Sashe 193
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zakice bashi yai tafiya ba a ranan don ya dawo a cikin lokaci yaso ya samu ummah a asibitin amma sai akace masa bata leko ba tun safe haka yasa yaja bakinsa yai shiru da zancen. Saidai yana kokarin ganin ya samu dama ya shaka min maganin kamar yadda tsohon ya fada mai yayi Allah cikin ikon shi sai ga Dije na fadin Aisha ta kaita gida tayi wanka su dawo tunda Ahmed din nan wajen hannatu kuma taje gidan su tun safe bata dawo ba. Haka ya tun kareni gadan gadan bai tsaya shakar komai da nufin ya shaka min caraf yaga na bude idanuna dake rufe lokacin don haka zan rufe ido zakice ko barci nakeyi alhalin idona biyu a lokacin. Wani karfi da bai taba zaton ina dashiba yaji nayi mai a lokacin shima hakan yayita maza baiyi wasa ba ya shaka min maganin tare da murza min sauran a fuskana ya shafe . A take nake wani gumji a daidai lokacin hannatu ta shigo dakon hannu ya daga mata alaman kada tayi magana ina karewa sai barci mai nauyi dayazo min ban kara sanin inda kaina yake ba kuma. Wai master yanzu fa gwaggona ta gama fadin anya ba mutanen boye bane suke damun zahra nake cewa a,a likitoci sunce thaphod ne da maleria. Cikin damuwa yake fadin dama kinsan tana dasu ai basu dai faye tashi mata bane ko wani lokaci don farkon haduwana da itama a cikin irin halin nan na sameta a school cilin mota kowa ya watse ya barta saida nazo na taimaka mata. Wallahi ban taba sanin hakan ba batama taba fada min tana da wanan laluran ba gaskiya ai kinsa bata da yawan surutu haka balle ki sani. Ta dan kura min ido na dan lokaci kafin tace iyayyenta sun san da wanan laluran nata kuwa master yace sun sani mana ai don mahaifiyar na tsayene ma abin yai sauki a lokacin. Yanzunma ina ganin wani abune ya faru har hakan ya tashi mata da badon haka ba ai basa tashi irin hakan har su wahalsheta irin haka tun wancan lokacin don har ina dauka sun bartane kwata kwata ashe har yanzun suna biye da ita din. Idon shi ya sauke a kaina na fada sosai na rame hancina yafito sosai a lokacin nayi dan wani haske ga ganin shi ajiyan zuciya ya sauke shi kadai yasan abinda yake ji game da hakan. Makwabata ta shiga diban wutan murhu nan suka tsaya suna tambayanta ya jikin nawa ta fara fadin umm,humm bari kudai yayan masu kudi suna wada suka so. In banda lalaci shigan ciki aka kwantawa asibiti harda su karin ruwa da kwanciya sai wahal da mutane akeyi suna sintirin asibiti shi dan rawan kan tunda ya dawo sau daya na sakashi a ido ban kara gani nai ba har yau dinga. Keko dai da wagga maganan wa yanda ma ba diyan kowa ba sun kwantawa ciko balle ita da ad diyan mai kudin gari yanzu ai haka yayina ga matan yanzu abu kadan atai asibiti a kwanta mazan suyi ta wahala koda miji baida shi. Ashe kegane dauri yaron ga kahin ya auro ta babu dai ababu gidan nan amma tunda ya auro diyaga yanzu daka mai magana zaicewa shi baida shi a,a ankason yayi da rayuwatai . Amma ita yar mulkin ko cewa tayi tana son kan dan sarki ko wuta zai shiga ya samo yanzun na kana ganin an kawo matashiya muko ko o,oho,ho,ho . Ai kesan dama haka zai faru tunda ta hito daga gidan masu kudi sai ta dan tabe bakinta kafin ta juya baya ta dawo da fuskanta garesu tana fadin inda ba masu kudin ko wa take ko a gidan nasu suda banza duk daya a gidan ai . Keko in bashi ba ana daukatan haka zikau a bashi nidai nasan wagga basuwa da ankaimai bata banzata ba da wata a kasa maji magani in gaskiya tta bayana. Keko bar wanga batanci ga danki mana wata yar dattijuwan gidan ta fada daga gefensu cikin takai ke kanki ke nuna ko dan naki ba cikakena bake nan. A,a wallah nikan dana ai garau yake mi att matsalanai ita daita dole akwai matsalan da yasa suka bashi ita don har gobe bincike nakai ko zanji wata matsala da aggareta. Ke arr da wanga halin banzan naki abinga da nikaji ashe shin da gaskiyana baki kaunar diyanga da alheri ke kan Rashida anyi mutumiyar banza wuringa. Shin yanzu mi nice na ganin laihins ga wanga maganan wai gaskiya naka hwadi kuma shina laihi ni kunga ida niyi tana fadin hakan tasa kai ta fice daga gidan da garwashin wuta a hannunta Nan suka sameta suka zageta tas bayan fitanta din don wanan maganan data sake a gabansu shine kuma a karshe ya zamo silar shirin mu sosai da mutanen gidan da muke makwabtaka dasu din. A gidan mu kuma mama taso ta dauki zancen da zafi saidai ummah bata kulata ba sam don haka bata samu wurin yadda mata maganan dake cinta ba a lokacin. Haka kuma koda Abba shima ya bugo yana tambaya ko tana ina da dare bayan ta dawo take fada mai tana gida. Hakama da safe ya sake tambaya duk tana fada mai tana gida yake tambaya bata koma asibitin ba tace tunda ga mutanen gidan mu da abokaina a gidan me zata komayi kuma ? Jin hakan yasa tasan da wata a kasa akwai abinda ake shirin kulla mata yasa ta share zancen gaba daya shima Abba din yayi shiru ya daina tambayanta tana inane saidai idan sunyi waya a yinin ranan ya tambayi ya taji jikin nawa. Sai tace bata kira ba don suce na samu barci mai nauyi inayi sun danyi hiran matsalan kafin ya kashe wayan tun wanan lokacin bai sake kiranta ba ya tambaya yasa ta share ta zauna gida ba don bata damu ba. Yabi taji muryanshi yana fada abinda rabon ta da jin hakan bata san tsawon shekarun da aka dauka ba sai gashi ranan ya kirata da haka kuma a cikon kakausar murya dake nuna bacin rai karara ga meshi. Ta dago itama ta kafeshi da idanuwanta tana sauke nata bacin ranta cikin nasa saidai ganin shi haka yasa nata ya kawu a cikkn dan kankanin lokaci. Fada min dalilin ki na yin almubazaranci da abinci a gidan nan don bansan me hakan ke nufi ba saboda hakan ya nuna rashin tarbiya da rashin tsoro Allah kwata kwatama badai tarbiya ko sanin ciwon kai. Ke nan nice din yau banda tarbiya banda tsoron Allah saboda nace mai aikina ba zata girka abinci a gidan nan ba duk mai sonci ya fito ya girka da kansa aiban daukowa kowa yar aikiba. Ok ashe ita Asabe din yar aikin kice bata gidana dana dauka yar aikin gidanace ita amma yanzu barin kirata mu raba gardama sai asan hukuncin da za a yanke karshe . Daga nan inda yake ya dannawa Asabe din kararawan kira da sauri sai gata dakin hjy yabi din a na ta samesu tsatsaye cirko cirko ba wanda kewa wani kallon arziki a cikinsu. Ganinsu hakan yasa tayi niyar juyawa saiji tayi yace dakata shigo ta tako zuwa ciki ta tsuguna a kasa yace dama na kirakine naji zaman wa kikeyi a gidan nan ne ? Yo Alh ai duk a karkashin innuwar ka muke zaune gidan nan yace ke kika san hakan don hjy tace ke yar aikintane yasa na kiraki naji daga bakinki yanzu idan zaman ta kike a cikin gidan nan da hukunin da zan yanke a yanzu kanku dama. Jin haka yasa da sauri tace dagani har hjy din ai a innuwarka muke zaune ayi hakkuri Alh munyi kuskure dani da uwar dakin nawa hakan ba zai sake faruwa ba Insha Allahu. Asabe yaushe har kika samu daman yin irin wanan maganan da maigidan nan haka sai taja bakinta tayi shiru tace na fadama Asabe a karkashina take na sake maimaitawa ko a yanzun din kuma. Idan kayi hakane don ka tozartani dama to yanzunma na sake fada Asabe yar aikinace da diyana ba da wata ba ok idan yar aikin ce sai ki hada da ita yanzun ku bar min gidana bana bukatan bude ido in ganku a gidan nan kuma. Alh ayi hakkuri ni din zan tafi ku sasanta kanku abin bakaina tafiya tare da hjy ba sai ya daga hannu yana fadin dama abinda nake son naji ke nan kuma najishi a yanzu don haka awa biyu na baku kubar min gidana. Wani kallon mamaki take watsa mai lokaci guda kafin tace lalai namiji ba dan goyo bane yau Alh ni kake bude baki kace ka umurceni danabar maka gidanka akan wata mace ? Eh ba dan goyo din nake ba kema ba yar mutunci kike ba tunda har kikaso tozartani a idon jama,a don kina ganin ban iya daukan mataki a kanki ko me ? Ni kake fadawa na barma gidanka ido rufe haka yace kwarai na fada idan kika matsa gidan zaki barshi a yau ga baki daya don ina nadamar hada zuria dake da wanan hali naki na rashin imani ga kowa. Baki ta bude cikin mamaki tana kallinshi kafin ita Asabe din dake tsugune gefen su ta mike tana kara bashi hakkuri da fadin Allah adaiyi hakkuri a faki gaba anyi kuskure hakan ba zai sake faruwa ba don Allah. Juyawa yayi ya fice daga dakin ya barsu a cikin tashin hankali don har lokacin hjy yabi bata samu rufe bakinta dake budeba a lokacin don mamaki dayasa ta dauke dip a lokaci guda. Sam bata taba tunanen irin haka zaizo mataba a gidan don yadda da amanna da tayi da irin aiyukan mallaka da ake mata akan Alh wanda sai yadda tayi dashi a rayuwa. Ga wayanta yana kara amma ta kasa dauka don yanayin tashin hankalin da take ciki a lokacin dole maishi ta hakkura da kiran da take mata lokaci. Shiko na manzo yana fita malam sale na kiranshi ya dawo don haka yace ya kai kitchen yaba Asabe takaiwa bakin gidan suci amma kadata bari a gane ba a gidan aka girka abincin ba. Zakice bani bace yadda na koma kwana biyu kamar wace ta dade tana