← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 212 OF 286

Sashe 212

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kokatinta dai taga ta danne namiji tana juyashi yadda take so mutane na min kallon sha,sha wanda baida right ga mace. Akwai wani hakkinkine da ban sauke maki ba a gidan nan ne na matsayinki mace a gareni ko wanan bai maki ba dai saina koma mace kin koma miji yadda kike so ? Alh kada ka fassara min zancena da wani manufa don muna zaune kallo muna kula da junan mu na cikin farin cikin da makiyana basu son ganimu hakan tun farko shine kuma laifi. Su waye makiyan naki ki fada min yana mai tsureta da idanunshi yace dasu makiyan kine aida da kika shiga matsala kin nemesu ba ban tabo tsanmani zaki canza halinki yabi. Saidai ki sani daga yanzu zuwa ranan da Allah zai dauki rayuwata matukar muna tare da ke na daina yarda dake insha Allahu a rayuwana tunda ba imani ke gareki ba ke. Wani irin kallo take mashi hankali a tashe kafin tace ba mamaki zaka iya fadan komai a kaina yanzu tunda an riga da an shiga tsakanina dakai ana son ala tilas sai anga an raba tsakanin mu a yanzu. Wanan kuma jahilcinkineki kina ganin kowa kamar irinkine da har zai iya shiga tsakanin mu dake don rashin imani nidai nasan ba wanda ya shiga tsakanin mu Allah ubangijine da kanshi yayi nasa ikon ya kwatoni daga makircin da aka dade anayiwa rayuwata. Au zargina kakeyi da yima wani sheri ke nan ashe yanzu zaka dauki alhakina kuwa a kanka idan ka dauka hakane ashe. Yabi kiyi abindaya kawoki dakin nan ki bani wuri banson damuwa da yawa yanzu don kuskuren da kikasani na tafka a baya shi nake kokarin in gyara yanzu. Shiru tayi tana mashi wani irin kallon mamaki ganin yadda ya rikede kamar baahi ba lokaci guda idanuwanshi sun kada sunyi ja sosai dasu. Mikewa tayi tana fadin Allah ya sauwaka shi kadai ta iya fadi tasa kai ta fice daga dakin shi kuma ya bita da kallo cikin takaicin ta har ta bacewa ganin shi a dakin. Ya sauke ajiyan zuciya yana jan tsuki tare da jawo wayanshi dake gefe ya fara neman layin aminjn nasa yana son ya tambayeshi game da dansa Ahmed ko ya dawo a yanzu daga tafiyan nasa. Abbane a kwance da tun safe bai iya fitowa waje ba ga abin karyawa masu aikinshi sun aje mashi bai fito ba har shadayan rana ya buga yana kwance yana faman tunanen duniya. Ba komai yake tunane ba sai yadda wai ace matarka ta suna take kokarin son halaka da karfi da yaji taga ta mayar dakai baya ta gina kanta ita. Bai debe tsamani a yanzu idan akace hjy karimace ta turo barayin da suka shigo masu gida suka kwace kudin da aka kawo mai daga can garinsu gusau kudin kuma na wasu filayenshine daya sayar da sunan zai fada harkan siyasa a lokacin . Ba wanda yasan da zancen kudin amma kwatsam matasan bariyi suka dira masu a gida da sunan sukawo kudin nan da aka kawo mai su in cash a gida. Hjy karima dake bayan shi tana nuna tsoro sai fadin take Alh ka dauko masu kawai ka basu su tafi su barmu shiyafi kagansu da bindigogi a hannayensu. Yace wani kudi kudin da ba a shigo dashi gidan nan ba suna hannun wanda zai kawo min shi yana kokarin nuna cewa babu su a gidan ita kuma tana nuna cewa ai akwai kudin don sai fadi takeyi Alh ka dauko masu kawai su tafi su barmu. Jin hakan shine dalilin buga mashi gindin bindiga da sukayi ba shiri Abba ya nuna kudin suka kwashe suka tafi. Sai gashi kuma a yanzu ansace masa takardan babban filinshi haka kawai ranan yaje zagayen filin shine ya samu ana gina a ciki wai ansayarwa wani iyamuri da filin yana gina gidan mai a wajen. Hankalin Abba din ya tashi sosai ya tambaya sukace a hannun wani suka saya shima yace wata mace baka ta sayar masa ga takardunsu kuma ya duba tabbas takardun filinne hakan ya jawo masu matsala a tsakaninsu suka dinga rikici har ya kira mata yan sanda . Shine tace ba zata zauna ba tunda ya fara zarginta yace sai ta fito mashi da takardun nasa nan rikici ya tashi ta kwashe dama tana da gida ta koma ciki. Sai daga baya yake jin irin halinta hankalinshi ya tashi har ya kaishi da kwanciya asibiti yanzu kuma sai abubuwa suke son su tsaya mashi duk lokaci guda yayi hasara mai karfi haka mai yawa. Gashi iyalansa yanzu yasan suna cikin bukatu don sunyi waya da mama tana lissafo masa lissafi irin yadda ta sabayi mai abaya shine ya bata amsa cewa baida halin hakan a yanzu sai fitina ya tashi a tsakanin su. A gajiye na dawo daga school jakata kawai na aje nayi sallah saina shiga cikin gida mu gaisa dasu kafin na dora girki ya dauke min hankalina don da safe ban shiga ba. Koda na shiga Inna na zaune bakin kofanta Dije kuma tana dan sharo dakinta da kanta a hankali nayi sallama dije din ta dago kai tana fadin Amarya kin dawo ashe ? Nace eh dije yanzu na dawo da safe na fita ban samu shigowa ba shine yanzu nazo in gaida ku tace nasan kin makarane ai tunda naga hakan. Ina kokarin karban tsintsiyan a hannunta tana fadin haba barshi jeki huta abinki ai ina iyawa yau mai mun sharan ta fita zuwa gidan kawartane tunda ra dawo daga boko. Nagane Aisha take nufi nadai karbi tsintsiyan ban duka yin sharan ba sai na nufi wurin inna ina gaida ita da ina wuni inna da kyar ta dago kai tana amsawa kamar ba zata tanka min ba sai naji tace. A yi abinki yarinya tunda kin samu an kama maki in bashi ba inhar muna da muhinmanci a wurin ki aiba zaki fita gidan nan baki gaishemu ba. Yanzu baga umma na wani tarewa ba shima dabaki sauki uwarshi da kakanshi da muhinmanci ba aigashi cewa yayi bai bude kaya sai kin dawo daga bokon ki kinzo ya bude a gabanki. Da uwarki ne aiba zaki fita haka zikau zuwa wai bokon daba riba kawai baki nuna kulawa a garemu ba bokon banza bokon badala in bashiba macen aure da boko don lalacewan zamani aiko ga bokon nan muna girba a gidan nan yanzu. Ke Rashida idan danki yai maki laifi kada ki sauke ga diyan mutane don bataji bata gani ba ita daya sauka a dankinta bata saka rai ga abinda yazo dashi ba saikece uwarshi zaki saka rai kinace tun dare kan magana daya. Wai in tambayeki Rashida ke haka iyayyen mazanki sukai makine da kikai aure nan uban yaronga a lokacin dan isa ubangidanshine kawai amma nan ya dinga nuna ina aka saka dake don kawai mijnki yana aiki a karkashin shi a lokacin kuma baida kowa. Nan dai ta fara gaya mata maganganu masu zafi ina jin hakan na shige dakin Dije nayi saurin sharowa na fice daga part din na barsu suna magana ina shiga na samu Ahmed ya shigo yana tsaye ya dafa baranda yana sauraresu. Yana ganina yake fadin meya farune naji dije na fada da inna haka nace ban sani ba ya kara kallona yace baki sani ba ba daga can kike ba sai kawai na shige daki abina na kyaleshi. Yaji zafin hakan da nayi sai naji ya kuta yasa kai zuwa sashen nasu nan naji muryanshi yana tambaya wai me ya farune haka don Allah haba inna ko yaushe a dinga jin muryanki da Dije kamar wanda yake zaune da kishiyarshi hakan baiyi ba wallahi gaskiya ki sake ina haka ai abin kunya kike jawo muna a gidan nan yanzu. Kazo kai min fadane ubana ko ni bansan abinda ya dace ba ko da ace uwarta nake zata fita gidan nan bata gaida mu ba can dije ta amsa tace ba gashi yanzu tazo tace wallahi makara tayi da safen ba ta fita. Wai inna dama akan zahra ake duk wanan abin haka akantane mana tunda kun daure mata gindi tayi iya shegen da takesowa mutane don kawai banda komai ko dadin abindai a tsatsona kafito ko mahaukaciya nake kuwa . Inna zan saki zahra kowa ya huta ba shike nan ba ya fada a fusace yana juyawa nan djje ta shiga kwala mai kira yaki dawowa ya fice daga wurinsu din bata barshi ba ta biyoshi a baya tana fadin karka soma wallahi dama hakan takeso don ta aurama suwaiba.
Chapter 212 · 0% Book details