← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 275 OF 286

Sashe 275

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikin Abba da saukin musulunci don ba a cewa ba sauki ga musulmi sai dai ace Alhamdullahu don tun zuwa a yadda muka sameshi yake kwance sai ruwa da ake faman kara masa ko wani lokaci. A haka master ya shirya tafiyan su cikin kwana uku da zuwan mu garin inda zasu tafi dashi da ummah sai shehu da zai bisu a matsayin namijin da zasu dashi. Nan mama ta dire ta hau masifa wai an kawo mata munafunci ai ansan itace zata fita dashi akace ummah a wanan karon yan uwa har da meeting hjy ta nemosu dashi a dakinta kan wai ba aiwa mama adalci ba da za a tsameta don haka saidai a fasa tafiyan a barshi nan ko ina ai Allah ke bada sauki ga mutum ba wani ba. Nan baki ya kasu biyu ana kus kus sai baba harunane yayi kindunbalan fadin asha hjy asha ashe ba lafiyanshi muke nema ba ke nan tunda har za a tsaya zaben wanda zai tafi dashi. Matan nan matarsace ta farko kuma uwar yayanshi itama haka kuma yar tane zata fita da mahaifinta waje sai muce mu bamu yarda da wanan gatan da zasuyi mashi din ba yanzu ko me ? Hjy don Allah kibar shiga irin shirmen na mata don yanzu shekarun ki sun dara yin hakan a tsaya ayi zancen Allah a nan meye zamu tsaya muna wani kwana kwana a kai bayan saukine Allah ya kawo masa. Saunawa ita hjy maimuna ake fita da ita duk fitan da yakeyi da maimunan yakeyi sai yanzu da Allah ya nuna mata nata lokacin zatace kuma zatayi bakin ciki da hakan har tasa ki tara munan kan wanan zance nata na son kai. Abin nan bada kudin shi bane itama bada nata bane muma nan duka ba a cikin jikin mu bane din me zamu zauna muga dan uwan mu zai cutu mu kyaleshi muna kallo ? Inda wani zaman lafiya tayi dasu a baya na kyautatawa juna nasan dole hjy salma ta daga kafa aje da ita yanzu don kara amma kiri kiri ana tauye mata yanzu Allah yaji kansu ya juya arzikin zuwa garesu sai kuma a nuna masu bakin ciki a fili. Hakanane yayyun nasa suka kama fada haruna kayi maganan gaskiya a nan don gaskiya hjy idan muka marawa hakan baya sai a zagemu ma a gari. Ita maimuna bata da kunya da tsoron Allah sam a zuciyar ta ina auren gaiya da wullakanci tasa akaiwa yarinyar nan tare da yayanta donta tozartasu a gidan kowa yasani ba abinda kowa bai sani ba a nan saidai in kun boye. Izzalan naka ta motsa zakaciwa mutane mutunci a yanzu ka fadi ra,ayin ka kowa yabi ina shike nan suyi ta tafiya ita kuma sai tayi hakkuri nasan ma shima ba zai yarda ya zauna ba zai bisu ya samo lafiyan shi. Kuma abinda yasa nace hakan ai kowa nan yasan maimuna itace wayayya mai ilimi ni shiyasa kaga ina mara mata baya ga komai yadda mijinta ya dauka din. Hjy abar wanan zance wayewa wani irine hjy salma bata dashi wanan wani zancene kawai kuke son ku kawo yanzu a cikin zancen nan kuma amma inane hjy salma bata iya shiga ita kadai. Sam baba haruna baiba da kafan da zancen mama zaiyi tasiri a garesu ba nan ya koge zancen kowa yaja bakin shi yayi shiru gwaggo shafa ita ke tsegunta muna yadda akayi daga baya a wurin ummah. Tana kallo suka shirya da kyar mama ta iya fitowa kofan gida rakiyansu suka nufi Abuja dashi inda zasu shiga jirgi subar kasan tare da master dasu baba su biyu akai wanan tafiyan inda su zasu dawo gida bayan sunga tafiyan su din. Mama ina wuta ta saka ummah a lokacin saidai mutane kar suke kallon ta don kowa yasan abinda ke faruwa banje rakiyan Abba ba har Abuja nan dai gida mukaje mukaga tashinsu don a lokacin gaskiya nayi nauyi cikina wata bakwai nea jikina. Aisha tana gidan mu tare damu tun ranan bata koma can ba saidai taje ta dauko kaya kala uku don canzawa zuwanshi abujane ya rakiyan Abba ya samu mahaifinshi kan zancen dawo da mummy dakinta. Murmushi mahaifin nasa yayi kafin yace a yanzu na gane ka saukin kanka yafi girman kaka babana kaida kanka kazo min da zancen wai na dawo da yabi cikin gidan nan kuma ? Ai a zatona na dauka zancen mahaifiyarka zaka fara yimun duk da a yanzu din nayiwa Rashida nisa amma ita son kai sone ba kiba sai kuma gashi kazo min da akasin hakan akan yabi a yanzu. Kada ka manta yabi da yan uwanta rayuwana suke so bani ba don wanda keson kwace maka dukiya ai rayuwanka yakeso ke nan ko wa yan nan diyan fitinan data haifa min na fara ganin irin halaiyan agaresu na fadama irin halin da yasir da salima suka shiga lokacin dana turasu karatu waje . Nayi dana sanin wanan abin don a karshe kai din dama ban saka kwandala a karatun ka ba kaine ka zamo min abin nuwa tsarana dakai zanyi tun kaho a cikin abokaina. Kawar da zancen yabi nayi maka bayanin komai a tsare nan mahaifin nasa ya dauko tarihinsu tiryan tiryan ya fara masa bayani har zaman karshe inda ya saki yabi din da irin sharadin daya kidaya ya kare da fadi. Dukiyana ta hannun Bande ga baki daya na mallaka makashi a hannun ka don haka ina sin kafin ka koma zamu samu lokaci aje can din aga yawansu a lissafa haka nan kuma zaka fara sarrafasu walau nau,in madara kona nama don shanayen suyi yawa sosai gaskiya zasu iya bayar da madaran shanu dana rukumai. Arzikina na gadone asalin mahaifiyata daga kasan Cameron suke arzikin su na gadon gadone don haka ko yaushe arzikin keda albarka amma akwai ka,ida duk wanda yasa shirme zasu kare su koma ga waninsa haka ka,idan abin yake amma su sunki su gane hakan. Gyara zama yayi cikin ladabi ya kalli mahaifin nasa a rude yace amma Abba idan anyi hakan ba a shiga hakkon sauran magadanka ba kuwa don sai nake ganin kamar anyi son kai a cikin zancen. Murmushi Alh yayi yace kai yaro ke nan ai yanzu dukiya dai tawace bata magada ba tukun don hanasu nayi yadda nake ganin ya dace ba tare dana shiga hakkin kowa a cikin ku ba. Amma Abba hannu ya dagawa dan dake sonyin magana a lokacin yace ka barshi a hakana yadda na tsara don kai baka san komai ba yabi ta zalunceni sosai Allah ne ya ganar dani da wuri ko a hakan nasan ban maka komai ba cikin irin abinda sukai min da dukiyana. Amma abin takaici da bakin ciki shine duk wanan uban dukiyan da yabi take murkusa wai ace basu ajeshi ba ko sun tanada sai a gun malamai da bokaye suke tafiya dashi don batan basira irin nasu na batatu da sukeyi. Shiru Ahmed din yayi yana sauraren mahaifin nasu kafin ya sauke numfashi yace kayi hakkuri da hakan kamar yadda tasa nabawa kowansu gida a baya haka kaima na mallaka maka gidana na apo wanda na ginasune bada saninta ba. Don haka idan kana kasan nan nan zaku dinga zama ba wani matsala na mallaka makasu halak malak daga cikin kyautatawana a gareka kuma ban son korafi a bayan hakan . Abba na gode da wanan karamcin amma nima ina da yan uwa kuma a yanzu zasu fini bukatan dukiyan ka donsu a cikinsa suka taso kaimun shiru nace na riga dana gama maganata ya fada a hasale. Nagode Abba ya fada mahaifin nasa ya amsa da shike nan zuwa safe sai a dakacesu idan sun kira muji halin da suke ciki Allah ya bashi lafiya. Ya amsa da amin har ya daga mahaifin nasa sai kuma ya zauna yana fadin a yanzu nasan kafini mabukata a kusa dakai ina son ka samu lokaci ka ware ka kyautatawa yan uwan uwanka dana matarka dama wanda duk ya taimaka maka a baya daidai gwargwado kafin ka bar kasan ko bayan ka bari din hakan zai kara habbaka arzikin ka da samun ka a kullun. Godiya yayi kafin ya kara sako zancen hjy yabi din yace amma Abba har yanzu ina roko a gafarce mu abar mummu yabi ta dawo dakinta ta zauna a cikin diyanta. Dan dattijon ya kara murmushi yana fadin baka fahinceni bane har yanzu in har yabi zata dawo gidan ka tabbatar da uwarka zata dawo gareni ke nan final ya mike ya bar dan nasa a zaune wurin. Lalai Abba ya dauko magana ke nan baisan yadda inna ta koma ba a yanzun din sai tafi hjy yabi wata kila baka matsala don haka ya mike kawai ya fice daga gidan shima zuwa masaukin su don bai sauka a gidan mahaifin nasa ba don tare yake dasu baba Ado a lokacin. Ya samu musu girki da kula da gidansun kammala abinci sun kawo masu suna ci ya gaidasu ya haura zuwa dakin da yake ciki ya kwanta saman gado yana tunane. Ina zai fara yace inna ta dawo gidan mahaifinsu yanzu abubuwa su taru su rikice masa ya rasa yadda zaiyi gashi karamin amana da suka bar mata na dan lokaci ta iya sayarwa balle nan da zataga dukiya a banza kamar ba a son su. Kwanan su biyu abuja yakaisu suka sai tsaraba suka kamo hanyar gusau wurin iyalansu suka barshi can don bai gama abinda yakai shi ba a lokacin. Su umma basu samu kira ba ranan da suka sauka sai washegari suka kira aka samu layin su nacan da suke amfani dashi a can din da suka tafi. Mun gaisa take fada muna jikin na Abba da sauki sosai yanzu hakama an fara kula dashi don har ya dan dade zaune a yau din ta bani Abba din muka gaisa dashi yace jiki Alhamdullahi. Lokacin hankalin kowa ya fara kwantawa banda mama dake fatan wani abu ya faru da Abba din don yan uwa su kuka damu sunan mu ya baci cikin dangi kaf. Ya musa yazo gidan mu mun dade muna hira dashi a ranan sosai nan yake fada min irin abubuwan da suka faru dashi a lokacin. Na tausaya masa
Chapter 275 · 0% Book details