Sashe 189
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tani data hadu dashi zai shigo asibitin ya tsaya suka kara gaisa nan kwarmaton ta ya debe wurin dadin hira har take labarta mashi abubuwan da suke faruwa kafin tayi mai sallama zataje taron yarane ya biya mata kudin mashin ta dane zuwa gida. Da sallama ya shigo dakin sai ga su Hannatu suma sun shigo tare da Dije da kanwarshi Aisha dauke da ledan pure water a hannun Aisha din. Gaida ummah yake jin hakan yasa na juyo ina masa kallon mamaki lokacin hannatu ta gani take fadin masha Allah kintashi matar master ? Duk suka juyo suna kallona to keyi kwana na rigaki karban jakkan tun dazun ai har na banye na bar maki ragowa jin hakan ya dan sani murmushi kadan ina kokarin juyowa. Sai ya mike ya nufo bakin gadon yana fadin kin tashi Zahra ya jikin naki yana kokarin taba jikina lokacin Dije ke fadin kai danga ga idon uwarku kana kokarin taba matar ka gaba mu ? In bakaji kunyan idona ba aikaji na uwarku ummah ta mike tana fadin mama ki barsu sallah zan tafi yanzu inyi ni to Dije ki bita kada ki zauna ki saka muna ido Aisha kai masu ruwan nan sai suyi alwala dashi. Babu Faro ne hannatu kuka sayo wanan ga ummah da ledan Faro kuka dauko ai da sauri ummah tace a a kai wanan din ma ai muna amfani dashi sosai ko a gida. Bari dai a je a sayo makushi wanan din sai a aje don wani amfani zauna abinka don Allah wanan ya wadatar ai lalurane ya kawo hakan. Jin hakan ya koma ya zauna yana fadin hannatu ko zaki zuba mata abinci ko zataci wai to Allah yasa tunda kana kusa amma rabon zahra da abinci ni har na manta ta fada tana mikewa da kyat na daga mata hannu alaman ta barshi. In serious voice yake fadin don me zaki zauna da yunwa a cikin ki haka kina gani yunwama ai yana iya kara maki ciwon na girgiza kai alaman a a. Naji yace haba princess ko yunwa na kara maki ciwo ai ki daure ko ba yawa kici ko kadan ne haka nake fada mata amma da takai baki zata dawo dashi. Wani kallo naga yayiwa hannatu dake bayanin hakan gareshi kun fadawa likitocin haka duk mun fada masu yadda take ji din sun dauki bayani. Tun kan a kawo abin na kawar da kai ya karba wai ya bani da sauri na rufe bakina kamar wanda yaga mugun abu a lokacin guda yayi yayi na juyo na karba na kasa. Haka ya hakkura ya mike tsaye ya fita ya dan jima sai gashi ya dawo da leda da kayan sanyi a cikinsa ya samu sun shigo dakin ummah tana min fadan cewa na don me ba zan daure koba dadi inci abincin nan ba. Ummah ku barta ko zata sha wannan yana kokarin budan ledan ya zaro goran fresh milk ya miko min yana kokarin budewa tare da fadin ki daure ga wanan ki dansha ko kadan ne. Yadda na karba a hannun shi hakan ya tayar mai da hankalinshi karkareni daya ga yadda na fitar da idannuna waje saida gaban shi ya fadi don tsoro. Wani iri yake ji lokaci guda kanshi na wani irin juyawa hankalinshi na neman gushewa gare shi Allah ya taimaka yayi dabaran mikewa zuwa wajen dakin da sauri zakace ya tuna da wani abune a lokacin. Ruwa ya saya ya tsiyayya a kanshi tun wanan lokacin ya koma wani sukuku dashi kamar wanda ke ciwo ko dakin baya son shigowa sai dole in ma ya shigo can kofa zai tsaya yai maganan da zaiyi ya koma. Ummah ce ta farga da hakan ta farawa dije bayanin amma taga Dijen bata gano komai data gano ba sai bayan sallah magariba ta dawo daga sallah ta sameshi zaune yayi tagumi shi kadai a wurin zaune. Har zata wuce ta gano shine tace Ahmed ne wai ya dago kai da sauri yana mikewa tare da fadin barka da fitowa ummah Allah ya karba tace amin. Lafiya dai na ganka haka tun dazun nake lura da sauyi gareka saidai ban san me ya jawo maka hakan ba lokaci daya ta fada tare da tsureshi da idanunta. Eh wallahi dama ba komai bane saidai ban san ya za a fahinci magana taba yanzu idan na fada don gaskiya na fahinci ciwon nan na zahra kamar dai bana asibiti bane kawai kamar ya dan surku da harkan jinnu haka. Wani kallo na tsab ta aika mai dashi lokaci guda kafin ta sauke ajiyan zuciya tace eh zai yuyu hakan ne don nima nayi wanan tunanen amma yanzu tunda munzo saimu dakata muji abinda sakamako zai bada kafim mu san abin yi nima dai hankalina bai kwanta ba a yadda nake ganin ta din nan. To shike nan ya fada tare da dan sunkuyar da kai katsa tace Allah ya kyauta ya amsa da amin ta nufi hanyar shiga dakin da nake kwance. Sai kuma taja ta tsaya tare da dan juyowa ta kalleshi tace da badon akwai gajiya a tare da kaiba dakayi sakkon zuwa zuwa funtuwa gobe kaje kaga wani kawuna a can da ake kira malam Idi mai rafannan acan. Da sauri yace ba matsala sai inje din ko yanzu badon dare yayi ba aida zan tafine tace a,a ka bari zuwa gobe din nan tayi mai kwantace yace ya gane insha Allahu kuma zai tafi din in Allah ya kaimu da safe sukai sallama take fada mai tunda jjkin nawa da sauki zata koma gida tunda ga Djje da hannaty har da Aisha. Tayi waya azo a dauke karfe goma yayi mata godiya ta juya ziwa dakin ya koma ya zauna nan dije tazo suka zauna suna dan tatataunawa kan zancen matsalan nawa. Cikin bacin rai ta juya tabar dakin ganin ya dauki waya ya fita batun ta ya nuna baida lokacin ta kamar yadda tayi mai itama ke nan da safen. Saidai bata dauki nata da sunan wullakaci ba sai nasa don haka ta kulla a ranta cewa ai don hjy murja dince yai mata hakan bako sauran zaman lafiya ke nan a tsakanin su a gidan . Don haka zata kada masu gangan shedan da sai duk sun raina kan su suyi da sun sani da basuyi mata hakan ba a rayuwan su don ba a takata a wanye lafiya a rayuwan ta. Ita mace ce dake tsaye da kanta da yayanta a ko wani lokaci tayi a mannan cewa boka da malam suna biyawa mutum duk bukatan sa idan ya nemesu. Da wanan kudirin takai dakinta ta kwanta tana faman saka yadda zata fara bullowa zancen da hjy murja zata fara koda maigidan yanzu nan tunanen ta ya tsaya akan zata yakesu a lokaci dayane don da zafi zafi ake buga karfe. Mai aikinta ta nema da sunan bata umurni akan ta san ita dai ta daukota aiki a gidan nan ko daga lokacin aikinta zai tsayane akan ita da yayanta da mijjnta kawai a gidan. Da sauri Asabe ta dago kai ta kalleta don jin umurnin da tabata a lokacin kafin cikin ladabi tace hjy ki gafarceni jiyan nan Alh ya ban umurnin da a hade girki ga baki daya a gidan nan. Itama din wani kallo ta jefeta dashi a harzuke take fadin Asabe nina daukoki gidan nan ko shi kece hjy Asaben ta fada cikin rawan murya. Tace don haka nina baki umurni da haka idan ya tambayeki dalili ki fada masa ninace ai hakan ki tashi ki van wuri Asaben ta mike da sauri zata tafi sai kuma ta dakarta da ita tana kare mata wani mugun kallo tace. Wai yaushe har kika samu daman yin magana da mijina haka ban sani a gidan nan wani iri Asaben taji sai ta daburce lokaci guda kafin tace da sauri a,a hjy jiyane da ina tsaka da aikin yamma ya shigo kitchen ya fada min. Wani kallon banza ta bita dashi kafin ta kawar da kanta gefe ta fita batun ta ta dan dade a duke kafin ta mike da sauri ta bar dakin tana watsa mata zagi a zuciya da fadin macuciya karyan ki dai ya kare tunda kishiya ta shigo gida nan da sunan zama. Har takai kitchen din tana tunanen yadda zata bullowa zancen Allah da ikonshi taji muryan maigidan waje yana magana yan aikin gidan maza. Nan ta dauraye hannu ta sameshi ta rusunna daga bayan shi tana gaidashi kafin tace dama Alh hjy ce dai ta kirani dazun nan ta ban umurnin dana daina girki da hjy karama da duk wani aikin daya danganta da ita a gidan nan. Ya juya gareta a cikin mamaki sai daga bayan shi kuma yaji mazan na fadin muma dai Alh munsan hakane zai cika damu gun hjyn . Don yana da wuya ta barmu muyu wani aiki daya shafi hjyn a gidan nan din ko baki akayi mukai masu wani abu zata zagemu tace zamu bar aiki balle wanan da take ganin kishiya a gareta yanzu. Innalillahi ya ambata kafin yace duk ku saurareni cikin tsawa shin hjy ce ke biyan ku koni to ku sani daku da ita duk a karkashina kuke har wana din datazo daga baya. Don haka kowan ku ya tsaya iya matsayin aikin da aka daukeshi a gidan nan wanda bai iya bin umurnina sai nata ya fada min tun yanzu na sallameshi. Kafin ya bisu da kallo daya bayan daya can kuma ya numfasa tare da fadin bayan hakan tunda aiki ya karu yanzu zanyi doubling din kudin kowa a cikin ku ga wata kai driver mai kai yara school. Zan kara ma kudin ka ya cike dubu hamsin haka mai wanki daba shuka ruwa kaima kudin ka a yanzu zakai arba,in da wani abu sama ke kuma ga wata nan zakuyi aiki tare zan baku a wata dubu arbain da biyar duk wata maigadi kuma dubu arba in. Kallon juna sukeyi kafin Bala driver yace Alh ai dama ni sha biyar ake bani duk wata yace what yace kwarai kuwa Alh ga yan uwana nan ka tambayesu kaji maigadi yace goma ko takwas ake bani ba da abinci ba hakama mai wanki da