Sashe 214
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zahra ki debo min bayan iccen tumfafiyan nan don Allah yake fada cikin wani irin murya mai nuna rauni a gareshi da alaman jin jiki ga bawa yake magana. Banji me yake fada ba saida na matso kusa dashi na fahinci me yake fadi hakan yasa na fita da sauri saidai gaskiya nikan ba zan iya zuwa wurin wanan dan itaciyan ba da kullun nake mafalkin haske a cikin sa don na riga na tsorata da wanan wajen ko gaskiya. Tsaye nayi a kofana ina shawara sai ga dije ta shigo gidan ta fito gidan mlm Tanimu da bata sameshi a gida ba lokacin yasa ta juyo gida hankali a tashe sai mukai kicibis da juna da ita. Ince dai lafiya na ganki a nan haka hankali tashe na gane me take nufi yasa nace a, a ba komai ba cewa yayi dama a debo mashi bayan wanan dan iccen dake wurin ban dakinku din nan. Iccen tunfafiya ke nan ko na gyada mata kai da nufin shi din tace ai abu mai saukine wanan bari naje na kakabo masa shi din ta shige ciki da sauri ni kuma na koma ciki. Bata jima ba sosai sai gata dashi a hannunta tana fadin wanan dai yake nufi ko tana kokarin nuna min abinda ta debo din a lokacin nan nace da ita bari a nuna masa idan wanan yake nufi. Maimakon in karba daga hannunta sai nayi gaba ta biyoni ciki da kyar ya iya tashi ya gani din don har lokacin yana cikin mawuyacin hali yadda muka barshi. Idon shi ya kade yayi jawur dashi lokaci guda kamar ba nasa ba daya kallo inda muke din don yaga me aka debo hannu ya mika ya karba yana kokarin murmusawa tace kawo nan a murza maka idan shine da sauri na fita zuwa kitchen na dauko dan karamin turmin karfe da ban amfani dashi na karba na daka yace a barshi hakana in miko masa turmin na bashi. Ya tura hannu ya debo yana shakawa a hancin sa Dije sai faman yi masa sannu takeyi ya miko min tare da komawa ya kwanta yana fadin Dije akwai garwashin wuta na turara ? Take fadin na daiga sun dora girki yanzu da zan shigo bari na duba idan yayi sai a debo ma kawai master ka tashi ko chemist ne katafi zaifi. Zahra ba ko wani ciwo bane na asibiti wanan ciwon na daban ne don, , , , atishawan daya fara sakewa ya hanasa karkare fadin abinda yayi niyar fada a lokacin. Yayi tayin atishawa babu kakautawa lokaci guda muna masa sannu kan dije ta fita da sauri zuwa debo masa garwashin wutan ta kawo mai ya mike zaune da kyat yana dan dube dube a dakin kallo daya nayi mai a lokacin naji gabana yayi wani irin faduwa. Saboda yadda naga yanayin tashin hankali karara a cikon idanun shi dagani kuma ciwon ba karamin ciwo bane gaskiya. Yunkurin sauka daga kan gadon yayi take fadin ina kuma zaka haka bari na zauna a kasa inyi hayakin ya fada cikin murya mai rauni yana sauka a gadon zuwa kasa mika masa abin rufa tace da sauri. Na dauko wani mai dauda da muka cire na bashi ya rufa nan dai ta taimaka mai yayi hayakin kafin ya bude lokacin yayi wani irin zufa sosai. Ya dan dafa gefen gadon ya dora kanshi muna tsaye duk mun zuba mai idanu can ya sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi sai kuma atishawan da yake danyi a yanzu jefi jefi kafin ya mike yana hawa gadon tare da tambayan yanzu karfe nawa ake ne ? Sha biyu saura minti ashirin dije ta fada mai don dai gaskiya ta nuna damuwa sosai a yadda take ganin shi din muryan innace daga falo take fadin wai har yanzun dai kuna kansa bai lafa bane ? Yafito mana yaje asibiti kada kuma dare yayi ya hana mashi shakat umma ki masa magana ya tashi ko matarsa saita rakashi zuwa asibitin mana. Amma kun zauna kun sakashi gaba kuna mashi aikin tsubbu haka har wani abu yazo ya sameshi ciwo daban magani daban. Haba haba inna don Allah ki sakewa yarinyar nan mara mana bafa ita tayi min hayakin nan ba ninace Dije tayi min don abinda nake ji a jikina bana zuwa asibiti bane. To ubana kada a fadi laifin matarka ko koma ita tayi aicewa zakayi uwatace tunda dukkan ku an gama daku duka yanzu kaika sani ai jikin kane. Naji din jikinane ko amma you better mind your tongue she's your mother and for perhaps is look like she is worry about your health now, so please don't misunderstand her. Na fada ina fita sai ya bini da kallo ya koma ya kwanta yana lulubewa da abin rufa bai kara magana ba kuma tun lokacin. Tun zuwan dan nasa kasan yasa a yanzu baida wani kwanciyan hankali a tare dashi don koda yaushe duk abinda dan yakeyi idonshi na kai yana gani. Badon komai yasa hakan ba don kada yayi wani abin shedana ya aikata irin abubuwan da yake aikatawa a can yazo yaji kunya a idon mutane. Duk da dai yana iya kokarin shi a boye don ganin dan ya daina wanan halin don mutuncinshi da kimar shi a gun mutane kada ya zube a sanadin haka. Asubace ganin hadari a gari yasa shi dawowa gida daga masallaci don yana fita yayi sallah asuba a cikin jam,i saboda yasan iri falala da tanadin da Allah yaiwa mutane a wanan lokacin. Don idan kana son Allah ya azurta ya daukaka yakuma tsare ya shirya maka yayan ka ka tsareyin sallah asuba akan lokaci maza kuma su tsare sallah a cikin jam,i . Insha Allahu zakaga mamaki a cikin zurian ka Allah zai azurta maka iyali a yadda baka zata ba idan sun taso Allah yasa mu dace da rahamominsa amin. Yana kwancen yaji an turo kofa hakan yasa ya gyara kwanciya zakace barci yakeyi a lokacin yadda ya kwanta din juyawa yaji anyi yasa ya bude ido yana kallon ta sai akai sa,a ta juyo ta ganshi . Ta juyo ta nufo wurin gadon tare da fadin ashe ba barci kakeyi ba Alh a wanan lokacjn zanyi barci kuma ya fada yana dan motsa jikin shi lokacin guda har tasbahan dake hannunsa yana ja tana dan sake kara hakan yasa ta gane abinda yakeyi watau zikirin safe a lokacin. Yayi mamakin jin kallaman ina kwanan da ya fito daga bakinta a lokacin kafin ya amsa yaga tana kokarin samun wuri takai zaune daga can wajen kafafunsa. Ya dan bi da kallo don ba yarda da tuban mazurunta yayi ba har lokacin kawai dai yana kokarin danne zuciyanshi ne akanta da yanuwanta . Muryan ta yaji tana fadin Alh dama kasan da halinda yasir ke aikatawane baka taba fada min ba kokuwa yanzune kaima kasani kamar yadda nima na sanin a yanzu. Kallota yayi yana kada santala santalan kafafuwan shi dake a harde lokacin kafin ya danyi wani irin ya kallota don jin abinda take fada game da dan nasu. Wani hali yakeyi sabo kuma yanzu wanda baki sani ba ko kuma son da kike masane ya hana kisan haka din tun tuni. Nan ta fara rantse rantse da cewa ita bata san wanan halin shaye shayen da yakeyi ba don ba wanda ya taba fada mata haka ke din yabi wace irin uwace wai ? Har zakice baki san da yasir na wanan halin ba tunkan yaje karatu waje ke wata irin uwa kika kasance wai ga yaranki inko har hakane baki da saka idanu akan dabi,un yaranki kin zamo sha sha shan uwa a yanzu gaskiya. Agaskiya ban taba sanin wanan zance ba Alh ka yarda dani dacewa bansani ba dinne sai yanzu ko yanzun ma Allah ya nufa in sani na shiga part dinshi nagananwa idona hakan. Da meye nufinki yabi kina nufin kalan tarbiyan da kike ba yaranki ba abinda zaki girbaba ke nan a wurin su kiri kiri koni mahaifinsu sai ki saba min idan na taba maki diya. Naji duk laifin yanzu a kaina zai kare tunda nice ban kwabasu ba akace amma yanzu meye mafita don gaskiya hankalina ya tashi sosai yadda na samu yasir din a cikin wani hali don bai ma sanda na shigo part dinshiba lokacin. Kin tambayeshi tsowon yaushe ina masa fada kan wanan halin don hakane nace ba zan barshi yaje karatu waje ba kika nace harda hada min banga kan sai ya tafi waje karatu ni kuma abinda nayiwa gudu ke nan a lokacin nasan kara lalacewa zaiyi a can din. Duka hannu biyu ta dora akai lokaci guda kamar karamar yarinya ta soma rera kuka cikin takaici tana fadin na shiga uku Alh shine baka sanar dani wanan halin nasa ba tun lokacin ? Kallon mamaki yayi mata don bai taba zaton jin hakan daga bakinta ba yace a yanzu da kika gane ina matsayin mahaifi a garesu zan yi hakan ko lokacin da ke kanki baki daukeni da daraja ba balle diyan ki su daukeni wata tsiyan zanyi hakana. Aina ba yasir kadai ba har ita saliman idan baki sani ba yau ki sani tana bisa kan tarbiyan da suka bakind don dai Allah ya gyarane ita na samu tun wuri na shawo kan lamarin amma ba zance ta daina halin duka ba sai nan gaba idan na tabbatar da hakan gareta. Baki bude ido waje take fadin Alh salima kuma ita kuma saliman wani matsala ta koyo kuma badai shaye shayen takeyi ba itama ta fada tana kallon shi cikin sonjin amsa daga bakinshi. Ya dan gyara kwanciyarsa yana fadin zaki iya zuwa ki tambayeta ta fada maki da bakinta tunda tana gidan yanzu ko kuma ki kyale ki saka ido kiga wasu halaiyane takeyi na nuna rashin tarbiya a gareta. Da badon Allah ya taimaka saman gado take ba a lokacin da ba abinda zai hana ta fadi kasa a sume a lokacin don gigicewan da tayi lokaci guda. Kuka takeyi sosai yana jin kukan nata na kara bata mashi rai don duk laifinta ne yasan alhakine Allah ya fara jifanta dashi tun nan duniyan hakan ke bibiyan diyan da suka haifa tare dashi din. A hankali