Sashe 145
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
dauki kwano ta shige daki ta barsu da kayan a wirin don haka yar babban ta jawo basket din ta bude tana kallon abinda ke cikin warmes din tana yamutsan baki tare da fadin. Wanga abu aiko ni daya ina iya cinyeshi innan mu kega abinda akan zubu muna wai mu duk addashi haka tana karkata abin abincin don takaici. Cikin kashe murya kada Dije taji su uwar tace a,a wallah waka magana yanzun innan mu tayo cikinai tace za a damu yara. Walle magana akai ke tai kice ta karo muna wanga ko ku baya isa balle mu duka yar naima da bakin rowan tsiya kamar nagode wanga abincina za a kawowa mutane shiya. Ina daga cikin dakin zaune ina zancen zuci naji muryan sama sama ana sallama a gadarance na bude labule ba gaisuwa ko wani magana yarinyar ke fadi a wullakance . Wai inno tace ki zubo muna mai yawa wanga daki bayar baya isan mu ko muna balle dasuwa na kasa fahintar mai take fada saida ta kara maimaita mun maganan ta na gane. Cikin dan fara,a nace ayyah wallahi shi kadai na zuba babu wani sai naga tayi min wani kallo kafin ta juya tana magana kasa kasa cikin fisge fisge ta tafi. Na juya ina shiga daki tare da dinbin mamaki bansan lokacin da hawaye ya zubo min ba a fuskana natakaici da bakin ciki don bawa kowa rainin wayau banso kuma ni ayimin hakan ko kadan. Ga wa yan nan mutanen da alama suna da irin halin wullakanta mutane din nan irin na nakasa dayiwa mutum kallon rainin wayau da wullakanci. Mii kawoki sashena ya tsare kanwar da tambaya tayi tsuru tsuru da idanu nan ta fara inda inda tana fadin innota tace in taho a karo muna abincin don baya isan mu . Idan bai isa ba kuba zaku iya dafawa ba koba akwaishi a wurin kuba an kai maku naku nan dai ya tsare yarinyar da fada sosai yaci mata mutunci ta tafi . Tana shiga part din su ta dangware kulan dake hannunta ta fara cicika uwar ke tambayan ta da mi ankai maki kuma kinka dawo kina wagga cika haka ? Ni dai naji motsin shigowan shi dakin amma banga ya shigo ciki ba naji fitan shi kuma can ya samesu a part din baiga Dije ba a wajen ya shige dakin Dije din ya sameta zaune. Yake fadin Dije mi da baku dafa abincin ku ba nan ba komai na aje maku ba ga kuma wanda aka kawo gidan su princess. Wani abu akayi ko wanda ta sako muna kaka magana kaine yake fada mata an tura Asmau ta karbo wani yanzu wai wanan baya isan su. Sallati Dije din ta saka tana kokarin mike tsaye ta tashine kanwar mahaifiyarshi ta shigo tana fadin kai dan Dije karanmu kakawo inda innan mu don mun aikawa matarka ta kara muna abinci wanga data sako muna bai isan mu ? Inna Shatu dole in yi magana yarinya ga bata saba da rayuwa haka ba yanzu yanzu da kawota zaku daga mata hankali don gudun hakana hau yasa na kawo komai nan na aje maku. A,a yanzu ai shike nan ni gobema tahiyata zanyi gida dama son tasan wadda akayine ta gyara yasa ankayi mata magana nikan gobema gidana nayi gumi zan komawata. In ke tashi kitai anka nice kitai anka wane irin dabia na haka wai kuka son tsirowa mutane dashi yace dije saida nace kadama tayi da kuwa. Tace a, a ko banza akwai hakkin makwantaka bata iya girki gaku gida bata saka maku shiya ba data bi maganata ta kyale da duk wanga ba ayita ba tsakanin mu. Waishi hauda yakayi don abinci walle da yaranga basu cishi ba da an maisuwa masu da abincin su kaka zuwa nan ka kawo wa mutane diban albarka wai kai mai mata. I aniya in baka koma mijin tace ba gidan nan jin fadan mahaifiyar nasa yasa ya mike ya tsaye ya fice daga dakin dije din kaitsaye ya shige su ya fice suka bishi da kallo. Ayadda nake ya sameni yana sallama ban iya amsa mai ba yake fadin lafiya ko wani abin tazo tayi maki a nan din ? Kai na iya girgiza masa don ba zan iya magana ba shiko yayi min tambaya kala kala ina bashi amsa da kai don ban iya magana da baki don yadda nake ji a lolacin nadai nuna mashi ba komai a lokacin . Yace zahra idan kina wanan yanayin ba zanji dadi ba don sai in dauka ko nine bakiso ko yanayin gidan namune bai maki ba . Yana fadin hakan na mike na shige daki na kwanta rub da ciki naci gaba da kukan da nakeyi harda shesheka ina hadiyan zuciya. Can ya shigo ya dan tsaya yana kallona tare da fadin o,o zahra tun farko gudun haka yasa na fada maki kiyi girkin ki iya bakinmu mu kadai. Can kuma ya kai zaune yana fadin haba zahra idan na bata maki rai ko wani nawa don Allah ki daina kukan nan kiyi hakkuri don Allah. Da kyat na iya budan bakina murya ciki ciki nake fadin No Master ba hakana bane na daiga na zuba masu abincin ai kuma zasu dawo har yarinyar na nema tayi min rashin kunya haka ? To kiyi hakkuri ki daina kukan nan ni zan dauki matakin hakan da kaina don ko zan hanasu shigowa part din nan ga baki daya. No ka barsu idan kayi magana tsanata zasuyi ga baki daya kaga kuma hakan ba zai min dadi ba don Allah ka kyalesu kawai nima ba zan kara kula haka. Ya zauna yai shiru ya dade zaune a hakan ba tare da yai magana ba sai zuwa can yace kiyi hakuri don Allah nasan ki da hakkuri ki kara har zuwa lokacin da Allah zai bamu namu wurin mu tashi daga nan din insha Allahu. Ba komai nace na juya nayi shiru kowan mu yana tunane kafin a kirani a wayata na duba ummah ce don yanayin muryata naki dauka. Ya kalleni yace waye ke kira ba zaki daga wayan ba ki amsawa maishi ummah ce na bashi amsa yace ki dauka mana sai hawaye ya zubo min na kifa kaina a filo ina kuka ganin hakan shi ya daga wayan ya dauka. Tare da sallama yace ummah ina kwana ta amsa mai yake fadi cikin ladabi wallahi ummah gata kwance bata jin dasin jikintane tayi barci. Allah ya sauwa ummah din ta fada tare da fadin dama kannen kune suke son a kawosu wurin ku tunda basu da lafiya a bari sai wani jikon ya aida an barsu sunzo ummah tunda gani. Tace su bari wani jikon sazo yau dai kan suyi hakuri kuma takardun ta suna nan kaf na hada mata a wuri daya zansa Tani tazo mata dasu anjima ta duba jikin nata yayi mata godiya ta kashe wayan.