallama yana neman ka. Nace nima ban sameka ba bari na sallama na tambaya mashi shine na shiga akace dani baka nan kaje daji daukan ice na karbo mashi ruwa na kawo mai. Shine yake fada min yazo wurin kane ka taimaka kai masa jagora yazon sayen dabbane gashi kuma bai sameka ba ni kuma jin hakan yasa na tallata masa uwar garken mu yace a kawo mai ya duba. Bayan na kawo mashine yace ai masa kudi daga sama na yanka mai amma ya tsaya a nan bai nemi ko ragowa ba har dubu biyar na mayar mai daga ciki amma yaki amsa haka yasayeta jakka arba,in cif. Ikon Allah to waye wanan malam tanimu ya sake tambaya cikin mamaki yace dogone fari ya dan rankwafa yana da farin gemu a fuskanshi. Dewa ya,i ni wanan mutum wanene kuwa don wallahi ban gane shi ba sam kuma dana dawon iyali basu fada min zancen wani yazo nemana ba. To shine shi Amadi ke fada min dazun wai yayi mafaki mafarki da asuba da mutumin na fada mai cewa ga akuyar nan ya dawo muna dashi kudi kuma tayi amfani dasu yabashi su halak malak. Kai malam Tani ke faman juyawa kafin yace lamarin da daure kai yake don sam ban gane waye wanan mutumin ba anya ba buda ido akai makaba kuwa Amadi. Kamar ya buda ido kuma dije ta fada a dan firgice ko hasale bayan ga kudi a hannun mu mutumi ya bayar kuma ya tafi da akuya dawowa tayi kawai. Watau Dije zancan nan ne da daure kai yake don sam na kasa gane mai wanan kwatancen da Amadi yai min yanzu. Saukin abindai yaga gida koda ya dawo ya sallama za a bashi abinshi kudi kuma wanan mafalkin wanan abinda zai farune kila yasa kayi wana mafalkin haka. Don haka ba laifi bane indon wanan ne sai kuyi laluran gaban ku da kudin koma waye tunda yasan ni ai ya kwana gidan sauki ga kuma akuyan shi nan a daure sai ya dauki abinshi. Yanzun lokacin sallah ya gabato don haka ku koma gida sai aje ai hakan nasan maishi zai dawo neman ta nan kadan wanan ba abin damuwa bane ai. Allah ya kyauta Dije ta fada ta juya zuwa gida tana magana ita kada tana ganjn laifin su ga sakacin da sukayi na barin akuyan ta dawo gidan nasu tunda yanzu ba hakkinsu bane uwar garken . Shi kuma Amadi ya tsaya sukayi alwala da malam tanimu su mike zuwa masalaci don yin sallah magariba da aka kira a lokacin. Ina idar da sallah hijsbi na kwabe zan nufi part din mama don muyu zancen motan da ita saidai ina fitowa fallon ummah na zaune ta zubawa yara abinci. Haka nazo na wuce ta na ji muryan ummah din na fadin ina fatan baki dauki key ba zuwa wurin ta ba, juyowa nayi ina fadin a, a ummah ban dauka ba ai yana nan dakinki. A to idan dai kikaje mata dashi karbe key din zatayi a hannun ki wanan karamin aikinta kin sani wurinta haka mai saukine.