← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 286

Sashe 139

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

na da namiji ki kawar da komai a zuciyar ki kada ki dauka wai kin fishi gata a gidan ku a, a zahra ki kwanta mashi Allah ne ya basu su maza wanan matsayin. Haka karki yarda koda wasa kiyi rauni a wurin girki don ko ba komai kiyi kokari ki girka masa abinci ko wani irine don kinsan an camfa matan yanzu a wurin girki an barsu baya. Don haka yanzu an saka ido an baza a dandana girki aji dama kuma an dauka diyan masu hannu da shuni baku iya aikin komai ba hakane ke yawan jawo matsalan aure da yawa yanzu. Zama na gyara na lumshe idanuna ina jin maganganun hannatu din kamar na wani babba can a kunnuwa kiyi hakkuri wata rana sai labari insha Allahu dan hakin daka raina shike tsonema ido. Shiru nayi sosai ina sauraren ta don nasan iya gaskiyan da duk mai kaunata tsakani da Allah zai fada min ke nan irin wanan zance da hanne ke fada min a yanzu din. Sallama akayi a kofa hakan yasamu katse zancen mu su mommy ne dasu mama Geshuwa yar ummah sukazo don na daukama sun tafine don naji a ranan ne zasu tafi. Saidai basu shigo part din direct ba kamar yadda hannatu tayi su sun wucene part din mutanen gidan suka gaisa dasu tare da masu ya gajiyan taro kafin su fito zuwa nawa part din. Suna shigowa na mike ina gyara mayafin kaina na rungumesu daya bayan daya ina gaidasu suna min ya jiki ya kuma kwana a bakon wurin ? Na danyi murmushi kawai bayan sun dan zauna can mama Geshuwa ta mike mommy ta bita da sauran mutum hudun da suka shigo dukkan su bakine sunzo sha,anin bukin ne lokacin. Kitchen suka shiga sun dan dade a ciki kafin su fito da wasu buhuhuwa suka hada da kayan da sukazo dashi mommy kubura tace oya tashi mu shiga ki kimtsa mu kaiki wurin sararkanki ku gaisa. Don tun jiya suka fara korafin wai ba a kaiki ba kun gausa an basu darajansu gareki Allah yasa naji na dawo ba basu hakkuri kan baki da lafiyane. Ta tafuto hannatu tace zo mu shiga ki tayata kimsatsawa hannatun ta taso muka shiga dakin tare shiga na kwarai na alfarma mommy da hannatu sukai mun. Muka fito gaba dayan mu zuwa part din nasu suna zaune da wasu baki mukayi sallama aka shiga nan suka fara kame kamen gyaran wuri da kyar muka samu inda zamu zauna. Nan aka shiga gaisawa kafin mama Geshuwa tace dasu to inna ga jikanki nan kuma yarki mun kawo maku ita amana don Allah idan tayi ba daidai ba a tsawata mata a sakata a hanyan daya dace. A,a ga uwayen su nan zaune tsohuwa Dije ta fada nikan kakace garesu amma ba laifi ai wanda yace yanayi da danka ya gama maka komai a duniya. Zahra ki saki jiki nan kamar gida kikazo ga uwar mijin ki nan ga kannensa muyi zaman mu lafiya keji kaina a duke yake kasa kuma na dunkule a tsakankanin gwiwana sai hawaye ke zubo min lokacin. Wanda ba zan iya fadin kona meye ba gadai hawayen ina zubarwa zan baka tausayi sosai a yadda nake zaune can sai naji muryan mahaifiyarshi na fadin. To kesan dai muna da yara mata a gidan nan dole sai kin hada da hakkuri wurin zama dasu mommy ce ta katse ta da fadin ai ko gida tana da kanne itama . Iyaka dai kowa ya tsaya matsayin shi su bata girmanta na matar wansu itama haka ta dubesu a matsayin kannenta saikuyi zaman ku lafiya dama hakane. Me zai kaisu wurinta in ba sa ido tana gefenta suna nasu kudai Allah ya bamu zaman lafiya ya kawo kazantar daki da wuri tsohuwa dije ta fada kamar tana katse zancen da aka dauko din lokacin. Nan dai naji mama Geshuwa tace ga dan abinda ya samu nan daga waje na uwayen miji kuyi hakkuri dashi hakana gaba dayansu suka juya suna kallon kayan da aketa shigowa dashi part din. Daga nan naji mommy ta dagoni muka mike zuwa nawa part din mommy kamar tana jurane mu shige naji tana fadin. Zahra sai kin jajirce a wanan gidan kada ki kuskura ki koyi wanan halin nasu ko kusa gida da kazanta haka kamar ba mata a cikinsa harda yaran mata amma kaya haka gajal ko ina., Ai ba zata koyi wanan halin nasu ba tunda bata taso a cikinshi saidai idan taso amma yaro na tashi wurin sallama bai koyi tsabta ba. Wace saboda tsabatanta har muna tsamanin shiya hanata samun haihuwa da wuri maman Zahra akwai tsabta kan gaskiya don komai nata tsab yake. Mommy ta amsawa mama Geshuwa din data fadi hakan kafin su dawo kuma kaina suna fadin yanzu idan mun tafi ki tashi ki dora girki ga kawarki nan ta kama maki ku hada abinda zakuci. Hannatu ta amsa da fadlin dama zamu dora ke nan kuka shigo hakan nada kyau gaskiya kada ki yarda kiso jikinkin ki ki jajirce sosai kinji Allah yaiwa auren ki albarka aka amsa da amin Na kuma ji wanan uwar mijin naki na wani zance kan yayanta kada ki yarda ki basu fuska da zasu raina ki ki tsara girman ki bawai sai kin sake masu yadda raini zai shiga ba don su din kinga kamar jahilai suke. Don in raini ya shiga tsakanin ku daga baya ko kinso gyara hakan ba zai yuyu ba shi kuma mijinki ba zaiki yan uwanshu ba ya goyi bayan ki don haka kisan yadda zaki zauna da kowansu. Sun kai wani lokaci kafin suyi min sallama su tafi muka mike muka gyara gidan nida hannatu muka dora girki kamar yadda sukace nayi din . Sai yamma lis hannatu ta tafi nima nayi wanka na canza kayan jikina zuwa wani dogon riga mai laushi a jikina na saka kamshi a jikina da dakin na zauna ina jiran a tayar da sallah.
Chapter 139 · 0% Book details