← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 272 OF 286

Sashe 272

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aje yaran yayi ya fita sallah ya barmu nan da inna sai faman kame kame takeyi ita da yarta ga Dije wace ido kawai ta zuba masu tana kallon su domin ranta ya gama baci da jin wai an sayar masu da awakansu duka ga baki daya . Saida ta idar da nata sallah ta juyo ta fuskanci inna tace Rashida baki da tunane baki kuma da tausayi balle imani da har kika iya daukan kayan yaron nan kika sayar haka cikin rashin tunane haba son Allah. Wanan halin naki same yayi kama ace mutum haka zube baida lissafi idan shi dankine kina kurin abinsa nakine ni nawa alhakin ina zaki kaishi tunda kinsan ina da hakki ciki kuma ba baki nayi ba. Umma lokacin auren Asmaune fa na sayar dasu na kara kudin ga sha,ani kinsan buki da cin kudi yadda yake dije din ta tareta da fadin. Auren Asmau Asmau tana da gadon mune ko ita ina nata gadon da ubansu ya bar masu shi nasu ba na sayarwa bane a fitar da ita kunyar kanta ba ? Wai Dije kina ta fada haka don kawai inna ta sayar da awakai ta kara ga aurena shine kike tayarda jijiyan wuya haka tun baki huta ba ? Koni a turai din wai baki waye bane kika dunkulo kika dawo haka sai sababi a bakin ki kamar kina jirace da mutane dama haba dai don Allah don inna ta sayar da abinku ta fita kunya shine me don Allah dai ? Ubanki , nace ubanki da wayewa irin naku ai gara in zauna haka bakauyata da na ci hakkin wani yafi min sau dubu don baku dauki cin amana a bakin komai keda uwarku yasa ki har kike kokarin fada min maganan banza yanzu ko ? Bakin auren naki da kikaki zama dame ya karaku yanzun bayan maida mutane baya da kukayi ai cewa kuke kuda uwarku kuma gadon ku yana can kun baro a Naija meyasa baku koma kun sayar dasu ba azo ai maki auren gatan dashi ? To ki kama kanki tun bakiki baijawa uwarki bacin ran dayafi haka ba a gareni don wallahi yanzu sai in saba maku kan wanan zancen daga ke har uwarku da bata da hankali. Ke Asma tashi tai zuwa inda zakina don Allah kada ki dauko muna magana wurin katobaran ki yanzu kuma cikin gwanewa da tantiranci tace ni ai bakinta ko tayi tasan ba zai kamani ba tunda ba haihuwana tayi ba. Amma yana kama uwarki ko dan Allah dai Asma kitai zuwa inda zakina nace kada ki tsaya kuna tonon asiri da umma kuma sai Dije din tace tonon asiri yafi wanda kikai muna. Ki kama dukiyan yaro ki sayar bayan ya turo maki da kudade masu yawa da zakiyi sha,anin bukin bayan na gado daya turo maki da wanda zaki sauran kayan amfani amma haka bai naki ba Rashida saida kika kama muna dabbobi kika sayar wai da sunan wanan bakin bukin naku da baida rana. Dije don Allah dije ki bar wanan zancen tunda an riga an sayar dasu ta juyo tana fadin ki bari yar nan abin akwai cin rai da kuma wullakanci a cikinsa. Ace duk wahalan da yaron nan yayi da abinsa ba a barmasa ko daya ba wai an kwashe an sayar kan zancen bukin mara kunyar nan ai abin akwai ganganci a cikinsa. Dije ku tashi muje tun ina waje nake jin muryan ki gashi ko abinci bakici ba don ko ruwa ban tsamani an baki da kuka shigo shine ya shigo yake fadin hakan daga bayan mu. Ina take da tunanen yin hakan inda dai zaluncine da yanzun sunsan dabaran da sukayi suka zalunce mu ai kome mutum yayi ai don kansa wallahi ta mike tana fadin haka. Wai me kaya ya daure me cira ke wayyo Allah ke kuma masifa aka kara koyo maki a can kuma zuwan ki turai din don Allah ke ke Asmau you are very stupid na kara jin bakinki a cikin zancemsu sai na bata maki rai sha shan banza kawai mara ta ido. But ta shige daki Dije tace aika kyaleta na dawo ke nan daidai nake dako wace dakariya a gidan nan idan kin dameni wallahi gidan ubanki zaki koma da zama tunda kuna da gidan kakanin ku a can. Kada ki dauka kunci banza sai kun san kuyi wanan ta,asan a rayuwanku indai nina haifi Rashida da cikina sai kawai mukaji inna ta saka kuka ta dora hannu a kai tana kurma ihu. Daukan yaranshi yayi ya juya harshe yana fadin ba zan tashi mu tafi bane shi baisan abinda yasa Dijema tayi wanan maganan ba yanzu. Nikan na mike na kama hanya don duk na matsu mu tafi dama don a gajiye nake sosai lokacin ga wahalan ciki ga kuma gajiyan mota duk a jikina don na dade banyi tafiya irin haka ba lokacin. Aisha ce ta shigo sai ihunta naji tayo kaina ta rugumeni tare da fadin ashe daku akazo yaya bai fada min ba ta sakeni ta kara kallona tana mamaki sai kuma ta sakeni tayi wurin yayansu da sauri tana kallon yaran. Kafin taji muryan Dije na fadin kiyi kukan jini koki kaini ga alkali shi zansan kinyi zuciya ai da sauri kuma ta sake masa yaran da sukaki zuwa wurinta tac Lah dije ta fada mata a jiki tana murnan ganin mu a lokacin taji yaya na fadin Dije mu tafi nakai yaran nan suci abinci yunwa suke ji lokacin cin abincinsu yayi. Inna zaku kuma ta tambayi dijen tace a hasale inda akafi son mu da tatalin mu tana wuce Aishan tana fadin ai zan dawo gidan inga karyan mara kunyan yarki. A ina kuka sauka kuma shine fa na dawo da wuri in gyarawa yaya daki nace ai ki barshi a gidansa daya gina sabo muka sauka dama jiyan da mukazo. Kukan inna ta bari tana sauraran zancen mu da Aisha da tace lah yaya yayi gina a garin nan dama bamu sani ba yaya nayi maka murna sosai wallahi dama na dade ina tunane yadda zai sauka a nan yanzu. Lallai dani ko za a wanan gidan yau babu inda zaki zauna gidan uwarki tunda nagane kasheshi kuke sonyi da ransa don Allah umma ki bar zancen nan hakana don Allah. Inda nasan sayar dasu zai zama magana haka nima da ban taba masa kayansa ba ai har gashi saboda su umma kina kokarin yi min baki waime aka sayar kuma Aishace ke tambaya don bata san ba,asin maganan ba a lokacin. Rufa min baki duk bakinku daya ai anga mun tafi an hade kai an kamawa yaro dabbobinsa an sayar a cika talle da miya ko ? Hannu nayiwa Aisha tazo guna da sauri na riketa muka bi bayansa daga can nace tazo muje gidan namu don a gaskiya na hango rashin hannunta a cikin lamarin . Daga can din kuwa muka shiga mota kafin ya koma ciki ya fito da Dije data tsaya fada a cikin gidan tana bata muna lokaci ya samu ya fito da ita da kyat yasata mota muka tafi. Saida muka danyi nisa ya furzo da iska daga bakinshi yana fadin wai Dije meyasa kika tanka akan dabbobin nan tunda ba zaki gane komai a cikin zancen ba don ni na gane inna yanzu abinda yaranta sukace take bi. Ba hakana bane yaya kace abinda Asmau ta fada dai, nikan ai sun bareni a gefe daya don ina fadin gaskiya ko lokacin da suka sayar da dabbobin nan saida na nuna hakan bai dace ba. Amma inna ta nuna min kayan dantane ai don haka nafitar da bakina a ciki ko kuma ta saba min kuma idan nayi waya na fada maku zancen wallahi sai ta saba min ina ji ina gani Asma na zugata aka kira mai saye ya sayesu wullakance yanzu haka akwai uku da nake gani a gidan mani a nan unguwar mu . Wani Mani dai mani da Aeka tace shi wanan mutumin mai sankon nan da katon ciki dake zama gidin darbejiyan gidansa kullun da dabbobi. Ai kuwa kowa yayi mai tsaye a garin nan sai ya dawo min da akuyata don sammako zan masa a gida in tara masa mutane hakan ma yafi wallahi bakiga tayin wullakancin da yayi ba amma inna ta shige daki da Asma waisuyi shawara sai gasu sun fito suna fadin sun sallama masa akan ashirin ashirin kan ko wani dabba din ya kwashi banza ya tafi. Kaji ko kaji cin amma wanan dabbobin da sukaci suka koshine za a sallama a hakan don rashin sanin ciwon kai Dije ai baki san rashin sanin ciwon kaiba sai kinga abinda yanzu Asmau take saka ina yi kamar wacce ta asirceta. Don ina magana sai cewa inna tayi ina bakin cikin da yar uwata a yanzun don naga ci gaba ya sameta nake hassada da ita duk zancen da Aisha keyi bai juyo ba saida ta fadi wanan kalamin ya juyo yana fadin. Cigaban meya sameta da har ake bakin ciki da ita na lalacewan da tabari tayi hakan a yanzu ko na batawa kanta lokaci shine nima nace ai yaya karshe dai dakin Dije na bude na share na koma ciki don ban iya ganin takaici. Naji dadi sosai lokacin da yan gidan su Anty sukazo suka kwashe mata kayan ta don wallahi da yanzu anyi abin kunya don da ba a samun komai a dakin nan nata don zuwa lokacin har an bude taganku ashe ana shiga ta nan ana diban kayanta ban sani ba. Salati me karfi dije ta saka tace wallahi ko dije abu daya ne bansan waye yake wanan aikin ba a lokacin tunda ban zama a gidani lokacin na fara karatu bani zama sosai dasu a gida. Shigowan mu get din gidan yasa kowa yin shiru banda Dije dake faman sakin salati irin nasu na tsofi a lokacin muka fifito a motan zuwa cikin gidan inda muka samu mama mai aiki da yarinyar nan binta sun gyara gidan tsab yadda yake so sai kamshi ke tashi ciki. Yaran ya aje ya nufi dakinshi ban tafi ba saida naba yarana abincin sukaci na samu na shiga dakina na kwabe kayan jikina don in huta saboda
Chapter 272 · 0% Book details