Sashe 209
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
sayi a lokacin nayi sa,a na samu zan shiga dakin da ruwan muka hade dashi yake fadin wai har yanzu basu shigo min da kayan bane kome ? Basu shigo ba na basa amsa a dadare ya fice da sauri daga part din zuwa wurinsu can naji muryanshi sama sama yana fada na saurara da kyau naji yana fadin ansan menazo dashi da za ace akawo min kayana nan idan na nan ne ai nan din zance su kawo dana shigo. Muryan Dije naji tana fadin in,maba hauka ba mutum da matarshi yanzu za ace ai masa hakan ina ruwanku da abinda yazp dashi din tunda ko bamu gani ba zai kwaso ya kawo muna indai abin amfanine. Ni wanga halin naku bansan inda kuka samoshi ba ace komai na yaro idonka nakai aiko akwai aiki ga hakan indai shi zaki koyawa yaran ki. Nidai na ganshi da kaya niki niki yana shigowa dakin dasu bai ko tsaya shan ruwan dana aje mai din ba saida ya gama shigo da kayan kaf yace ruwane nan zan kaiwa drivern daya kawonine. Naga ya fice da sauri na sake binshi da kallo karo na barkatai kamar a ranan na fara ganin shi a rayuwana don yadda yai min kyau a fuskana gaba daya ya canza min lokaci guda haka. Ko kafin ya dawo na hada mai ruwan wanka na juyo ina kokarin harda wormer dina don akwai shinkafa da miya danayi na danci kadan na aje saida safe. Sai gashi ya fado kwatsam sai nayi niyar gyara in kawo mai tunda dare yayi sosai lokacin naji daga bayana yana fadin mekuma zakiyi a kitchen yanzu. Saida na dan juyo na kalleshi kafin ince dashi abinci nake hada ma sai naji yace ki barshi nazo da abinda zamuci don nasan kafin mu iso dare yayi sosai don haka na riko muna take away a hanya. Yanzu wanka kawai nake son inyi ko zan danji dadin jikina ruwa na bayi na hadama ko na bashi amsa ina cire joni din wayan dana hada sai naji yace masha Allah . Allah yai maki albarka yana kokarin cire nicktie din dake daure a wuyanshi saman riganshi ya wurga min saman kujera ya shige dakin kai tsaye. Tattara kayan daya watsar nayi zuwa ciki na kwashi sauran na zuba wurin kayan wankin mu na kara gyara ko ina sai kamshin da ummah ta aiko min dashi da kannena sukazo. Take dakin har falon ya dauki wani irin kamshi mai dadi har ya fito yana dube dube a cikin dakin baidaiyi magana ba ya bude inda kayanshi suke ya fito da wata jallabiyanshi fara ya saka ajikinshi bayan ya fesheta da turarensa da bantaba jin irin kamshinsa ba sai lokacin. Falo ya fito ya sameni kwance saman dogon kujera na daga kaina sama ina tunane banyi aune da fitowan nasa ba saijin shi nayi ya zauna a kusa dani yana fadin wai Allah abin godiya. Princess Zahra wai fushine kike da Prince din naki haka danayi laifin me har ake kin daukan wayana don ba a damu da rashina a gidan ba ke nan kome ? Dagowa nayi niyar yi in bashi amsa sai naji ya dannena koma kwance a lokacin ne kuma yayi min rumfa da chest dinshi gaba daya ta yadda ban iya dagowa a lokacin. Ga kuma numfashin mu yana dukan juna gaba daya jikinane ke mutuwa lokaci guda saboda yanayin dana kwana biyu ban ji irinsa ba kuma ban shigesa ba sai a yanzu din ya tuno min da wani abu. Kokarin kai bakinsa a nawa yakeyi da sauri na samu na kawar da kaina gefe ina fadin da kyar baka fa rufe kofa ba baka gudun wani tashigo yanzu. Wanda ya shigo nan yanzu gulma ya kawoshi dama don haka yaga abinda yazo gani ke nan a lokacin sai kawai ya cakumoni gaba daya lokaci guda dakyar na samu na kwaci kaina na mike da sauri cikin tsoro. Ya bini da kallo yana kaiwa kwance alokacin tare da mayar da kanshi saman filo yana lumshe idon shi a hankali ya dauki hannunshi daya ya dora saman fuskanshi. A wani irin kasalalen murya mai rauni ya furta Zahra nasan har yanzu fushi kike dani akan wayan mu na ranan ba zaki taba fahintana ba zahra don baki sannin a lokacin da nake kama da mahaukaci ba. Lokacin da nake neman yan uwan da zasu tallafa min kona abincin na dinga samu wanan dalilin yasa kikaga ina mutunta malam Tanimu a garin nan har gobe. Don gidansa kawai nakan dan samu ragowan abinci ko kanzo naci kafin na fita neman abinda ya kamata damu a gari tun ina dan kankani nake fita na nemo abinda zamuci do malam Ladan yana kwance a gida ba lafiya. Malam tanimu shi yakan sani kwashe mai icce in tara komai yawanshi komai rana ko ruwa da iska ya dan bani kudi da zan soyo muna garin kwaki muci nida kakannina a lokacin. Ina kallo kiri kiri kakana malam ladan ya yarasa ransa don babu wanda zai kaishi asibiti asan abinda yake damunsa a lokacin. Gashi da yan uwa kin sani da suka fito ciki daya amma suna bakin ciki dasu taimakawa dan uwasu a cikin jinyar nan nasa dukkansu uku suka kara aure lokacin guda. Har ya tafi yabar masu duniyan basu barmu da abinda yake damun muba kuma suka bullo da cewa wanan gidan gidan gadon sune a lokacin. Sai naga ya girgiza kai ya dan lumshe idanunshi kafin yace ban iya mantawa da yadda Dije take kuka a lokacin amma mutanen nan basu tausaya mata ba saida Allah ya taimaka lokacin tsohon soja nada rai shine ya tsaya mata aka bar muna gidan nan. Amma abin mamaki ashe duk wahalan nan da nake sha a duniya zahra mahaifina yana raye a cikin jin dadi da daulan duniya dashi da iyalinshi daidai da rana daya bai taba tuno yana da wani dan a wani gari ba ya yar dashi ga duniya . Sai yanzu da rana tsaka Allah ya fara yaye min wahala zai bulo yace wai yasan da zamana a matsayin dansa na yarda sam wanan ba zai taba yuyuwa a gareni ba gaskiya. Jin hakan daya fada yasa na dan tako daga inda nake tsaye na tokare bayana da bangon shiga kuryan mu ina sauraren bayaninshi na baya da yake fada in brief cikin bacin rai a lokacin. Zama nayi a tsakiyan kujeran da yake kwance a kai duk da ban zauna da kyau sosai ba a lokacin don yana kwance mike na fara fadin. Haba master kada ka zamo cikin muranen da basu yarda da kaddaransu ba har ka fadi jerabawan ka da Allah ke gwada imanin ka akai mana. Ya dawo gareka yayi nadama sun nuna fitar masa da hankalishi akayi gareka duk dadewan nan yasa bai taba neman ka ba sai yanzu wata kila abin kuma ya karyene a kansa din. Dan yunkurawa naji yayi yakai hannunsa tsakiyan marata ya dan tausa kadan yana fadin ki bini kawai yadda na bisu shine alheri a gareni yanzu. Da zaran na nuna zumudina akan ganin shi ba zan taba tasiri a zuciyanshi har ya tuno da irin wahalan danasha a bayansa ba bance bashi bane mahaifina naji na karba mahaifinane shi har abada amma ba yadda yake zaton zanyi zumudi akanshi ba don yana da kudi har gobe na tsaya a inda Allah ya ajeni bankai kaina garesu ba balle su kara fitar dani daga rankowa. Kadaibi sannu don hakkin mahaifa kada Allah ya tambayeka hakan don ya nuna nadamarshi sosai ga Dije da sauran kakaninka da aka zauna din. Cikin wani irin dagowa yace wasu kakanina ke nan aka zauna dasu nace su malam Bawa mana da sauran mutanen gidan kaf sukazo nan aka zauna dasu. Kai duniya ina zaki damu yanzu su basuji kunyan zuwa akan zancen naba harsu zauna don mahaifina yazo ? Mutanen nan fa Zahra sune suka fara shegantani cikin garin nan har sauran mutane suka dauka hakane nidin shegene banda uba sai naji yayi shiru bai sake magana ba ashe hawaye yakeyi a lokacin. Wani irin kuka mai ban tsoro akuyan nan nasu ta sake lokaci guda saida na dan kadu ina fadin innalillahi bana son kukan akuyan nan wallahi . Don da zaran tayi shi hakan na nufin wani abune mai muhinmanci zai faru a gidan nan na rigada nayi marking dinta da hakan a raina na fada kamar ina sambatu . Ji nayi ya jawoni ya kwantar a samar kirjin shi muryan shi da tanayin da yai magana yasa na fahinci kuka yakeyi a lokacin yana fadin. Kwarai kuwa ba sani don uwar garke kamar aljanna take yanzu abubuwanta na al,ajanini idan tayi sai me hankali yake gane hakan nariga nima nasan da hakan gareta.