← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 286

Sashe 128

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da alaman yar arzikin nan ta shigo wai tazo yiwa uwarka gaisuwa bama nan. Har suka kawo muna wanan abin arzikin haka wai ace muna abokan karatun kane suka zo da motar su yaran nan na fadin abun gwanin ban sha,awa. Dan Dije ina kasan yaran masu kudi haka har suna zuwa da wanan irin alherin mai yawa haka uwar ta jefo mashi tambaya daga inda take zaune kofan dakinta tana cin abinci. Yace mama gashi sun fada abokan karatunane su din yar gidan wani mai kudine a garin nan jinin mu ya hadu dasu muke cin alherin su haka. Dan Dije kabi sannu banson daukan magana ka tsaya matsayim ka da Allah ya ajeka kada ka dauko muna fitinan da yafi karfin mu don hurda dasu tonon asirine a gareka karshe. Wane irin magana kikayi haka mara dadin ji don suna mutunci shina ka zama tonon asirinai ? Ba hakana bane inna ke san yadda duniya yanzu ta koma kowa baison ka rabai ka karu yar mai kudi sai dan mai kudi irin ta hakama dan tallaka ya tsaya matsayinai. Yafiki sanin haka shida a namiji yana jin irin abubuwan daka hwaru a gari yace maki soyayya yakai da ita ina zai fara haka gwalmadiya,i ya debowa kainai ruwan dahwa kaine . Wane uba ka tsaya mai duk garin nan a bashi yar gidan mai kudi dan dama dama da ubanai ya tuna dashi har ansanshi a dauki mata a bashi. Nina dade ina jiyowan wan ga ranan gare mu don nasan a lokacin nan za a tayar muna da tsohon hwamin daka zuciyoyin mu anyi haka dauri balle yanzu da kan kowa ya waye. Wani iri yaji a zuciyar shi daga shi har mahaifiyan tasa sai da kibiyan tsoro ya caki zuciyar su lokaci guda uwar tasa ta dauka da fadin . Yanzu ai kin gane abinda naka nufi ke nan ni rigimana banison ya dauko wa kanshi da abinda yasan bashi yuyuwa garai. Wanda ko ubane bai taba gani ba sunan kana dan halal ne kawai kaka zuwa gidan masu hannu da shuni kakai kan ka ? Wa hwada maki bansan ubana ba saukin abindai ina da uba da yan uwan uba don haka kko hwada min ina bashi amsa yanzu. Ya mike tare da saka takalmanshi ya fice a gidan Dije na kiranshi yazo yaci abinci baiko tsaya kulata ba ya wuce don rashi daya baci fa baki daya a lokacin. Wuri ya samu ya zauna a gaban gidan su baisan lokacin da hawayen bakin ciki ya soma fito mashi ba sai ranan ya tuna da malam musa. Waya ya ciro a cikin aljihun shi da niyar ta kira tsohon don sun kwana biyu basuyi waya da dattijon ba da yanzu ya zame mai kamar mahaifin shi yake jinshi a ranshi. Ya kira bai shiga ba ya sauke ajiyan zuciya yana sake kiran dattijon sai tayi sa,a kiran ya shiga ya dauka suka fara gaisawa yake tambayanshi shattu . Sun dan jima suna magana kafin su kashe wayan suyi sallama da junan nan su ya bike ya buga mashin dinshi ya bar unguwar bai dawo ba sai cikin dare sosai ya shigo gidan ya samu wuri ya kwanta. Lalai kan naji labarin cewa su Aisha sun tsayar da mazajen aure kuma na tayasu murna sosai ga hakan sam ban kawo rai da cewa wai don sunyi hakan nima na fitar da miji kona fara kula samari ba don ba rasasu nayi akwai su saidai babu fuska gareni ne don irin tsawatawan da Abba yai min a baya. Yasa yanzu na kara mayar da hankalina sosai wajen karatuna ban yarda koda wasa ma in tsaya da wani wai ina zance. Allah sarki ashe duk da hakan ba tsira nayi ba a wajen mama don sun hada min bom nida ummah dayasa zukata baci a gidan namu don ko Abba yai wani zuwa gaisuwa . Don anyi rasuwa suka zo hardasu yaya musa da ya jafar lokacin nan mazajen su Aisha suka zo gaida Abba din kuma suyi masu gaisuwa. Bayan sun wuce ne da dare suna falonshi da yayyunmu maza ana maganan a kai har aka jefo zancena cewa ni wana tsayar ya musa ne ya tare da fadin. Haba dai Abba Zahra fa karatu takeyi yanzu bawai lalai bane ace sai tare za ai masu aure dasu kafin ya karasa mama ta haushi da fada tana fadin to uban mu. Zama zarayi gidan ku jikata kusha ko me yarinya da wanda take so zaka wani kawo tsurku ka tare kana fadin wai tana wani karatune yanzu. Suma din ai karatun sukeyi bawai sun gama bane ko wanene take so yanzu din Abban ya tambayi mama din tace a wanan yaron daine na kwanaki mana don basu rabu ba tunda shi take so. Yaron da baida asali din dana rabata dashi ashe ta nace saishi mama tace a toh suna dai tare don basu rabu ba gaskiya tunda bata ba wani fuskan zuwa ba. Abba baida asali kamar yaya ya musa ya fada cikin dan bacin rai yace ta fada min fa ubanshi dan shiyoyin gabas din nan nd kuma har yana zuwa garinsu . Mama tayi saurin fadin kaji ba Alh ai na fadama ka barta kawai tayi don kada ta jawo muna abin kunya don Allah shi aure ai mukaddarine in Allah yayi shine mijin ta ba makawa sai anyi auren nan Alh. Da rabo yazo ya kashe ai gara ka yarda ka aura matashi a zauna lafiya haba haba mama wanan maganan bai dace ba haka ga zahra don kowa yasan irin natsuwan zahra din. Wanan yarinyar na gane abin kunya take son ta jawo muna kawai Abban ya fada cikin bacin rai mama tace ai shi nake fadama wa yan nan sakarkaru suna wani tarewa kada in fada. Karshe in wani mugun abu ya faru duk laifin mu za azo agani ace mun saka ido akai barna a gidan nan yadda take magana zakace wani mugun abu nakeyi a rayuwana. Abba yai shiru na dan lokaci kafin yace shiyasa kwanaki da sukaje kano karima ta samo mata wani a can yarinyar nan taki zancen nan . Kadai fada kaima yanzu ai indai har abu ya kwabe wanan kuma kai kajawa kanka Alh Abba din bai iya cewa komai ba a lokacin sai shirun da yayi. Bayan kwana biyu abin yana cinsa sosai a ranshi ya kira maigadin gidan mu yana tambayan shi wayaga yana zuwa wurina ? Mamakine ya kama maigadin yace Allah ai mama boyar Allah ce don ban taba ganin wani yazo gidan nan ba wurinta da sunan hira ba. Idan ta dawo ta shige gida ta shige ke nan sai kuma idan zata fita da safe gata bata kara lokaci ga yadda ta saba dawowa kullun. Tashi kaje kawai Abba ya fada ya mike yana mashi godiya ya fice daga falon Abba ya dade zaune yana tunane kafin ya yanke shawaran abjnda yake gani daidai a gareshi yabarwa cikin shi sauran zancen.
Chapter 128 · 0% Book details