← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 286

Sashe 88

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matane sunsha kwaliyan su sosai zasu fita saidai ganin masu gidan yasa suka nufo dining din suna gaidasu da kwana a take naga Abba bayan ya amsa ya dukarda kanshi taci gaba da cin abincin shi. Sai addua nakeyi a raina a wurin don na sheda dayan wace jiya na fara ganine dana iso kafin mommy ta dawo ganin cewa ba zanyi masu magana ba don ko daga kai na kalli inda suke banyi ba alokacin. Zahra meet my sisters lawisa and Aina suma suna zama damune a nan gidan though suna service ne a yanzu su suna gaba dake ke nan ga komai. Ina kwanan ku na fada na kawar da kaina ban daiji amsan su ba nadai ji suna sallaman yar uwan tasu da fadin mun fita sai mun dawo ke nan tace yauma ba zaku karya ba ke nan? Mun makara zamu karya a can daya ta fada nidai ba zance naji sun gaisa da Abba ba ko sun sallameshi har suka fice daga gidan. Mikewa nayi ina sake kujera daga inda nake zaune OK zaki koma kifito anjima fa kici abinci ta kara nanata min nace to mommy na juya ina fadin Abba adawo lafiya ya amsa min kamar ba Abban mu dana sani ba a baya. Don gaba daya sai naga dabi,un shi ya canza min ga baki daya wanda hakan ya daure min kaina na kasa fahintar komai sai na nasa ko har yanzu yana fushi danine kan zance na da Amadi ? Ko kuma wani sabon sauyine kuma yazowa Abba din a yanzu ya daina yawan damuwa damu yadda ya saba nuna kulawanshi garemu a baya. Na fara kula da hakane tun zuwansu sallah inda baida lokacin kowa koda yaushe suna tare da hjy karima a falon shi ko sun fita zuwa unguwa ko a part dinta sunfi yin hakan a ranan girkin mama yafi sintiri part din hjy karima din. Sai gashi naga haka a nan kuma danazo dan kana daya kawai danayi a gidan na fara fahintar hakan ga Abba din nakai wani lokaci kafin na danyi barci sai shadaya daidai na falka don lokacin karyawana da yayi har ya wuce a lokacin. Namike daga saman gadon na nufi bandaki na kewaya na fito falon gidan na nufo da har lokacin kayan abincin na nan yadda suka fita suka barshi a wurin. Nasan mommy tabada umurni kansu aje min shi kada su taba haka kawai sai naji habkali bai kwanta danaci ba kitchen na nufa wurin masu aikin dake dan shakatawan su a lokacin. Ga wakan coci yana tashi a wayansu dayan ma tana kwance ta daga kafa ido rufe tana bin wakan da suke saurare din sai dayan dake tsayene tana fere doya taga shigowana. Sannu da fitowa tace min nace sannu kema nace ko zan iya samun ruwan zafi please na tambayeta da sauri dayan wace naji hjy ta kira da Tabitha ta mike zaune tana fadin. Anty kin tashi mene kikeso ayi maki a lokacin na dan kakaro murmushin dole a fuskana nace ina son ruwan zafine sai naga tana kokarin mikewa zaune da niyar tashi ta dora min ruwan. Nace no barshi barin dora kawai don nasan komai saboda wasu kayan kitchen din ma wanda mukai amfani dasune a baya har yanzu basuyi komai ba don ni dai banga wani abu sabo sosai ba a gidan da hjyn tazo dashi ba. Duk kayan da ummah ta barine da zamu koma zamfara Abba yace ta barsu nan koda zuwa ya kamata ya saka masu komai a can ma shine ummah ta barsu nan din don mun tafine da sunan zamu dinga zuwa hutu wurin Abba din lokaci lokaci. Zamu komane ne kawai gida mu saba da yan uwa da al,adun gida irin namu na can tundai wanan hearter dana daga ban mantawa fita mukayi da ummah da kawarta ta sayoshi a sahadda store lokacin sun bude tsore din sabo sabon budewa mukaje. Ban mantawa don ina da wayona a lokacin batayi amfani dashi ba sai daya dade aje sai haihuwan jamila ta fito dashi gashi ba a dadeba muka bar Abuja din zuwa zamfara. Wani bakin cikine ya kama min zuciyana nake fadin don me Abba yakewa ummah hakane wai duka maza dama haka suke su dinga banzatar da matayesu akan wata kodai Abban namune kawai halinshi haka wai. Iya sanina a nan Abuja matan da ummah ke ma,amula dasu makwabtan mu su kadaine ga mazajen su suna kuma zaman lafiya dasu hakama yayayen su suna jin dadin su. Amma mu ke nan yau ace wancan gobe ace wancan ke nan mu bamu da wanan gatan to don me na nasa don umma bata da iyayye masu karfine ko ? Na dawo nace aiko mama ba wani karfi a gidan su da taimakonta suke kuri kaf din su kuwa kodai don tana uwargidane kuma to ai ba wani ragaman uwargidancin da take samu a gidan namu. Tunda komai mama ke gudanarwa tun komawan mu gida din na gani tomeye hakan dama haka maza masu kudi sukene wai kome ? In hakane kuwa gara mutum ya auri wanda baida komai su zauna lafiya da miji yafi anty nace kawo na dora maki ruwan Tabitha ta fada na dawo daga dogon tunanen da nakeyi nace . No barshi kawai in dora nagode tace da kin kawo aikin mu ke nan ai yanzu mu nace ba komai ki huta abin ki na fara daureye jugdin saida na wankeshi tas don kyaman da nakeji. Sannan na tara ruwa ya cika na aje ya dan sha iska ina tsaye ina kara bin kitchen din da kallo naji muryan Tabitha na fadin anty nace abinci yana falo hjy yace kitchen in kin tashi . No bana cin abinci da safe na fada ku dauka kuci kawai ku wanke kayan na fada sai naga sun kalli juna sunyi yarensu kafin Jenet ta juya zuwa falo ta dauko kayan ta shigo dasu ta koma ta kwaso saura. Wanan miyan naga sun bude sun kalla nayi kamar bansan me sukeyi ba sai naji sunyi yare a tsakanin su can naga sun fara tsame abin cikin miyan kifine manyan yanka zai kai biyar. Sun tsame daga cikin ruwan miyan suka aje a cikin plate sai nagata juye ruwan miya ya wuce a sink ta tara kifin ta daure sai lokacin ta dago taga ina kallonta tace. Miyar ne idan mun barshi ciki zai iya bata kifin shiyasa muka zubar dashi ai murmushin yake na sake a gefen fuskana lokaci guda na juya ina kallon abinda nakeyi suko sunata yare a tsakanin su. Hjy don Allah kada ki fada ma Ajiya cewa mun zubar da miya zata iya koran mu gidan nan yau din nan basai gobe ba don Allah kada ki she ba kaine kaci ba fada zatayi muna sosai idan tasan hakan. Murmushi nayi kadan nace kada ku damu ba maiji idan ta tambaya ku fada mata naci sosai kadan na rage kukaci ok anty mun gode dayan na aika ta hado min kayan tea na aje a dakina harsu complaints da goldenmore sugar da sauran ajewa daki don bukata sai gata tadawo min da canji nace suje su rike. Wanan sayayya su na mayar abincina a gidan sai kuma indomei nakan bude fridge na dibi nama in girka muna a sayo bread mu zauna muci dasu ko Sydney kifin gwagwani. A wanan karon na kara godewa Allah cewa ni din na kasance ba mai yawan cin abinci bane sosai sai hakan yai min dadi don idan mommy ta dawo nakance na koshi da abincin dare bana cin abinci da dare ni. Hankalin mommy a kwance don tasan wasu dama haka suke a rayuwa basu damu da abinci ba ranan weekend kuma tare muke ci da ita indan tsakwara duk abinda naga taci a cikin jerin abincin. Ranan zata fita nake fada mata cewa zan shiga gidan makwabta dana sani na gaidasu naga sauyin fuska sosai a wurin hjy din saidai ta daure tace min kada ki jima a can din. In sha Allahu mommy ba zan tsaya don ummah ta fada masu zuwanane kada suga ban shiga ba tace is OK kamar na sani na dauki kayan shayin da sauran abubuwan da nakeci na boye inda bata gani. Don bayan fitana mommy ta shiga dakin nawa ta bincika kayana saidai ba wani abin assha da tagani a cikin kayan nawa. Tafito can ma ta tsure su Tabitha da tambayoyi a kaina sukace basu san komai ba a game dani don idan na fita bana fitowa barci nakan yi ko karatu a falo. Ban magana da kowansu abincifa ta tambaya sukace ina ci amma sai rana yayi sosai nake fitowa in karya saita washe baki tana fadin shiyasa nakejin dadin aiki daku Tabitha. Ban jima ba na dawo muka hade da mommy zasu fita take fadin har na dawo nace mommy sannu da gida ta amsa min tana faldin zata fita sai ta dawo nayi mata adawo lafiya na wuce zuwa dakina. Ina shiga dakin nabi dakin da kallon don na fahinci an shigo min dakin lokacin sarkokina da wasu abubuwa na duba suna nan yadda na barsu ba a tabasu ba. To me ake nema a cikin kayana na tambayi kaina ni daya a dakin saidai ban nuna nagane haka ba ga kowa don kosu Tabitha baki na rufe masu ina basu kayan kwalan da dan kudin kashi da wanan na saye su a gidan. Dije zanyi tafiya saina dawo ya fada daga kofan Dije din Amadi sai ina kuma yau tau zamu diba dai wani gari can inda ake samun hatsi da sauki mu dauko don haka zamu kwana daya ko biyu a can din saidai idan Allah ya dawo damu lafiya ga wanan ki rike a hannunki ya ciro hannunshi dake cikin aljihu da kudi yana mika mata. Karba tayi tana saka mashi albarka ya amsa da amin tare da fadin na tafi a gafarce mu yasa kai ya fice daga gidan dije bata daga daga inda ya barta ba aikai sallama a gidan ta amsa. Wani yarone ya shigo yake fadin ance anawa Amadi sallama Dije ta amsa da fadin Amadi yanzu ya fita daga gidan nan yayi balaguro. Yaron ya juya ya
Chapter 88 · 0% Book details