← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 261 OF 286

Sashe 261

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

hakan ba sai a yan shekarun nan maganan ya dawo sabo kake yinshi a yanzu da yaron ya girma ya kawo kansa gareka don haka nan duk ba zamuce bamu da wanan labarin ba gaskiya. Magajiya gaki kin sani na sani shiru nayi nasan duk abin da ake kullawa tun ina yaro a gidan nan ina dai kawar da kainane don kina zaman uwa a gareni ko banza akwai alaka ta zumuci tsakanin mahaifinki damu don haka ko baki auri baffa ba kedin jininane. A lokacin tsohuwar tayi magana tun zaman ta a zauren da suka taru din a ciki tace kana son kaga laifina a yanzu nasan dama a yadda ka dauke mu don kawai kana ganin arziki a hannunka har kake kokarin kula muna sheri ka wullakantani da iyalina. Son kawai Allah ya zabeka a cikin mu kaje can ita data kawo wanan maganan kuyishi da ita haka zaifi amma ba yanzu kazo nan kana fadin wasu zance a kaina ba. Murmushi yayi ya dago kai ya kalli magajiyan yace magajiya harda in na kira Bande a nan zaki iya musa wasa hakan da kikeyi yanzu ? Wani Bande banden da yake lahira ko wani banden ka samu a yanzu da zaka kawo muna yanzu yace bande wanda kika sani har kika nemi halakashi a baya kaina da uwata don yaki biya maki bukatan ki. Shi Bande din sherin da zai mun ke nan kuma don anga kasa ya rufe masa idanu baya duniyan yanzu indai akan kana bakin ciki har yanzu da dukiyan naku daya gudu dashine ka fito fili ka fadawa mutane hakan kawai zaifi. In kuma don ka kulla min sheri a gaban diyan cikinane suna kallona yanzu za ka iya don kaga kana da kudi da iko zaka iya mulkan mu ke nan a yanzu. Zancen matar ka kuma koni yabi yanzun bata barni ba don a makiyiyarta ta daukeni yanzu ba gimana ko kimata take gani ba don haka bansan komai akanta ba. Inna inkin fadi hakan akan yabi kinwa Allah karya tun farko waya kawo shawaran hakan ya cusawa yabi wanan akidar ta dukiyan dan gaske duk kece tun muna yara kika saka muna hakan a zukatan mu ai. Kin koya muna yadda zamu dinga cin karen mu ba babbaka a cikin jikinahi kuma a mallakeshi ta hanyar da ba zai iya motsin komai daga shi har kowa nasa kuwa yanzu don haka ta kasance a gareta zaki zame jikinki a kanta ? Duk wanan abin inna ke kika jawoshi don da baki nunawa Yabi wanan hanyar ba da tana zaune lafiya da mijinta a cikin diyanta yar hjy yabi da sukazo tarene ke wanan maganan a hasale. Alh an gama ina iya tafiya yanzu Abba ya fada ina zaka tafi ba akai ga matsayan zance ba don wasu sabbin magana biyu sun shigo a ciki yanzu na farko kace ba alakan aure a tsakanin ka da matarka yanzu. Sai na biyu daka kawo muna zancen Bande da muka dade da mantawa a nan yanzu maganan ka ya nuna kamar kasan inda yake ayanzu bai mutu ba. Kome maganan haka ke nufi don har hardo ya kwanta dama akan binciken wanan lamari ya tafi ya barmu dashi yanzu gashi kazo muna da wani zance kuma akanshi. Ku tambayeta yana nuna magajiya da tsohuwan take zaune tayi tsuru tsuru da idanun cin mutumci a garesu lokacin don duk diya suke a gareta wurin itace uwargidan hardo mahaifinsu Abba din. Magajiya zan yakeki da Allah da manzonsa me kika sani akan wanan zancen tsohuwar ta dago kai tana tafi da salalami tare da fadin yau Allah ka gwadamin ranan da yayan hardo zasu tsureni a cikin gidan nan. Bai kai can ba ya dauki waya ya danna kira Alh jauro ya dauka yace Alh kazo min nan da hardo Bande yanzu lokaci daya kowa ya kalloshi jin abinda ya fada din a lokacin. Ba a dauki lokaci ba suka iso da sallama tsohon a duduke yake a yanzu amma da karfinsu kuma yana gane kowa dake wurin ta fuskokin su don kamanin su ba a boye yake basu yan gidan nasu. Amma ka cika munafukin Allah ta,ala dama kana raye baka mutu ba ashe yayin da sauran mazan suka mike suna ambantan sunansa da Bande kaine ko kamane dai ? Ku tambayi magajiya tasan komai akan batana gashi a gaban ka hardo duk da shima hardone a yanzu a can nahiyar da yake zaune a kasan benen republic dake makwabtaga da kasan nan ta yamma damu maso kudu. Wanan dan nawa na cikina da yabi take kokarin aibantashi a yanzu shine silar gano muna Bande a yanzu don shi Banden yai amfani da sani da iliminsa ya ganoshi a can wurin kasuwancinsa donshi yaron bai zauna duk da baida gata a lokacin bai yarda ya zamo raggo ba a cikin maza. Lalai Amo tantiriyan matsafiyace dama kin fada min da sannu cikin hankali komai nawa zai tonu a bainan jama, a kafin na mutu yau gashi kuwa komai din yakai karshe . Tabbas kin nuna min aljanni kuwa gaskiyane kince zaki hada ruhi da ruhi suyi aiki biyu a lokaci daya gashi naga sakon naki ya baiyana gareni duk abinda nake boyewa tsawon shekaru a yau ya baina ya bainan jamma,a. Lawali dauki magajiya kukai ta ciki hakan ma ya isheta iahara ita da yan baya in zaka gina ramim mugunta ginasa ya zan gajere . Dan nata da aka kira da Lawali ya dago a ciki takaici yana fadin inna kin shu,shemu kin batawa ahalinki suna na har abada kan rashin godiyan ki mm a fada maki tun baya Allah bai raba daya ba. A ina dan uwanmu dan gaske ya rago muna munaci muna sha daga cikin jikinshi muda iyalin mu a kulun yana muna komai inna ashe hakan bai isa a gode mm ashi ba sai anbishi da wanan sakaiyan na sheri. Yau ga yabi din da kikasaka gaba nan ta watsar maki da duk wani manufa taki ta fara gina kanta akan huduban ki ke yabi banda batan basira don da daya ya shigo cikin ku yau me zai rageku dashi don Allah. Uhumm,humm ai baka sani ba yanzu zamu zauna mu lissafa ko nawa na kashewa yasir tun daga ranan haihuwanshi har kawo yau sai a cire wa wanan yaron nasa kason don nasan akwai hakkinsa a kaina banson na mutu da wanan nauyin nasa. Duk ya nuna bai kaunar kwandala a cikin dukiyana don nasa ya isheshi a yanzu shi da iyalinsa amma ni hakan bai mun ba don hakkin zai yi yawa a kainane. Ga Bande nan ya dawo min da dukiyan mahaifiyata dake hannunsa na yanke shawaran barmasa su ya dauka halak malak idan bayan ancire duk abinda addini ya tanada ayi a dukiya sai ku mallaka masa don kune shedun hakan iya abinda zan iya masa ke nan a yanzu. Wani irin kururuwa Hjy yabi ta sake tana fadin bata yarda ba wanan zaluncine da cin amananta da yayanta akayi ai Hardo yace a jata zuwa ciki shike da dukiyansa shi kuma ya kyautar da abinsa don haka babu yadda za ayi gaskiya saidai shima din ya dai kwatanta yadda ya kamata. Yace iya adalcin da zanwa wanan yaron ke nan a yanzu gara na fitar dashi cikinsu tun ina raye zaifi don wanan macen da kuke gani yabi ba karamar azzaluman mace bace
Chapter 261 · 0% Book details