Sashe 116
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
yarona wani abu akai ma da bai maka dadi ba ko yanayin muhalin namune bai maka ba ? Kai Ahmed din ya kada yana kokarin kakaro murmushi a fuskanshi kafin ya iya fadin wallahi ko daya baba baku min komai banda Allah ya saka da alheri banda abinda zance a kanku yanzu kuma. In bashi ba yaushe zaka kawo maganan gida yanzu kai da ka baro wuri mai nisa kazo nan neman magaifin ka ana tsaka da nema kuma kace kai ka tashi gida zaka. Komawa gidan a yanzu ai baida amfani a gareka ba tare da kasan waye mahaifinka ba har in kana ganin cewa neman da muke masa bai maka bane sai mukai cigiya gurin magabata dama haka shine tsarina na gaba. A,a baba ba sai kaje ba don na gano mahaifina da kaina wanan fitan da mukayi da dan bayaro jiya kuma har nayi magana dashi a jiyan don hakane nake sin komawa gidan ma. Tsaye Shattu take tana sauraren su tun soma maganan su da taji malam din na fadin ko sun mashi ba daidai bane a nan din yasata dan tsarguwa. Sai kuma taji saurayin na fadin ai ya samu ganin mahaifinshi ya gano ko waye shi din haka a cikin ruwan sanyi anya ba dai fadi yayi ba don ya kwantar masu da hankalinsu kada su zargi komai ga tafiyan shi ? Dana kace ka sadu da mahaifinka a garin nan yace kwarai baba don hakanema nake son komaw gida yanzu don na fahinci yabarni da gangan bawai wani matsala aka samu ba. Azoto da talauci ko rashin lafiya ko rashin zarahi yasa ya kasa waiwayana amma yanzun na fahinci cewa hakan ra,ayinshine kawai ya wofintar dani haka cikin duniya. Subbahanallahi duk meyasa kake wanan tunanen ko zato akan abinda baka tabbatar dashi ba gareshi kada ka manta cewa koma yaya yake shine dai mahaifin ka daya kawo ka duniya. Wani malolon bakin ciki Ahmed din ya hade kafin yace duk nasan da hakan baba nasan kuma abinda yasa nace haka baba. Don baya cikin yanayin rashi ko damuwa saima falalan da ko irin mu goma ya watsar zai iya neman mu cikin duniyan nan. Amma babu tunanena a zuciyan shi yadda naga rayuwan shi na tafiya ya samu wasu diyan yanzu ya manta da zancena ga baki daya. Murmushi malam musa din ya sauke a fuskan shi kafin yace kana ganin haka daine baka san meke zuciyarshi ba game dakai ai don haka karka yanke hukunci akan abinda baka sani ba ko kayi zato. Waima waye mahaifin naka dake masa wanan hukuncin hakane don har yanzu ban fahinci inda zancen ka ya dosa ba ta yaya kayi ka ganoshi kuma ina ka ganshi har kasan shine din . Zuwan da wata mace tayi gidan suka tsaya gaisawa da malam din yasa Ahmed din tashi ya bar dattijon a wurin ba tare da dattijon ya farga da hakan ba . Dakinshi ya shiga ya soma hada kayan shi a cikin fushi da bacin rai ya mike ya dago sai kuma ya fita waje ya rasa me zaiyi a lokacin don haka ya nufi inda garken gidan yake yaja ya tsaya yana kallon su. Idon shi ya sauka kan akuyan nan me zubin uwar garke sai yaga kamar akuyan na hawaye lokacin dan kara kura mata ido yayi sisai. Tabbas hawayen takeyi ba karya idonshi yai mashi ba hawayen take sakewa a idonta to hawayen meye ya tabayi kanshi tare da nufar inda take kiwo din. Yana zuwa kusa da ita tayo kanshi tana zagayenshi tana dan tuma kafin ta wani ja baya ta dawo ta kwanta a gaban shi tana cigaba da tuka tare da dan rufe idanunta. Tsugunawa ya samu kanshi a gabata yayi yakai hannunshi saman bayanta yana dan shafata a hankali yana fadin . Allah kadai yasan dalilin hakan a garemu nasan akwai wani sirin dake boye ga hakan koma maye ubangiji Allah ya mayar muna dashi alheri a tsakanin mu., Haka yai ta shafan akuya yana jin wani iri a zuciyarshi wanda shi kadai zai iya fassara irin abinda yake ji a rayuwan shi lokacin sai can ya kalli akuyan yace. Uwargarke kokece ko bake bace in Allah ya kaimu gobe in sha Allahu zan koma gida sai kuma in Allah ya sadamu da alheri sa ke nan.