Sashe 255
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
nima yar iskan kaina ne don inbata fada min da bakinta ba zan nuna mata kamar banji ba nima a tafi a hakan. Sai ga wayan Rukky ta dauka tana fara,a tace wai mama ashe zahra ciki gareta ta haihu yanzu wata kawata ta bugo min amma zahra taji dadin ta wallahi. Ke banson shashanci kawarki data bugo maki uwarkice ko kuwa idan naji kin kara zancen nan ranki zai baci kuma ki saurareni da kyau kiji kada inji kinwa salma barka idan kinzo gidan nan. Amma mama ita ai tana kiran mu mu gaisa don haka kinga ba dadi ta haihu bamuyi mata barka ba ai ta fada cikin wani murya. Idan ta kira ta fada maki yi mata murna a waya shike nan idan bata kira ba ki shareta kinji ai naji mama ta fada a sanyaye ta dangwarar da wayan tana jan tsuki. Ba afi minti goma ba ummah tayi sallama dakin ta amsa a gyatsare ta shigo suka gaisa take fadin hjy kinyi sabuwar kushiya fa don Alh yau angone. Yarki ta sauka lafiya dazun nan suka bugo muna ta haihu cikin iya tako ta dago kai tana fadin wace yar tawa tace zahra ta sauka yau da asuba din nan. Zahra dama zahra nada cikine koda ta tafi haba hjy maimuna zakice bakiga ciki a jikinta ba lokacin ina zan gani tunda ba a taba fada min ba cewa tana da ciki. To ta sauka dazun ummah ta fada Allah ya raya tace kafin ta fara kiran mai aikinta tazo ta dauke cup din data karya dashi a gabanta ganin hakan yasa ummah ta juya ta fita sai ji tayi mama din na fadin. Saukin abin dai kowa ya haifa ai dan haka ba maima wani cin fuska kan da a gidan nan idan banyiwa mutum ba yace zai mun sai mu zuba dashi ai. Kai jama,a ummah ta fada data shiga part din ta Tani ta kalleta tace tayi halin ko ummah tayi murmushi tace bari Tani gara da Allah yasa bakije din ba da kinsha bakar magana yau a wurinta. Don cewa tayi bata san wanan yar tana da ciki bama wai wai mutum tsufa baisa ya tuna da mutuwarshine bafa a nan zamu tabbata ba fa ? Abu dai anyishi tunda kurciya yanzu girma yazo ba za a gyara hali ba a zauna lafiya kullun abu sabo yake komawa kullun ya kamat ace zuwa yanzu an aje wanan kishin ana duba yara kuma. Hjy ke mai tunane kika san wanan amma ita hjy ai har yanzu duniya sabo yake gareta sam wanan matar bata tunanen mutuwa ko kadan balle ta daina wani halin nata. Tani me akewa kishin yanzu shima wanda ake fadan donshi ta kansa yakeyi yana neman lafiyasane da abin rufin asiri tunda komai ya kare yanzu kowa ya gudu. Ai hjy akwai rufin asirin Allah don ba kowa bane zai gane hakan yanzu saina tare daku kadai zai gane gaskiyan su kuma masu gudun dama akwai ya kawosu ba mutunci ba. Don shege akewa ya manta halarci yanzu mu mugudu muje ina ai sai duniya ta zagemu kan zunubin mu. Abba ya bugowa mama waya yana zolayanta amma haka mama ta fuske ta nuna mashi shidai akaiwa haihuwa tunda yarshi ta haihu ba yarta ba. Yaji maganan bambarakwai yasan akwai magana don haka yace to Allah ya sauwaka dama na kirane don mijin nata ya kirani kan zancen su, , , Alh ba uwarta na nan ba ka kirata mana ku shirya abinku don Allah ka fitar dani cikin wanan zancen bana son fitina ka barni kawai. Ok shike nan Allah ya sauwaka zan kira ita salma din tace yafi ummah din ya kira suka aje yadda za ayi zasuyi taron sunan su a nan gida kamar yadda aka saba yiwa kowa. A wurin mahaifinshi ya samu aka zana suna gidan inna da gidan mu akai taron sunan kamar yadda aka saba a al,adan bahaushe. Inda yarinyar taci sunan khadija sunan dije ya roka a saka mashi mahaifin nasa ya saka mai nan ma gidan inna manyan raguna biyu tasa aka yanka gidan mu kuma rago daya da shanu gidansu kuma a can mambila Abban ya tura akayi komai Allah ya raya muna baby khadija Amin. Ranan inna tayi yadda take so don komai daga ita sai diyanta suka katantane komai sukayi har da dije ta dauko suka sha rawa da zawarawan unguwar ana hakane sai ga yan gidan mu sun kawo masu gara . Wanda a wurin mu ya zama kamar ibada idan bakayi ba abin fadene gareka inkayi din kuma yai kadan a fadi ko inyayi yawa a yaba. Don haka ummah ta shirya gara na gani na fada aka kawo gidan inna din dako har sun fara yada magana da sukaga anyi azahar ba a kawo ba suka fara fadin su wa yan nan mutanen me suke nufi ba zasuyi gara ba ke nan sun samu hanyar cewa yarsu bata gari ko ? Saiga robobi sunga ana shigowa dashi sai buhuhuna da jarkokin mai da sauran kayan miya na baki ya mutu ga kowa aka shiga kuma yaba kokarin mutanen gidan mu. Inna ta kara rakashewa tayi yadda ranta yakeso a wanan harkan bamu me kwaba mata sai abinda taba mutane a can gidan mu kuma an kwasa da mama. Don tun lokacin da taga shanu an kawo da ragp hankalinta ya tashi sosai ko kadan ummah bata sakata cikin sha,anin ba kamar yadda tace taje tayi ita kadai. Nan kuma mama din ta shiga yankar kauna tana zagin su gwaggo shafa wai sune munafukai don sunga arziki yanzu idanunsu ya rufe a wurin ci. Saidai duk abinda akayi ummah tana dibar mata nata har hjy tsohuwa kakarmu anci ansha don master ya taimakawa ummah da Abba da kudi yace su kara wurin harkan sunan.