← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 286

Sashe 7

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

saida ya fifitaki kafin salma a gidan don yanzu ya tuna da ita ya bata zaki nuna bakincikin ki ga hakan. Wanan fadane yasa mama ta danne zuciyar ta wayence da fadin salma aini fushi na dake wai ace mun samu alheri amma kika iya boye min baki fada min sai kawai gani nayi a jikinki ? Murmushi Salman tayi tana fadin haba dai ai da kunya na fadi abu haka kai tsaye ballema ba tabatarda cewa cikine ko ciwo ba a jikina nidai baki kyauta min ba tunda baki bari na nunawa yata ko dana farin ciki ba tun yana ciki yadda kike nunawa diyan ki. Wanan ya jawo ake kirana da diyar mama duk da maman ta kasa yin yadda ummah ke mata dawainiya da nata diyan lokacin haihuwansu don tabar ummah da kula da abinta karshe ma tabi Abba zuwa lagos ita da diyanta sukayi shekaru a can tare saidai idan sunzo yin wani abu ne zasuzo gida cewan mama takai yaranta su sami ilimi ingantattace a lagos din. Yasa na taso a hannun mahaifiyata lokacin dana isa karatu kuma sai mahaifin mu ya dauki ummah ya mayar da ita abuja da zama don a sakani karatu har Allah ya azurta ummah da diya uku bayana lokacin mama tana da haihuwa shidda a duniya. Komawan ummah Abuja yasa ta waye har ta dan shiga karatu a can a wani women center na matan aure da haka itama ummah tayi nata ilimin shiga cikin manyan mata ya tallafawa ummah ta fara kwato incinta a gidan mu yanzu. Duk da dama ta sani tana dai barin su da Allah ne kawai don son da takewa mijin ta shima in a bayan mamane yana nuna mata kulawa irin wanda ya dace. Mama ta raina abuja a lokacin don sun dade basu hadu ba wani sallah da suka hadu a gida taga yadda ummah ta sake a lokaci zama da manyan mata ya juyar da ummah ta zama mace mai yancin kanta sai hankalin mama ya tashi sosai da ganin hakan. Nan ta matsa itama Abuja zata dawo da zama Abba yace karatun yaran fa gasu sunyi nisa ga karatu ba kunya tace su dawo abujan suyi duka a inda nake. Duk kamanin mahaifiyata na kwaso a wurin kama don hakane duk mama ta kalleni takw jin wani iri game dani saidai tana danne zuciyarta ne kawai a zauna lafiya saboda mutane. Gashi kum sunn mahaifiyar Abban mu aka samin yana kirana da mamangida wanda mama bata yarda ba sai ta mayar dani maamah kawai a takaice da sai mutune sun tambaya da suna wa aka saka minne ake kirana da maamah ? Akwai shakuwa na musanman tsakanina da mahaifina da yan uwana maza na sakin mama matan ne dai sam.bamu shiri dasu da ba wanda yasan dalilin hakan. Hakama kakan mu danaci sunanta muna shiri sosai da ita don tun muna abuja zaune nakan zo wurinta hutu a gusau amma tare da mai hidimana. Lokacin dana kare secondary zan fara jami,ane mama ta kawo cewa sai mu koma gida tunda yanzu yara duk sun girma gara dai su koma gida cikin yan uwa su koyi irin al,adan gida acan kuma. Abba yaso ya nuna mata bai yarda da hakan ba amma sai ta nuna mashi cewa yanzun fa yana da tittle a masarautan zamfara zai iya son wani abu a nuna masa ai ba a gida yake zaune ba har iyalinshi da wanan mama taci galabanshi muka dawo zamfara da zama . Don kawai kada yayan ummah su samu karatu ingantattace da zai amfanemu kamar diyanta a nata tunanen ke nan. Sai gashi Allah yaba yan dakin mu baiwa na ilimi don gaba dayan mu na daya muke ci ga jerabawan mu idan munyi exam. Kokai waye idan ka shigo gidan mu ba zaka fahinci akwai wani zama na daban ba a gidan mu zakace zamane mai tsabta a tsakanin don yadda ake nunawa a fili. Har wasu sukanyi kwantace da irin zaman lafiyan da akeyi a gidan mu tsakani mama da ummah d basu nuna haukan kishi akan junan su sai zaman lafiya zallah. Saidai abinda basu sani ba shine irin wanan zaman yafi cutarwa ga irin zaman da ake haukan kishi din afili tsakanin kishiyoyi. Shiyasa zancen hjy karima ya dagawa mama hankali da har yakai ta kasa barci kan wanan maganan a ranan sai faman sake sake take a zuciyarta. Hankali a tashe ta wayi gari don ba karo na farko ke nan ba da take jin irin wanan zancen a bakunan mutane saidai har yakai kawarta tun na kurciya kuma aminiyarta ta fada mata haka a gabanta tasan akwai abinda hjy karima din ta hango game da yarin yar ke nan. Tana idar da sallah ta jawo waya ta danna kiran layin anty Asmau yarta dake aure a Silami wace suke kashewa su bisa tare da ita.
Chapter 7 · 0% Book details