← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 286

Sashe 78

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ban ganin kowa. Sati biyu muna hakan har kowa ya gama fahintar komai ranan monday bayan mun fito daga daukan karatune hannatu ta tutsiyeni da tambayan dalilin rashin zuwana group discussion a yan kwanakin nan ? Ba komai kawai na daina hakan ne don nima na koyi fahinta daga malami da kaina wani irin kallo tayi min ta sake murmushi tare da fadin. Zahra kenan kina ganin a dan zaman mu tare a school din nan ba zan iya fahintar halinda kike ciki ba ke bake bafa har su manir da sauran su ina iya fahintar yanayin su suma maza. Nasha zaki fada min don muga ko za a iya walwale matsalan a cikin sauki duk da daga ke har master din kuna kokarin boye muna cewa babu komai a tsakanin ku. Umhumm hannatu ki bari kawai wanan zancen ya wuce nake gani don ina kokarin mantawa da komai kan wanan zancen. Zahra kina ganin cewa ku bata tsakanin ki da master shine mafita a gareki ko me kifa sani irin su master tsada sukeyi yanzu a cikin maza. Ko kin san yawan yan matan school din nan da suke son kasancewa dashi amma yaki bada daman hakan, ni wallahi dama ganin yanayin sa idan badon naga gidansu ba sai nace shi din dan gidan wasu manyan mutane ne sosai a garin nan. To amma kuma nasan shi har irin sana,anshi sai hakan ya fara sani a kwankwanto a kanshi kuma yanzu dai ba wanan nan bama zahra meya kawo matsala a tsakanin ku ? Kamar bansan tana magana ba don hankalina na mayar a wayana ina duba ban dago kai gareta ba naji tace to shike nan yanzun na fahinci irin zaman da mukeyi da juna dake duk da kece kika daukeni hakan. Don ni tsakanina da Allah nake zaman arziki dake ba don wani abuba can zarah amma naga ke ba haka kika daukeni ba ke har yanzu. Nan nake kawo maki korafin yayata dake tasheni ki bani shawara in kuma je inyi amfani da shawaran naki yai min amfani a karshe. Kaina dago na kalleta a cikin yanayin tausayin kaina nace hannatu ba hakana bane matsala aka samu an fadawa Abbana cewa wai soyayya muke da Ahmed shine Abbana yai min iyakan tsayawa dashi. Abba fa har wanan zancen yakai kunnen Abban ku kai mutane basu da kyau yanzu shiyasa wasu ke fadin anbar kiwon dabbobi a yanzu an koma kiwon mutane. Ba wanan ba hannatu Abba har Ahmed din ya kira yai mashi iyaka dani ya kumaci zarafin shi a kaina da wani ido zan kalli Ahmed a yanzu kike gani. Ke kanki Hannatu kinsa Ahmed kadai ke min bayani na fahinci abinda darasi ya kumsa na gane yanzun kuma Abba yaci mashi mutunci kan haka, har yana fadin cewa Ahmed baida asali . What ta fada da dan karfi tana kallona kafin tace min kuma shi Ahmed din yasan da wanan zancen bansan koya fada mashi ba daya kirashi din. Zahra ki bar wanan zancen don Allah mu bari sai mun samu lokaci mu zauna asan yadda za a bullowa lamarin sai dai ban zaton ya fadi hakan a gaban shi Ahmed din ai. Nima shine tsorona don nasan halin Abba zai iya fadin komai ko a gabanshi idan ranshi ya baci tunda acewa Abban soyayya mukeyi nida Ahmed din ba karatu ba. Amma ke baki ganin rashin kyautawan ki ga hakan aisai ya zata kema hakan da Abban yai mashi bai dameki bane kamata yayi mu sameshi mu bashi hakkuri . Kinga a nan zamuji shin Abba ya fada mashi maganganu marasa dadin kamar yadda ya fada maki ni gaskiya kamar hanyar daya dace ke nan mubi nake gani. Hannutu kunyanshi gaba daya nake ji a yanzu bazan boye maki ba kan wanan maganan wallahi nasa cewa ba karamin shakuwa ashe mukayi dashi ba. Don tun wanan ranan wallahi Hannatu na nemi farincikina na rashi a tare dani kullun jin kaina a cikin kinci nake kuma Abba har zai tafi ya kara jadda min cewa duk aka fada mai cewa angani tare dashi zai dauki mumunan mataki a kaina ranan . Wanan yasa nake matukar tsoron fita har mu hadu din dashi wani dan gulma yaje kuma ya fadawa Abba kinsan Abba ba zai raga min ba idan har yaji hakan. Gaskiyane ki dai bari gobe idan nayi tunane kan yadds zamu bullowa zancen sai mu san abin yi don gaskiya ban baki shawaran barin wanan guy din ba zahra. Murmushi nayi tare da fadin wai meyasa mutane ke yawan dauka muna soyayya da Ahmed ne, mutuncine fa kawai a tsakanin mu kema kin sani. . Nikan ban yarda da wanan maganan ba ga kowan ku donko makaho ya laluba yasan gaskiya kedai kawai mubar zancen sai gobe in sha Allahu. Ina hanya komawa gida wayana yayi ringing na mika hannu na dauka daga gefena ya musa ne a layin da murnana na dauki wayan ina gaidashi. Zahran mama ke nan ya fada na lumshe idona don tunawa da wanan sunan da suke kirana dashi shida ya jafar yace yanzu kin zama busy ko neman mutane bakyayi ki gaidasu. No wallahi yaya ba hakana bane yace to ya ne Allah karatune yanzu yai min yawa sam banda lokacin kaina ga komai yanzu. Saina soyayya da yan uwanki dalibai ko Zahra Abba ya kawo min karanki yace kin fara soyayya da wani karamin yaro dan karamin gida a school din ku. Wallahi ya ba hakana bane na fada ina samun wuri na parker motar na kwashe komai daya faru na fada mashi har mutuncin dake tsakanina da Ahmed din da dan sabon da nayi dashi fiye da kowa a school din. Bayan ya gama saurarena yace min kin gane zahra ki janye duk wani alaka tsakanin ki da kowa yanzu kiyi facing din studies din ki kamar yadda Abba yake son kiyi. Shawara sosai ya bani kafin mu kashe waya bayan munyi sallama na tayar da motar na karasa gida ina tunane don ni abubuwan ma sun min yawa a yanzu nake gani. Ranan banyi barcin kirki ba ina faman tunanen maganganun ya musa dana hannatu a raina sai kullawa nake ina walwalewa ni kadai a dakin nawa . Washegari na tashi sukuku dani nagama shirin da zanyi na fice a gidan tunda safe na samu malamin yazo bai shiga ajin ba don haka kusan tare dashi muka shiga. Sai bayan gama lectures din ne hannatu taso muyi maganan jiya din sai ya kasance kaina yana dan sara min muna fita maimakon mu wuce zuwa mosque sai cewa nayi da hannatun kaina ke min ciwo zanje gida insha magani in kwanta. Kallon mamaki take min din muna da lecte karfe biyu da rabi ganin da gaske nake yasa ta kyaleni in tafi din na nufi wurin motana nadan duka ina bude motan naji muryan shi abayana yana fadin 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,, 🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,, 🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA 2️⃣7️⃣ ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,
Chapter 78 · 0% Book details