Sashe 92
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
malam tanimu da fitosanshi ke nan a lokacin take labarta mashi rashin dawowan Ahmed din gida da sunan zai shiga kauye ya sayo hatsi kamar yadda ya fada mata din. Dijeki kwatar da hankalinki duk inda yake in sha Allahu Amadi yana lafiya don ni jikina bai bani cewa wani abu ya sameshi a can ba kinsan tafiya yadda yake. Mai yuyuwa wanan karon yayi nisane da gida sosai don in kin kula abinci a yanzu yayi nisa sosai ba ako ina ake samun shi ba haka kai tsaye. Malam Tanimu Amadi bai tafiya irin haka yakan danjene ya dawo gida don haka donle in damu da rashin dawoawan shi haka yaufa kwana biyu ake nema ga tafiyan nasa. Namiji nefa Dije don Allah kijeki ki kwantar da hankalinki insha Allahu yana nan lafiya ba abinda ya sameshi a can saidai muyi adduan Allah ya dawo dashi lafiya yanzu kan. Wanan zancen nasu da malam tanimu yasa ta danji hankalinta ya dan kwanta ta ta koma gida da dan kwarin gwiwa ba kamar yadda ta fito ba da farko. Kowa ya fito a motan ga yamma da yayi sosai a lokacin don har wasu sun fara shirin alwala shima fita yayi da dan jakkarshi na ratayawa kalan ta maza a kafadan shi. Wurin wani dan Union ya nufa da yake gani dattijone a wurin yace don Allah malam tambaya nakeyi mutumin ya juyo don jin hausan shi yana kallon shi. Yake fadin mabila nake son zuwa don Allah ko za a samu motan da zata tashi a yanzu zuwa can ? Malam da yamman nan kuwa gaskiya yana da wuya a samu motan da zai tashi yanzu zuwa can don yanayi hanyan a yanzu. Amma ka dakata mu gani nan zuwa dan anjima amma da zaka bi shawarana ka bari sai zuwa safe kabi motan farko ka wuce kasan yanayin boko haram din nan da muke ciki ya fara kawo muna nan. Jin hakan yasa jikin Amadi din yai sanyi shi yanzu idan yace zai kwana a ina zai kwana ke nan don haka bashi da zabi in mota ta samu zai dauki kaddara hakana yabi hanya Allah ya tsaresu. Kaje can ka zauna mutumin ya fada yana nuna mashi wani benci a wurin Amadin yace bari nayi sallah a can na fito zan dawo yanzu in sha Allahu. Jeka Allah yasa mu samu motan mutumin ya kara fadi shi kuwa Amadin ya nufi wajen da yaga wasu na zuwa don yin ibada. Har ya idar ya fito ya dawo wurin ba alaman mota har lokacin yaja ya zauna a nan inda mutumin ya nuna mashi da farko kafin yaje sallah. Bai dade da zama wurin ba wata mota ta shigo cikin tashan yaji sunawa drivern kirari ana gaisawa dashi wanan dattijon yaje gurin shi shima suka gaisa. Daga can yaga mutumin yana masa hannu ya taso da sauri zuwa wurin su ya iso mutumin ke fadin kayi sa,a ga mota nan har gaba da mambila ya nufa shi sai su sauke ka su tafi. Kudin mota dubu biyu da dari biyar ne ka kawo a bashi dama mutum biyu yake nema ya cika kuma ya samu don ga wani dattijo can shima gembu zai tafi yace. Hannu ya saka a cikin aljihun shi ya ciro kudin ya mikawa mutumin saura dari biyu ya sake mika yace babba ga wanan kasha ruwa. Godiya sosai mutumin yai mashi don shi tausayi dattijon ya bashi a rayuwa yafi tsanan wanan aikin na Union din tasha sai yake ganin shi ga aikin malalatane. Sai kaga mutum har mutum.daya dace ace yana aikin karfi amma ya buge ga yin kamisho din mota ana bashi taro sisi zuciyarshi ta kara mutuwa . Wanan din ma ya ganshi ya dan tsufane yasa yaji tausayin shi haka kuma ya hango idon mutunci ga mutumin tun shigowan su cikin tashan dama shiyasa ya nufi wurin shi. Ba bata lokaci bayan shiganshi motar yana rugume da yar jakan shi motan ta tashi suna daga masu hannu da alama wanan drivern sananene sosai a cikkn tashan yola din.