Sashe 125
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
tambaya akan mahaifinka yanzu mutumin da yai tafiyan shi ba kara waigo inda kake ba . Ko bai taho nan don kowa ba ai zai taho don kai amma tsawon shekarun nan ya kwashe ba tare da yasan ya bar wani halittaba a nan Koma meye shidin dai mahaifinane ko Dije banda wanda zanyi tunkaho dashi a duniyan nan bayan shi banda wanda zai tsaya min ya zama min gatana a al,umma bayadashi. To wai miya kawo wanan maganan yanzu kuma ina kule da cewa tunda ka fara girma ka dauki ranka ka dora akan shi ka daina tuna wanan mutumin. Dole in tunashi Dije tunda an fara shegantani cikin garin nan ana kirana da mara asali mara gata a idon mutane duk da nasan ina da gata gatan da ba kowane keda shiba garin nan. A kul akul naji ka kara fadin wanan haukan waya isa ya sheganta min kai duk garin nan in maka na mahaukaci bayan kowa yasan da auren sunna ma,aikin Allah aka haifeka. In hakan yasa ka fara haukan hasashen maihaifin ka nada gata ko wani abu gara ka daina tun wuri don wanan kan ba gaskiya bane haka yazo garin nan fakirin shi. Wanda na tabbatar da sanadin haihuwankane ma ya kawoshi garin nan ya biyo yan zuwa kudu yazo nan ya zauna tare dasu a karkashin Alh Akilu mai shanu. Har Allah ya taimaka don darajan Alh da uwarka ta nace saishi aka dauketa aka bayar da ita amma kamar mai bakin uwa ana zaune kalau haka kawai da rana tsaka ya bijiro da barin garin nan kamar mai aljannu a kanshi ko kurciya ba yadda malam baiyi ba amma ya kyankyashe yace shi tafiya zaiyi. Allah ya kyauta ya fada ya mike ya fice daga gidab lokaci guda kai tsaye waje ya nufa duk wanda ya ganshi sai ya tsaya yana kallonshi don labarin shi daya karade garin na batashi da kowa ya sani. Ya dai sha tambaya da kallo kafin ya isa kasuwa ya sayowa dabbobin su haki ya hauwo mashin ya dawo gida zakace yadda yai wani haske ya murje yayi kyau kamar inda ya fito a cikin AC yake kwana yake wuni yadda yai kyau din. Haka yasa mutane ke kara mashi kallon mamaki inda duk yabi bayan ya kawo masu abincin ya sake fita zuwa wurin oganshi na kasuwa suka dan tatauna dashi din a can. Wallahi na gaji Yabi wanan tafiyan ma da kyar nakeyin shi a yanzu duk katarana ya zoje wurin hawan tsaunin nan dafata tayi ba tare data iya bata amsa ba ga magananta ta dan taka wani dutse ta haya tana mayar da numfashi da sauri sauri ta fara fadi. Adda Wuro da badon bukatana bane ba yadda za ayi ace na hawo wanan wurin amma ba yadda na iya tunda ina son bukatana ya biya . A rayuwana na tsani in bude ido inga anyiwa diyana yan uba a duniyan nan dubama ga yanzu yadda dukiyan Alh ke kara bunkasa sosai yanzu. Ba zan zauna ina gani ba wata ko wani yazo daga sama yace zai cudanya damu da sunan inuwa daya a karkashin Alh ko ita wanan jakar na bartane ta zauna kamar yadda mai allon karfe ya umurceni dayi a kanta. Na riga naba kare mahaifanta ya cinye don haka yanzu banda fargaban komai a gareta tunda mahaifanta karnuka sun lashe shi tuni bata da sauran amfani a yanzu. Kai Yabi baki da kyau kiga yadda matan nan tayi kamar zata mutu lokacin nan kuwa amma kika nuna kina tausaya mata kene har da fita kasan waje da ita. Saida hakan ne Addah wuro mazan yanzu in kayi sake kaine a baya balle irin nawa mijin da idon shi akan mace har indai yaga mace yana so yanzu zakiji zancen aurene. Amma yanzu kinji shiru ba wanan zancen tundana hada shi da makulli na kulle na kada wanan tsohon rijiyan baki kara jin wani zancen aure ba kuma gareshi. Haka suka sukai ta hira tsakanin su har suka isa bakin bukkokin dake tsakiyan amtsaunin da alaman mutanen wajen su dan wayesu nan aka gaisa akai ya kwana biyu. Basu sha wuya ba wurin ganin bokan don yasan zuwansu wurin shi alherine garesu shida iyalan shi gasu dai fulanine amma kuma arnane su basu ko wani irin addini a rayuwan su sai tsafi. Zaka kuma samesu da dan walki a jikin su mazansu da matansu ga tarin dukiya da Allah ya basu a tsakiyan dajin sun gabatar mai da abinda ya kawosu duk da yaga abune mai wuya a iya dakatan da hakan . Amma sai ya nuna masu zaiyi aiki mai wuya ya hana hakan faruwa ya dai dan kwantan masu da hankali tare dayin surukulen jayewa Alh hankali ga barin wanan maganan . Sukai mai sallama mai tsoka suka dawo a gajiye ace tsafi gaskiyan mai shi saiga Alh na fadi washe gari ta shirya su koma Abuja ya gaji da garin nan shi. Haka suka tattara suka koma ba wanan zancen nan ya bar Jabbi da dan baro da mamakin yadda akayi lokaci guda Alh yabar zancen yaron daya tasasu a gaba a cikin yan kwanaki biyun nan. Duk da haka basu share zancen ba a bangaren su don sunci gaba da bincike a tasu bangaren saboda sanin halin hjy Yabi da sukayi don irin hakan yasha faruwa a tsakanin suma ganin haka suka kulla da ita. Har suke kwato abokin nasu daga halakanta idan tayi wani abin sai subi su warwale ba tare da sanin aminin nasu ba. Wanan yasa ta tsanesu da duk wani abu daya shafesu duk inda ta buga kuma sunki rabuwa suna manne dashi ko yaushe don har abuja sukan bishi wani lokaci duk da sun san tsanar da take masu din. Don hakane ma wanan karon basu tsaya bin ta kanshi ba koda ya tafin suka samu isah tella yai masu bayanin unguwar da yaran suke suka bashi sallaman da sukai mai alkawari suka tafi. Ni dai an wayi gari naga sauyin fuska tsakani na da mama sai hakan yasani shan jinin jikina amma ban yarda na fadawa ummah komai ba. Haka abinda ya faru dani da mommy ban mata hiran komai da naji ba kona gani saina barwa cikina zancen har muka koma school mukaci gaba da karatun mu kamar yadda muka saba. Saidai karatun yanzu baija sosai don rashin Ahmed da bai samun shigowa yana muna bita ko yaushe a yanzu busy yake wurin neman kudin shi. Mun dai hadu dashi sau biyu ya dan taba muna karatu daga nan bamu sake ganin shi ba kuma da mukai waya dashine yake fada min cewa ba zama garin ne yana yawan shiga kauyoka har wasu jahohin suna sayo hatsi.