Sashe 16
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
gefen mama din ta dan jaye tana gyara zama. Lafiya naga kin hade rai haka ta kallo shi tana fadin duniya na hada haka kawai za a ce wai na hade rai a kan me kan wa yancan banzan iyalin naka kome zan hade raina. Murmushi yayi yana fadin sune kuma banza yau da bakin ki ke fadawa iyalina haka maimuna wai meke damun kine haka wai ? Lokacin su Aymana da Aisha suka fito daga dakunan su jin muryan Abba din a part din nasu suka fara gaidashi kafin su fara zuba mai shagwaba yana biye masu. Daddy sai ka ban kudin gaskiya don in katafi saidai muji cewa ka bar gari kila Aisha ta fada tana wani shagwaba kamar karamar yarinya. Dole Abban yasa hannunshi a aljihun shi ya ciro kudi masu yawa suma ya mika masu har lokacin mama na zaune sai busan iska takeyi tana jan kamshi ita a dole an mata ba daidai ba. Yayin da shikuma Abban yake kokarin ganin cewa ya daidaita tsakanin shi da mama din ita kuma tana bultsewa. Ranan ya kamata ya juya don wayan daya samu amma dole ya daure ya kara kwana don mama suka daidaita kansu suka koma daidai. Shi kanshi Abba din a lokacin ba zaice ga dalilin dayasa yaji lokaci guda ummah ta tsaya mai a rai haka ba har yake dan jin tausayinta ita da iyalanta a wanan zuwan. Don baibar gari ba saida yayi dabaran ganin ya kyautatawa kowa don ya cikawa ummah account dinta da kudi har saida tayi mamakin ganin hakan wanda da dane saidai mama ta bata idan yatafi tace Alh ya basu su rike. Lokaci guda itama ummah din tana jin wani son mijinta yana taso mata dan lokaci lokaci a ranta wanda yasa Abba yana isa Abuja ummah ta kirashi tana mashi godiya tare da addua mai inganci a gareshi wanda hakan yasa shi lumshe ido a cikin wani yanayi. Yau kwana biyu ke nan yana zuwa school yana dawowa hannu sake ba kamar yadda ya saba rikowa Dije dan ledan abinda ya samo a wurin aikin shi ba. Saidai Dije din ta amsa gaisuwan shi sannan tayi mai sannu kafin tace da alaman dai kunyi fada da shugaban aikin kuce kwana biyun nan ko ? A cikin mamaki ya juyo yace tun wancan ranan ban koma wurinta ba don na samu labarin cewa tace idan nazo korata zatayi yasa nayiwa kaina kiyamalleni da ita. Ka kyauta gara da baka tafi ba ina amfanin wullakacin Allah daya bata bai manta damuna muma idan da rabo namu yana tafe a wurin Allah. In sha Allahu ya fada tare da jingina jikinshi da bangon ginansu ya shiga tunane don yasan abinda tsohuwar keyiwa dan abincin daya saba shigowa dashi gidan da yanzu ya daina yasa ta kai ga magana har ta fahinci akwai magana. Itama dijen shiru tayi na dan lokaci kafin taji muryanshi yana fadin sana,a nake son in nema in fara yi saidai jari shine matsalata a yanzu don sana,a saida jari mai dan tsoka a hannun ka. Tau Amadi kace kayi sana,a babu wani kudi ko abin sayar a hannun ka indai ba wa yan nan dabbobin da su kawai muka mallaka a yanzu ba. Saidai idan su din zaka kama ka sayar saika rike dan kudi a hannunka kai ya girgiza mata tare da fadin mu daiyi addua Allah zai kawo muna mafita ga komai. Allah ya nufa ta fada a sanyaye sai kuma ta dora da fadin dadai kabi shawarana sai ka dauki ita uwar garken kakai kasuwa kudin sai kayi amfani dashi Allah yasa akbarka kaga saura kwara hudun in Allah ya raya muna su sai a more masu kuma gaba. Dije ki bari na kara addua a kai insha Allahu Allah ba zai barmu haka ba da yardan ubangiji da fadin haka yai shiru yana tunane ba komai yake tunane ba sai halin rayuwan daya tsunci kanshi a ciki . Yau ace mahaifinshi da mahaifiyar shi suna raye amma yana zaman kunci irin na marayu don dan wani dalili mara tushe da mahaifin nasa ke takama dashi a zuciyar shi. Har yakai dije na magana dashi lokacin bai jiba yayi imani da abinda zuciyar shi ta yanke mashi akan mahaifin nasa. Dago kai yayi da idanuwan shi da suka kade sukai ja kallonshi tayi lokaci daya sai taji jikinta yayi sanyi ta fasa fadin abinda tayi niyar fada mashi din a lokacin . Shirun dayayi yawa yasa ta dauko mai zance makwacinsu da maciji ya sara a daji jin hakan yasashi dago kai da sauri yana fadin subbahanallahi shi malam Abashe din ? Tace kwarai taci gaba da fadin dazun nan aka dawo dashi daga gona inda abi n ya sameshi suje noma gonan su a can ya tabashi aka daukoshi zuwa gida. Yanzun dai suna asibiti dashi ance magani dubu sittin da biyar na shiga masu tanzango abin ba dadi gaskiya saisai Allah ya gyara kawai. Bari inyi sallah sai in leka gidan in yakama har asibitin sai in tafi jn gaidashi can tunda yau naga babu hadari a garin ya mike ya nufi inda suke aje buta. Washegari na tashi da sauki sosai don haka na shirya zuwa school lafiya lau na shiga mukayi darasin farko bamu fito ba sai sha biyu da rabi. Wurin motana na nufa na bude shiga na zauna nafito da goran ruwa tulawa cikina saida nayi rabin ruwan na daga goran na cire a bakina. Kainane ya sara lokaci guda hakan yasa na dora kaina saman sitiyarjn motana na dukar da kaina lokaci guda motar ta fara horn hakan ya jawo hankalin mutanen dake dan sintiri a wajen. Wai yarinyar can tana da hankali kuwa tun dazun take duke mota na horn haka wasu gugun matasa dake zaune suke fadi daga bayan su Amadine zaune yana karatu saye yake a cikin wani dogon wandon jeans Pdayo kode sai wata shirt fara mai zanen kanana kana tsaye jikin rigan duk da farine shima rigan ya kode saboda tsufan da yayi shima. Dan juyowa yayi inda yake jin horn din yanatashi ya hango mace ta kifa kai saman sitiyari mikewa yayi da sauri ya nufi wajen kamar wanda ake ingizawa zuwa wajen. Ganin ya nufi wajen ya kara jawo hankalin sauran matasan dake zirga zirga a wajen da sauri ya karaso yana dan magana daga inda yake boyar Allah lafiya kike kuwa ? Shiru yaji ga goran ruwan da nasha ya zube a jikina rabi a kasan motar yana tsiyayaya kasan motar kai ya fada yana matsawa wurin ke boyan Allah lafiya kike kuwa ? Karan horn din ya isheshi yakai hannu ya dafa kafadata da sauri ya jaye hannun nasa yana fadin kai don Allah ku taimaka wanan suma tayi ko bata da rai ? Sai suka fara dan ja da baya kowa yana gudun jefa kanshi cikin wahala don haka basuga abinda zasu tsaya sujawa kansu matsala ba a nan. Don Allah ba wanda yasan ko wzcece ita ya fada da dan karfi mayanace fa yar gidan mayanace wanan ai ga lamban gidansu nan a jikin motan wata ta fada a dan tsorace tana ja baya. Kai ya fada kafin yayi kundun bala ya dagoni daga jikin sitiyarin motan na sauke wani ajiyan zuciya lokaci guda kafin na kara lumshe idanuwana. Meke damun ki hakane ya fada cikin son yasan ko meye matsalana a lokacin kaina nace cikin wani irin kasalalen murya mai wahala. Bai fahinci me nake fadi ba sai ya kawo kunnen shi kusa ya kara maimaita tambayanshi gareni nace dago hannu da kyar na nuna kaina. Kanki ke ciwo ya fada yana mai zuba idon shi a kaina na dan bude idona da sukai ja kamar garwashi lokacin na dan gyada kai da sauri ya fara lalaban aljihun wandonshi. Kokarin shaka min yayi ba tare da shakkun komai ba ya turmuza min a hancina baikai second ba na sauke wani uban atishawa lokaci guda.🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,, 🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,, 🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA 7️⃣ AL MUHAYMIN,,,,,,,,,,