← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 286

Sashe 50

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ciwom kanne ya kara dawowa kuma jin haka yasa na dan kai zaune saman hannun kujeran dake kusa dani ina fadin ummah kaina bai ciwo saidai idan na rufe idone sai na dinga jin tsoro. Koda barcin ya dan daukeni sai naji kukan dabba a kusa dani shine kawai damuwana yanzu ina maganin da kike shakawa yake ta tambayeni yana daki cikin jakkana na bata amsa. Dauko shi ki shaka kafin ki fita kuma ki fito nan gabana ki shakashi yanzun nan ta fada a tsigar umurni a gareni wanda hakan ke nuna ba wasa ga zancen nata. Juyawa nayi na dauko a gabanta na shaka a take na fara atishawa tasa Tani ta kawo garwashin wuta nayi hayaki hakan dana tsaya yi ya bata min lokaci saidai na gode Allah malamin bai shigo ba ya aiko motarshi ta lalace a hanya . Don haka na samu kowa na harkan gabanshi a cikin ajin hannatu na zaune da wayanta tana charting nayi mata sallama na zauna yau kinso makara ta fada daga gefena. Wallahi ummahce ta tsayar dani nasha magani kafin na fito ko tun jiya da kika sauke mu kina nufin baki da lafiya nace eh to ba dai wani sosai din nan ba. Amma kuma ai lafiya mukaje gidan nan ni har na tuna jiya kun tafi kun barni da mamaki da tausayi a raina zarah kinga gidan da mutanen nan ke rayuwa a ciki zarah ? To meye shi Allah ya nufa su mallaka a nan duniya wata kila rabonsu yana nan tafe nan gaba tunda dansu yana karatu yana kuma sana,an shi . Hakane abinne da ban tausayi wallahi ni tsohuwar ma tafi ban tausyi jifa daki kamar zai fadi har ya duka don tsufa an tangaleshi da wasu manyan itace da duwatsu. Kai sannu dai hannatu duk kin kallace masu gida ashe da kallon kwan niko banji komai ba illa wana akuyar mai kuka itace ta firgitani har mafalkinta na dingayi jiya a dakin ummah na kwana. Keko kan akuya zaki firgice haka duk wanan tsoron haka inaga kinga zaki a gabanki ko biri ido na lumshe nace ba zaki gane abinda nagani ba. Sai da malamin da yai muna lecture karshe ya fita munir yayi saurin samuna don har mun daga zamu tafi yace Mayana yaufa akwai matsala don master yayi fushi sosai damu yadda mukai mai jiya wai mun raina da arzikinshi yasa muka hada mai kudi mukai mai sayayya ko ? Kai haba dai hannatu ta fada a cikin mamaki nace nayi wanan tunanen kuma na fada maku zaiga mu raina mashi ai. Wallahi kin fada kuwa aina fada mai komai na kuma bashi hakkuri saida naga kamar ba zai kara koya muna ba yadda ya nuna don yace shi badon mu biyashi yake koya muna ba saboda Allah yake taimakon mu. Yanzu yaya za ayi hannatu ta tambaya manir din yace ai shine na fadawa mayana ko zata bashi hakkuri tunda dama don ita yake koyar damu din don mu albarkacinta muke ci kowa ya sani. Gaskiya ba zan iya mai magana ba don ina jin kunyar hakan yanzu yaya za ayi don gaskiya ni namafi fahintar shi akan malaman nan wallahi. Hakkuri zatayi ta sameshi da sauri nace dasu but not now don na fada maki bana jin dadi yau gida nake son naje na dan kwanta. Manya ke nan yadda kikeso haka za ayi indai har zaki roka muna shi din nace naji na kalli hannatu nace muje don tare muke fita daga makaranta wani lokaci yanzu tunda muka dan saba da ita. Ban samu ganin shi a rana ba sai bayan kwana biyu ga matsin da yanzu nake gani a wurin mama yafi nako wani lokaci. Don yanzun yakai mama ta rufe damu har ummah ta dauki gaba tanayi damu wanda mu bamu san dalilin hakan ba garemu . Tundai dawowan ta lagos hakan ya fara don sun dade a can sai su Rukkaiya da yan aiki ke part din ta ita Aisha daga baya tazo tabi mama da suka dawone ta fara daure muna gaba daya. Sai kuma da Abban mu yazo shine har yakai ko muna gaida ita zata nuna muna bata jiba kawai ta kyale ganin haka ummah tace mu kyale ta ida mun ganta dai mu dinga gaida ita koda bata karbawa. Sai hakan ya dinga damuna tunda ba,a saba hakan ba a gidan namu don akwai lokacin dana sameta falon Abba suna tare na shigo bansan tana ciki ba na gaida Abba kafin na juyi na gaida ita. Ta kyaleni Abba yace mata bakiji bane ana gaida ke tace konaji me zance da ita badai diyana suna gaidani ba to ai Alhamdullahi. Wani irin zance ne wanam kikeyi haka maimuna tace zancen gaskiya yanzun ne a gabanka zatace zata gaidani yarinyar da gani gata take wucewanta yanzu kamar bata ganni ba. Da sauri na dago kai na kalleta kafin na daga ido na kalli Abba din yai min alama da hannu na kyaleta nace mama kiyi hakkuri son Allah. A, a wanan ya rage gareku fa keda uwarki ni dai nasan ba zaku tsunci komai a gareni ba in kuma karyane mu zuba nidaku a gidan nan a gani murmushi naji Abban yayi ya dago yana fadin maamah ya akayine kuma , ? A, a dama na dawo naga motarka kana gida na shigo in gaida kai yace to nagode ai ina nan zan kwan biyu tare daku nasan dai shikikewa karna wuce bamu haduba nayi murmushi na mike nace mu wuni lafiya na barsu tare tana jan tsuki. Irin wanan abubuwan suke damuna yanzu har nake dan rama zuwan Abban namu yasama na mace da zancen neman shi muyi maganan sai gashi mun hade dashi ya fito sallah mu kuma muna zaune su hannatu na hira ina duban wayata hannatu ce ta zungureni take nuna min shi tana fadin. Ga Master namu can fa sarkin ka,ida waifashi da gaske guy din nan keyi yayi fushi damu ke nan ba zai koya muna ba daga abin arziki saiya zama muna dan kari kuma ? Hannatu ku dinga yiwa mutane adalci mana don kowa akaiwa haka zaiga an raina mashi wayaune fa na fada ina mikewa zuwa wajen shi. Da alama sauri yakeyi lokacin amma yana ganin na nufoshi ya dan rage saurin da yakeyi da ganin shi kaga irin daliban nan yan ba ruwan mu karatu ya kawomu . Kayan jikinshi da nake ganin irin wanda basu shiga din nan bane a cikin kayan da yake sayawa ya saka abinshi hakana kodai kodai dasu ya saka abinshi a jiki. Na karaso tare da fadin brother ina wuni yaja ya tsaya tare da dab gyara tsayuwan shi kayi wuyan gani fa na fada. Ya dubeni da kyawawan idanun shi yace abubuwane sukai min yawa kwanan nan kisan tallaka baya zama wuri daya ai ina nan ina can ko yaushe. Kodai fushi kayi kan zuwan ba zata da mukai maka don Allah in hakane kayi hakkuri munyi kuskure hakan ba zai sake faruwa ba in sha Allahu. Suma din abin ya damesu a yanzu tun days ago sukace na baka hakkuri dan Allah ban samu ganin ka bane sai yau din nan don Allah kayi hakkuri. Yace babu komai ni zuwan ku don baku ganni ba kwana biyu yayi min dadi saidai dawainiyar da kukasa kanku shine ya dan sosa min rai don zakuzo wurina shine sai kunyi wani dawainiya irin haka ? Nace haba ba don wani abu bane mukai hakan niya alheri kawai sukayi ma don sun rasa me zasuyi mane su dan rama alherin ka garemu. Yace toh nagode amma next time don Allah karku sake irin hakan nayi murmushi tare da kallkn shi nace su dai amma ni ai dan uwana nayiwa koka manta kai yayanane kuma ? Yace ta nan zaki fito min kuma zarah to ai nine yayan ni yakamata nayi maki bake ba nace a yanzu nice din dai zan tallafawa yayan nawa ko zai daina shiga rana haka cikin wahala. Kai wanan ashe kina magana irin haka nace ai dole master yayi fushi da daliban shi su kuma sun sakani gaba na roka masu kai ? Su hannatune daga bayan mu suke fadin master muna gaisuwa baka jimu ba wanan uwar kwarkwasan ta dauke maka hankali da surutu. Shima murmushi yayi tare da fadin kanwar tawace kuma kuka radawa wanan sunan mai kama data wata babban mace can ? Suka kwashe da dariya tare da fadin afuwan master ita dince ta faye jiji da kai da wuya kaga ta tsaya irin haka tana magana sai taga dama irin wurin ku manya. Haka muka dan taka dashi har zuwa inda zamu shiga building din mu shi kuma zai shiga nasa lokacin ne na dan juyo ina fadin a gayar muna da kaka ya danyi murmushin gefen fuska yana fadin zataji itama tana tambayana ku . A haka muka kara shakuwa sosai dashi har yakai nice yanzu nake aje mai kudi idan ya tara shakuwan mu har ya zama mutane sun fahinci da muna tare dashi sosai. Sai dai basu fahinci meye a tsakanin mu ba saidai sunfi daukan abinda irin shakuwar dalibai din nan ne na karatu nake karuwa dashi shu kuma yana dan samu daga gareni don ganin canjin da sukayi a garseshi yanzu.
Chapter 50 · 0% Book details