← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 231 OF 286

Sashe 231

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

kike nufi. Wai meye hakan ne kukeyi a gaban surukin ku kuma kai kuzo nan Abba din ya fada jin hakan yasa muka taka zuwa gareshi muna gaidashi. Ya kalli Ahmed yace tare kuke tafe kana gari ke nan yace eh nazo sai kuma nayi dan rashin lafiya shine ban koma ba yace jam aiko kaganta bata bugo muna ba ya jikin naka yanzu kuma ? Yace da sauki sai kuma tari ya kama Abban hankalin kowa ya daga a dakin da kyar ya samu ya lafa yana son cigaba da magana da Ahmed din sai tarin ya hana. Mama tace wai maganan dole baka bari har ya fadama sai kajawa kanka matsala kuma tunda likita yace ka samu hutu. Ke haka nake fama dashi fa yanzuma ai naji saukinsa sosai ya fada kamar bai gane me mama din take nufi ba a lokacin. Suyi fira da Ahmed din yana bashi labarin ciwon nasa a lokacin ne ummah ta bude abincin tana fadin ga Abinci nan sukazo ma dashi ko a zubo makane ? A bari a kawo daga gida mana wanan din wasu suci mama tayi saurin fadin hakan shi kuma Abba din yace don me zan bar wanan din ba yata ta dafo min ba zuba min inci jin hakan yasa kowa ya fuske a dakin nan ummah ta dan zuba masa ta dora masa gaban kazan ya karba yana zolayan mu yana ci.
Chapter 231 · 0% Book details