Sashe 147
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sannu a hankali wani irin shakuwa da sabo yake shiga tsakanin mu wanda hakan ya kara kwantar min da hankali a gidan matsalata dayane zuwa biyu shine irin matsalan dake tsakanina da uwar Ahmed da kannen sa har ma dai ita karamar tafi shiga min ido sosai. Don dayan ba zance ga wani matsalan daya taba hadani da ita ba saidai kawai ba sakin fuskane itama daga wajen ta kamar yadda uwar da yar uwan keyi min. Sai tsohuwar gidan ce mai sake min fuska don ina zaune zanganta a parrt dina ta shigo mu danyi hira ta kuma ta ban hakkuri na daure da yanayin dana tsunci kaina a ciki wata rana sai labari. Nakanyi mata godiya idan ina da abu na dan bata ko nayi dafuwa in saka mata da dan yawa duk da nasan bata iya cinyewa ita daya . Don su din na kula da sunyi fushi kan zancen abincin da master yace a daina sakawa dasu din gashi koni din bako yaushe yake bari inyi girki ba a part din mu din. Saidai idan zai dawo ya sayo dan wani abu mu danci harda ma yan cikin gida wanan sallon kuma yasa mahaifiyar shi saka ido ga hakan da yakeyi din . Tana fada ranan a gabana cewa wanan ai salon kashe mata dane aka dauko wai ace mace ba zata girka abinci suci ba sai an fita an sayo abin kwalan a kasuwa taci. Da Dije taji fadan yayi yawane ta fito tana fadin kai kai Rashida baki biyo halina ba wallahi baki da godiyan ubangijo ko kadan dake watace sai ki godewa Allah daya hada danki da yarinyar nan a yanzu. Koda yake ba abin mamaki bane don kinyi hakan a yanzu don baki san irin wahalan da muka fito a cikiba a baya har zuwa ranan da Allah ya hada dan naki da yarinyar nan abubuwa suka fara bude mashi. Fadin hakan da tsohuwar tayi sai naji maman ta saka kuka tana fadin Dije ko baki min gori ba nasan na tafi na barku a cikin wahala shekara da shekaru nima kuma hakan ai ba laifina bane tunda aure nabi. A, toh ni dai na fada in kina cire ido ga yaran nan ki cire don arzikin su yazo data idan kinyiwa dan ki sawal, walin tsiya kuma ya rabu da yarinyar nan wanan kuma kinwa kanki don dai ki sani. Shine kwana biyu naji shiru ta daina shiga harkan mu tama dauko fita in tabar gidan tun safe sai yamma zata dawo. Da yan kushin abubuwan irin su rake yalo karas lemu mangoro ayyah da sauran su a nan zasu baje saman tabarma da yaranta suci sai wata rana wata rana akan debo min akawo min dan kadan. Saidai Allah bai sako min kwadayin irin kayan nan ba wata rana in karba in aje idan ya shigo shi zaici wata ran kuma ba zan karba nace a mayar nagode. Sai su cinye abinsu ko wanda ake kawo min din ma ita yar babban yar nata Aishan ce kecewa a diba min sai karamar ta yatsune baki tace abinda baida yawa zatace wai sai an dibamin shi. Haka dai zasuyi ta fada a tsakanin su har ta kawo min ruwa kuma koda sanina koba da sanina ba haka zasu shigo su bude fridge su dauka susha saidai wanan bai dameni ba kamar yadda sukanyiwa fridge kamar da gaiya zakaji an rufe shi da karmi har sai mutum yaji shi har cikin ranshi . Irin hakan wata rana ya faru yana gidan Asmau tazo ta dauki ruwa ta buga marfin saida duk muka zabura lokaci guda. Ya mike yana fadin meye hakan da kyar na iya dago kai na bashi amsa da frige ne aka buga wata kila wanine ya dauki ruwa a ciki. Ya juya ya fita a hasale ya samu yarinyar Asmaun daice ma lokacin yayi mata tas saiga uwar ta fito tana fadin don ruwan da nace ta dauko min din shine zaka zo kana kokarin fadawa mutane maganan banza. Ke karbi ashirin ki karbo ruwan ki mayar masu don Allah kuma daga yau kada wanda naga ya koma shiga sashesu da sunan dauko wani abu. Innan mu bafa fadan an dauki ruwa yakeyi ba yadda asmau ke buga masu marfin fridge dine yayan mu ke magana a kan shi. Wani tsawa ta dakawa yar nata da saida ta kadu lokaci guda ta koma ta rakube a bayan Dije tana ci gaba da sauraron uwartasu dake sake magana. Inna nifa ba ruwa nace meyasa ta dauko ba yadda take rufewa yarinyar nan fridge ne bai mun ba don Allah ai mata magana ta bari. Yana fadin hakan ya juya ya tafi ya dawo dakin yana cicika kafin muji muryan Asmau tana sallama tare da fadin ga ruwanan ance in kawo. Ya mike ya fito da sauri yabi bayanta yana kiran tazo ta dauke ruwan ko ya saba mata abin taron kurciya dukansu sai ya kwasa ya bita da gudu ita kuma ta koma bayan uwar dake hasale ta boye tana leken shi a inda yake tsaye yana wa uwar kallon mamaki. Dake fada tana fadin don ruwa kawai zaka taso min ya a gaba zaka doketa ina dai don ruwan kake wanan hasalan gashi kuma na sayo na mayar maka da abinka. Mama don me nake sayen ruwan ba don asha bane nake sayowa ni magana nake mata cewa ta dinga kula mata da kaya kada a bata matashi. To ai shina nace mun daina tabawa ruwan kuma dana dauka nasha gashi nan mun biya koba shike nan ba ta fada tana mai wani irin kallo na tsana. Kai Amadi maza koma ka zauna in fita zakayi kuma tai zuwa inda zaka ke kuma in dai radhin kunya abin yine ki biyewa uwarki gara ita takamanta a yanzu na haihuwan shi da tayine keko fa ? Ina shi din daine gatan ku garin nan don in kun iya ko abinci sai ku daina cin wanda yake sayowa kunaci din karewan dai ke nan ke yar banza ko mutum daya kun gani gidan nan da sunan dangin uban ku halan ? Zaki biyewa uwarku da bata san ciwon kanta ba kunawa yaro iya shige iri iri idan yai magana uwarku ta tare maku tundai ke Asmaun nan ba ma,un arziki kike ba wallahi don duk wani iskanci da iya shige kece ummul,abasin shi a gidan nan yanzu. Ko shekaran jiya in kula dake da kika gama wanki yarinyar nan tana shigowa kika dauki ruwan wankin nan kika watsa mata da kadan a jikinta in ba Allah ya gyara ba. Ido waje yace kin gani ba kingani ba Dije ni idan zasu takurawa yarinyar nan ne gaskiya saidai nabar gidan nan mu koma haya da ita don ba zan dauki hakan ba a rayuwata tunda yan uwanta ni basu raina min ba don me ni nawa zasu dunga wullakanta min ita ? Jeka ai abin baikai na barin gida ba yar banza maganin shegiya mara kunya zanyi gidan nan tun kan aika ga hakan asirin mu ya tonu idan ka bar gidan nan yanzu da dan Amo ya gwajesu yaran banza kawai. Ya juya ya tafi har ya shigo part din kuma yasa kai ya fita zuwa wajen dabbobinsu a nan Aisha din kanwarshi ta bishi tana fadin. Yayan mu kaiyi hakkuri nima ynzu na gane gaskiya abinda akai wa amarya ba a kyautawa ko ranan ni nishigarwa maganan da Dije ka hwadi dazun da niyi magana innan mu ta dawo Asmau ta kwashi karya da gaskiya ta hwada mata. Kije ai ba komai duk abinda mutum yayi don kaine don kuma baku san irin gidan da zaku hwada ba ai ga amre don Allah yayan mu kayi hakkuri damu da innan mu. Ya duka yana gyara wurin dabbobin yana fadin ki tahiyar ki ai komai ya wuce garan nikan bandai yadda a rainawa matana da wayo don na aurota gidanga shin hakan laifina ? To in abin yayi min yawa daukan mata zanyi mubar garin in koma gidan ubana mu zauna don su can basu gudun mu duk wanan abin na kula cewa dani innan ku ke adawa kiyayyana ne ya shafi Zahra yanzu itama. Yarinyar tayi shiru na dan lokaci kafin ta furta don Allah kayi hakkuri ta juya ta tafi dama ya fadi hakan ne don yasan sako ya bata zai isa kunnen mahaifiyar nasu. Yasan kuma ba zasu taba yarda dacewa ya koma gun mahaifin nasa ba a yanzu don irin yadda suka kulla shi a ransu irin yadda suke ganin yayi banza dasu a baya sai yanzu da yaro ya fara tasowa zaice zai koma garai. Tana shiga ta samu suna maganan tsakanin Djje da innar tasu nan ta samu wuri ta zauna tana sauraren su kafin a kawo inda ta tsoma baki tana fadin. Ai yayan yace tahiyatai zaiyi gidan ubanai wane uban ne ubanai uwar ta tambaya a hasale tana kallon yar nata. Lokaci daya suke kara tambayan junan su da cewa wane uba kuma to ai yanzu kin gani kinji hukuncin da dan naki ke kokarin yankewa zuciyarshi yanzu akan halin da kika dauko mashi a yanzu. Sai in bani raye hakan zai faru mutymin da yai tahiya tai bai ko taba tunawa da muwa ba a duniya sai shi da rashin zuciya ya daukeshi ya kaishi inda yake . Yan uwanai sunka taho nan da barazana waisu ga dangi wagganshi ko yasan inda yake yanzu maganar banza da wofi kawai. Ki dai natsu kada wani abu yaja maki bacin rai daga baya wanda ba maganin hakan a gareki yanzun dai kekin ka rage da shawaran da zai fusheki inba haka ba kina kallo danki ya gujeki saboda halinki na banza. Shiru tayi har tsohuwar tagama ta naji tayi shiru tana nazarin zancen tafiya gidan ubanshi da kanwar nasa ta fada masu lokacin. Ina kwance ina karatun handout a hannuna don abin ya dan shige min duhu shi kuma baida lokacin zama ya koya min karatu yanzu sosai. Sallama nake ji a kofa yasa na aje takardan na mike zuwa falon din don ganin wace ke min sallaman Tani ce mai aikin ummah bansan lokacin dana sako fara,a a fuskana ba lokaci guda ina