Sashe 218
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
koshi don zurian yaron daya bari akai mai kwatance da Amadi din ya ganeshi har yake tambaya ina dan yake yanzu ya daina ganinshi . Amma wani lokaci mai tsawo tsohuwa tazo ta fada mai zancen aurenshi balafiya bai samu zuwa ba yadda yaso anyi auren kuma yana garin nan saidai bai zama garin yanzu don yana karatune a zaria. Falon ya fito babu kowa dan haka ya nufi wurin aje abinci nan ma babu komai da aka aje a lokacin cikin mamaki yake kallan kofan part din matan nashi. Kafin ya maida kallo a kofan kitchen inda yaji motsin fitowa hjy murjace tafito daga kitchen din take gaidashi don ganinshi datayi girshi a lokacin gabanta. Da sauri ta nufo dinning table din tana bashi hakkuri da bata san ba a girka abinci ba don barci ya dauketa data tashine Indimi ke fada mata ai ba a girka komai ba gidan shine ta fito yanzu ta girka masu yayi hakkuri. Kai ya gyada alaman gamsuwa da zancenta don yasan hjy taki girkine saboda tana zaton tare sukai tafiyan a lokacin, abinda bata sani ba kuwa shine. Suna cikin Abuja ya ajesu wani gida nasa dako hjy bata sanda shiba ya sayeshine don ita hjy murja din ta zauna a ciki sai kuma yayi shawaran hadasu wuri daya don tasan irin illan da tayi mai a baya. Wanan zaton nata da yake mata shine kuwa shine yasa tabada umurni ga Ladi mai aiki akan kada ta girka masu komai na karyawa a gidan don tasan diyanta ba matsala bane dan ba damuwa da abincin sukayi basu. Zama yayi ya karya gurguje zai fitane a lokacin ta fito don taga ya zasu kwashe da yunwa a gidan sai ta samu yan matan hjy murja din suna kwashe kulan abincin dayaci ya raga zuwa part dinsu . Hakan yasa ta gane sun gitka abinda zasuci ke nan ashe tarkon data dana baiyi amfani ba don inda dane tace kada a girka hjy murja bata isa ta dora tunkunya a gidab ba da sunan wani dahuwa. Amma yanzu hakan na kara nuna mata cewa powern ta ya fadi sosai a gidan tunda har hjy murja zata iya yin abu bada izinin ta ba. Hanya fita daga falon ya nufa kamar bai ganta ba a lokacin mamaki bai kare mata ba don haka a fili tace dashi Alh wai fita zakayine dama bai juyo ya daga mata hannu kawai alaman ta dakata kawai daga fadin abinda take son fada a lokacin. Yasa kai ya fice daga gidan tabi bayan shi da sauri kafin ta isa inda yake har yashiga mota aka ja suka fice gaba daya daga gidan. Mun gama cin abincin dare muna zaune kowa hankalinshi na a naji muryan shi yana fadin Zahra in Allah ya kaimu gobe zanyi tafiya zan dan kwana biyu a can kuma. Kaina dago ina kallon shi ina fadin inane zaka yace kinsan garin da ake cewa Illo to can zani wurin wani zai ketara dani zuwa kasan Benin republic akwai abinda zamuje yi a can. Ashe tafiyan mai nisace da har sai kun fita kasan nan yace eh zan tafi na duba yanayin kasan ace ana samun abinci da sauki a wuraren don ina son na dan kara habaka sana,ata ta saida hatsi da nakeyi. Ubangiji Allah ya bada sa,a da rabo na alheri yasa a dace da nasara ubangiji yace amin nagode da adduan ki gareni zanje in fadawasu Dije don asubanci zamuyi mu bar garin nan goben. Da goben kuma nake son na roke zuwa gida nagaida dasu don na kwana biyu banje na gaudasu ba ki tafi idan Allah ya dawo dani lafiya kuma sai mu koma tare. Ya mike ya tafi ya dan dade a can din kafin ya dawo hakan yasa na gyara wurin da mukaci abinci din har na mike na shiga kitchen na hada kayan miya na fito don ina sonyin asubacin girka mashi abinci kafin ya tafi duk da yace asubanci zasuyi ga tafiyan don haka ba lalai bane ya samu wani yaci abincin ke nan. Karfe hudu na tashi na fara soyan dankali baiji motsina ba har na fita na gama don ba yawa na kwashe sai gashi ya tashi sallah bai ganni ba dakin ya fito nema shine ya samu ina kitchen a lokacin . Ban yarda ya bar garin ba saida ya karya don koda ya tafi bai karya ba ki gane cewa ke mai karatun labarina hakan ba halina bane waina gjrka abinci don yaci kafin yayi tafiya. Amma haka kawai naji yana da bukatan yaci abinci tunda tafiya zaiyi mai nisa suka tafi yana min godiya na dawo part dina na kara rufewa dije kuma tashige nasu part din. Na gama na shiga na gaidasu su Aisha na juyewa sauran abincin daya raga din na jawo kofata na rufe nafice zuwa school. Munyi lactures mun fitone nake fadawa hannatu zancen tafiya amma kinsan me hannatu ni sai naji zuciyana bai bani ba ga tafiyan nan na master don bai taba tafiya naji hakaba a raina. To kiyi sadaka koma meye kike tunanen zai faru Allah ya mayar dashi alheri gareshi nace amin idan mun fita ki tuna min nabada sadaka ga almajirai. Da maka tashi batama tuna ba ni naga almajiri da dan jagoranshi na saka hannu a jakata na dauko dari biyar na mika mashi. Ya fara fadin bayan dan jagoran ya fada mai abinda na basu yake fadin sarkin da ar sarki ya karba ya biya maki bukatun ki na alheri. Sarkin da akaiwa ya sani ya shige maki gaba ga bukatun ki mayafiyan mu Allah ya tsare ya kare ya dawo muna dasu lafiya. Kallon juna mukayi lokaci guda da hannatu kafin mu amsa da amin baba mun gode muka tafi shima ya doshi wani wajen mashin muka tare muka hau nida ita kowa ya nufi gidansu. Banje gidan namu ba don nasan ummah zatayi min fada idan nace da ita baya gari yayi tafiya yasa na fasa zuwa saboda na tuna da fadan da tayi min ranan