← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 286

Sashe 13

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ganin wanda ya shigo sai hangoshi tayi yana shiga dakin nasa a lokacin tayi. Shiru shiru bata jishi ba yasa ta mikewa zuwa dakin daga kofa ta tsaya tana magana Amadi lafiya yau ka dawo haka da wuri gida nayi jiran ka shigo banga shigowanka ba. Jin shirun da tayine yasa ta daga tsohon labulen dake kofan dakin nasa kwance yake saman tsohon katifan shi dake yashe kasan dakin ya kwanta yayi rubda ciki. Ikon Allah yau Amadi kaine da wanan irin kwanciyan da ba, a son ga musulmi ya kwanta ya kifa ciki bansan ka da irin wanan kwancin ba haka ? Jin shiru baiko motsaba yasata kutsa kai cikin dakim gabaki daya Amadi fa wai lafiya kake yau din ko wani abin ke samun kane ? Hannu ta mika ta dafo kafadan shi wani zafi ya daki hannun nata da sauri ta jaye hannunta saman jikinshi da sauri tana irin salatin su na mutanen da sai ta dauko wanan kafin ta aje ta dauko wani ta dora a kai. Amadi jikin ne yayi tsanani haka ka dawo baka fada min ba yanzu ina amfanin kwanci da ciwo haka a cikin daki ni Dije ta ina zan soma a garin nan. Allah kazama muna gata ya Allah ka dubemu mun tuba Allah ta fada tana kokarin kara taba jinkin nasa taji saidai tana kai hannu taji kamar kara zafi jikin nasa yayi a lokacin kuma. Hankali tashe tayo waje zuwa dakinta tana jawo gyalenta na sallah ta dora saman kanta ta nufi waje gidan makwabtansu ta nufa saidai ba taimako don maigidan bayanan don haka ta fito daga gidan. Malam Tanimu ta hango kofan gidansa wurin sana,anshi ya dan rarafo yasha iska don bai gama farfadowa daga tausan da gina yayimas bako a lokacin. Ganin ta a hargitse yake tambaya Dije mai kamu ince ko lafiya ina fa lafiya malam Tanimu jikana ya dawo min a cikin wani yanayi na rashin lafiya yana kwance a dakinshi rai a hannun Allah. Subbahanallahi ya fada yaba yunkura saidai gefen kafadab shi da gina ya taushe yayi tsami a lokacin yasa ya koma da sauri yana yamotse fuskanshi kafin yace meke damun shine ? Dama tun kan ya fita yake fadin sanyi yakeji da kuma nauyin jiki na jiya kuma yace kai ke dan sara mai haka dai ya fita yau din zuwa daukan karatun shi na boko sa yakeyi. Yanzu shine nace bari nazo ko za a taimaka min ko wani shawara na samu ga mutane indai da kai barin bashi wani magani ya shaka in,sha Allahu zai samu lafiya indai ya shaka wanan din. Kinsa sana,ar tamu dole saida tambaye tambaye don haka na aje wanan danaji ba daidai sai nadan yi amfani dashi naji wasai. Mikewa yayi da kyat ya shiga gida ya dan dauki lokaci kafin ya fito sai gashi ya fito da kullin dan bakin leda a hannunshi yana fadin ina ai Amadi yaron kirkine bada kamar shi a unguwar nan baki daya . Ki kai mashi wanan insha Allahu yana amfani dashi kome ke damunshi da yarda Allah zai sake indai yayi amfani da wanan dai ya aje sauran a wurinshi. Godiya sosai Dije ta fara yi mashi kafin ta dingisa kafantal taja zuwa gida yana kwance yadda ta barshi ta zaunava kusa dashi tana bude ledan kafin ta debo ta turmuza bashi a hanci ta koma gefe ta zauna ta kafa mai idanu tana tunane a zuciyar na jikan nata. Kafin dan wani lokaci taji ya saki wani irin atishawa da karfi lokaci guda tana zaune saida ta zabura daga inda take zaunen tana ambatan sunnan shi take fadin Amadi sannu sannu kaji Amadi. Wani atishawan ya kara sakewa har yana dan dagowa daga kwancen da yake dije sai fadi take Alhamdullilahi barka Amadi sannu kaji Allah ya yaye sai kuma tasa kuka lokaci guda. A hankali ya fara bude idonshi yana ganin dishi dishi a dakin kafin ya sauke kallonshi kan Dijen yana fadin Dije lafiya dakyat yake wanan maganan lokacin. Sannu Amadi ta fada a cikin muryan kuka tana share hawaye da gefen gyalen ta tace yaya jikin hankalina ya daga sosai banda dabara shine na tafi wajen malam Tanimu yabani wanan na shaka ma tana nuna mai kullin dake hannunta din. Kallon maganin yayi a hannunta kafin ya yunkura da niyar tashi jiri ya mai dashi ya kwanta yana lumshe idanunshi a hankali tare da jin wani iri a idonshi ya mayar ya rufe. Kaci wani abin kuwa yau ta tambayeshi ya dan girgiza mata kai yana gyara kwanciya ta mike ta fice daga dakin kwano ta dauka ta fice daga gidan . Wurin masu sayar da abinci layin ta nufa ta sayo shinkafa da taliya da ganye a sama ta kawo mashi dakyat ya tashi ya fita ya wanko bakin shi ya dawo ya ya zauna ta kara tura mai abincin gaban shi . Saida ya dan samu natsuwa ya bude kwanon shinkafan ya kalla yasan saye tayi don basu da halin dafa wanan a gidansu tausayin kakan yaji ya kara shigan shi lokaci guda yana tausayawa tsohowan kan irin rayuwan da suke fuskanta din. Mikewa tayi ta fice daga dakin ruwan zafi ta hada mai ta kai mai bandaki ta dawo tana ka gama tashi ka watsa ruwa a jikin ka ko zakaji karfin jikim naka ko ? Sai kuma takai kallo ga kwanon dake rufe har kaci abincin ke nan ta tambaya tana kallon fuskanshi ba zan iya cin wanan din ba dije ya fada ya kokarin mikewa ta sakw fadin me zakaci to ? Banjin cin komai a yanzu ya fada tare da mikewa da karfi ya barta dakin tsaye tana mamakin shi dama ita din da yunwa tare da marmarin shinkafan take saidai babu halin hakan a gareta. Yasa ta daukan kwanan zuwa waje ta zauna ta faraci tana lumshe idanu wani gefe kuma tana jin zafin kudin data fitar ta sayo wanan abincin gashi yanzu baici ba ta bata kudin a banza. Shiko yaki cine don yasan itama tana so ko kan ya fito har ta kusa gamawa da abincin ya fito daga bandakin wankan maza yayi na watsawa aji iska a jiki kawai a lokacin. Alwala ya zauna yayi don ya rama sallolin dake kanshi yana kallon dijen a fakaice tare da girgiza kanshi ya mike zuwa daki ya gabatar da sallah bai sake fitowa ba sai washegari.
Chapter 13 · 0% Book details