← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 286

Sashe 10

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

yana cika radunan ruwan su kafin ya dauko na karshe ya shiga bandaki ya watsa ruwan ya fito. Dakin Dije ya leka ya samu tayi barci a lokacjn kofa ya jawo mata ya rufo ya nufi nashi dakin bayan ya saka dan abin da suke kare gidashi koda wani zai shigo masu gida da dare zasu iya jin motsin shi don barawo bai raina abin sata don an taba shiga masu aka sace wa Dije din tukunyar ta babba suna barci tun wanan lokacin suke rufe kofan gidan nasu. Washe gari kiran farko ya samu matashin saman abinda yake sallah mikewa yayi yakara zagayawa bandaki ya dauro wani alwalan daga nan ya kwankwasawa Dije kofa daga ciki ta amsa da gyaran murya yagane cewa ta tashi ke nan a lokacin yasa kai ya fice daga gidan. Babu kowa sai wani dattijo dake nafila shima nafilan ya fara kamar yadda dattijon daya sama aciki yakeyi kafin mutane su fara cika wurin daya bayan daya wurin ya cika. Bayan an idar da sallah ya jima yana addua bai fargaba ashe daga shi sai wanan tsohon a zaune a lokaci kusan daya suka mike kowa ya nufi hanyar fita. Amadi ya riga dattijon fitowa saidai a yadda yanayin tsohon yake tafiya yasa Amadin tausaya mai ta hanyar dauko mashi takalman shi da yawan jama,a yasa suka turashi nisa ya dauko ya daidaita mashi ta yadda zaiji saukin sakawa a kafanshi. Kafadanshi yaji andafa ana mai addu,a ya amsa da amin tare da dagowa yanawa tsohon godiya ta hanyan dan ja da baya kadan har lokacin daya daidaita ya saka takalman nasa. Ganin sun sauka daga dan steps din masallacin ya dan juyo yana fadin nagode baba Allah ya bamu wuni mai albarka sai baiga kowa a wurin ba shi a zaton shi tson yabi ta baya ya wucene a cikin duhu don wurin babu haske sosai don haka yasa kai yawuce zuwa gida. Sannu sannu yake jin kamar sanyi a jikin shi kwanciya a wanan lokacin ba halinshi bane amma sai yadan kishingida kafin gari ya ida wayewa. Mafalkin dayayine ya sashi tashi a firgice Dije ce tsaye a kanshi tana tayar dashi daga barcin ya amsa da na,am tace lafiya kake kuwa yau har wanan lokacin baka fito zuwa daukan karatun kaba ? Mikewa yayi yana mika gami da salati yana fadin wallahi sanyine naji lokaci guda na dan kwanta ashe barci ya daukeni ban sani ba a haka. Tashi ka gagauta ka shirya kafita kasan halin matar nan da kake aiki a karkashinta da fitinan tsiya kada kaje yauma ta hanaka kudin aikin ka ga kudin nan na jiya sai kayi amfani dashi. Ki barshi Dije zanyi sauri na karasa da kafa insha Allahu zan isa da wuri ya fada yana jawo tufafin shi dake rataye akusa ta dan tsaya tsaye sagale da hannu da kudin tana mamaki halin jikan nata. Tausayin shi take yadda shima yake tausayinta saidai basu da dabara sai addua a tsakanin su don talaucin da yai masu katutu a rayuwan su banda dan gidan nan da uwar garke da yayan ta hudu yanzu da suka mallaka basu da komai a rayuwansu sai hamdala ga ubangiji. Duk saurin da yayi kamar zai tashi sama ga jikin yana dan jin shi hakan bai hanashi makara ga aikin shi da yankan fara yiba kafin ya shiga class. Don har madam ta bar sakin cewa idan yazo ace dashi ya wuce kawai bata so yana zuwa yarinyar shagon ta tare shi tana tsugunta mashi jin haka yasa yayi kwana zuwa department din su. A dadafe ranan ya dauki darasin shi saidai ga dawo dole abin hawa ya nema ya dawo dashi gida yana kokarin ciro dan dari biyun daya kwana kusan bakwai cikin aljihunshi yana boyom shi yaji mai acaban yace dashi barshi kawai taimaka maka nayi aini ba haya nakeyi ba dama na kawo wani wurin. Godiya ya fara mai kafin shikan yaja mashin din shi ya tafi shi kuma yasa kai ya shige cikin gidan a kasalance daganin shi kasan jikin shi ba daidai yake maiba a ranan. Don shi mutum ne mai kazar kazar da zafin nama don yana amfani da karfin shi da kiran da Allah yai mashi na masi karfi a jika. Haka na wuni a kwance inbanda ruwan tea din da ummah ta matsa min nasha da safe babu komai a cikin cikina mama kuma tunda ta tafi bata kara lekowa part din mu ba da sunan dubani. Ummah ce ke faman zaraya a kaina har saida taga na dan samu sauki zuwa yamma na zauna ta dan rage lekoni a dakin . Allah da ikkn shi a wanan yammacin Abbam mu ya dawo daga Abuja kowa na zuwa falon shi gaidashi don haka sabian gidan mu yake . Saidai har yara suka gama zuwa baiga nazo na gaida shi ba yasa ya tambays ina mamata take ne banga giccinta ba a nan wani irin kawar da kai mama tayi gefe daya tana fadin tana part dinsu mana. Lafiya take kuwa ya sake tambaya a lokacin da ummah ke shigowa dauke da abinci don taron shi duk da basu san da dawowanshi ba a ranan amma bai rasa abinda zai ciba wanda zai saka a cikin shi. Wai maamah yake tambaya ta fada dana wani dan cicika she wai fushi mamakeyi a rana wai Abba ya dawo ranan girkin mama saboda haka an munafurceta ke nan shi da ummah. Ina mamata ya tambayi ummah yana fadin naga kowa yazo gaidani bangata ba tun dazun ya tambaya yana tsure ummah da idon jin amsan da zata bashi. Saida ta kalli mama take fadin tana daki bata da lafiya tun jiya take fama da ciwon kai dazun ma saida na kaita asibiti da safe da kan ya matsa mata. Subbahanallahi shine ba a fada min ba yanzu an samu magani ya tsaya ko ya fada yana saukowa daga saman kujeran da yake zaune a kai don yaji dadin cin abincin da zaici. Kallon mama yayi yana fadin hjy maimuna amma baki fada min ba ai dana kira dazun to ai naga uwarta ta kaita asibiti ko ta fada a dan tsiwace. Murmushi Abbacdin yayi yana fadin yau kuma salmace uwarta cikin zolaya ta juyo fuska daure tana fadin uwartane mana tunda takaita ina gidan nan nima banda labarin hakan. Ai ina na fada maki dalilin kaita tun dazun bawai na kaita da wani manufa bane wallahi naga dai za a takura makune kawai. Ni bashi ba yaya jikin nata yake yanzu Abban ya tambaya tana kallon fuskan ummah din yasa in ya kallo mama abinda zai samu a wurinta.
Chapter 10 · 0% Book details