← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 220 OF 286

Sashe 220

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suwaiba wacece kuma suwaiba dije suwaiba da daka sani yar gidan sidi wani kallo yaiwa dijen na baki san ma me kike fadi ba tsohuwa kafin ya mike zuwa hanyar fita daga gidan. Bata kyaleshi ba ita a zatonta sakina zaije yayi lokacin ta biyoshi tana fadin nace kada ka aikata hakan akan yar mutane jjn hakan yasa yaja ya tsaya ya juyo yana fadin Dije koma ciki ni abin miya zanje in sawo mata yanzu na manta bansayoba na dawo gida. Ja,iri ni har ka daga min hankali ga banza yayi murmushi tare da fadin ko kare ya cijeni aiba zan saki zahra ba don ta gama min komai a rayuwana da inna nake wanan zancen tunda muradinta ke nan a kanta kuma na tabbatar da zata iya aiwatar da hakan akan ka. Ashirme ke nan Dije ki koma gida fita zanyi yanzu saina dawo zan shigo muyi maganan dake ya fada yana tare abin hawa ya wuce ya barta tsaye tana zancen zuci. Allah ya dorawa mata son jikan nata fiye ma da yayan nata biyu data haifa don hakane bata son abinda ya samu rayuwanshi ko kadan kalaman yarta Rashida akan jikan nata yana daga mata hankali shiyasa a yanzu bata dagawa yarta kafa a zancen jikan nata ko kadan. Lokacin ina daki bansan duk abin dake gudana ba don wayan da ummah ta bugo min a lokacin ya dauke min hankali inda take fadin bayan mun gaisa ashe mijinki ya dawone shine baki sanar muna ba. Ke wani irin sakarcine gareki wai mahmah in ba don yazo gidan nan ba ashe da ba zaki kira ki fada muna ba ke nan wallah ummah yanzu nake shirin kiranku in fada maki. Ta katseni da tsawa tana fadin rufe min baki shasha ga dai Tani nan zuwa ta kawo maki sako saura kada kiyi amfani dashi idan ankawo maki din ko wurin sakarci har ki bari ya gani. Fuska na bata duk da ummah bata ganina don dajin hakan nasan ko sakon meye a lokacin kina jina ta fada na amsa a sanyaye da inaji ummah . Tace kuma mijjnki yazo dan albarka ya kawowa yaran nan tsaraba harda muma dazun da rana nace ni bani gida yanzu na dawo aiya fada kina makaranta yanzu ke don baki da hankali har kika fita zuwa school yau mijinki yaje ya dade haka bai kasan ya dawo kice kinga wurin fita ? Shiru nayi saida tagama fadan tayi min sallama na amsa muka kashe wayan ina sauke ajiyan zuciya a daidai lokacin da Tani mai aikin mu ta shigo gidan da abu dunkule a cikin hijjabinta. Saida muka gaisa tayi min barka da dawowanshi ta fara min bayani kuma ta umurceni da in tashi in boye kafin ya shigo hakan nayi a gabanta saida na fitone take fadin tsaraba haka hardasu mama aina zata ba zata karba da aka kai mata sakon sai gashi ta karbe harda godiya. Ban kaiga magana ba naji shigowanshi ya dawo hakan yasa mukayi sallama a gurguje ta fito tana gaisawa dashi cikin dan kame kame ya amsa a cikin nuna kulawa a gareta ta tafi ina fadin tayi muna godiya wurin ummah. Kodana juyo na dawo na samu ya shiga dakin yana tsaye gaban kayan dake cikin leda ina shiga yakai zaune yana jawo ledan tare da fadin me muka samu kuma wurin ummah haka harda wahalan taso da Tani tayi. Ba kaje gidan gaida itaba shine ta hauni da fada wai ban fada masu cewa zaka dawo bashine take tayi min fada kuma ta aiko Tani da wanan din nima bansan ko meye a cikinsa ba don ban bude ba. Allah sarki uwata ninasan cewa a yanzu ummah tafi sona akanki ai don wallahi har na dawo ta kan kirani a kai akai taji lafiyata keko kina can kina kayan fushi dani. Aina sani tunda naje gaisheta ta hauni da fada wai na fito baka gari dole tasa na dawo gidan nan ban shirya ba a ranan kai amma ummah tayi min daidai wallahi haka nake fata dama in samun uwa mai mutunci da sanin ciwon kai. Kinga nafi dace da sa,a don ni nawa uwar matan tana sona keko uwar mijin ki gakunan kullun sai anjiku a gidan nan kuna rigima da ita jin hakan na danji sanyi a raina nace. Ki inna ai zata daina watarana kawai dai tana amfani da zugin wasune tana ganin laifina a yanzu amma wataran zata gane gaskiyan hakan insha Allahu . Gyara zama naga yayi yana lumshe idanunshi can ya bude yana fadin naji dadi da har kika fahinci hakan zahra ni kaina yanzu nagane cewa tana amfanine da shawaran wasu a kan ai. Ledan hannunshi na kalla daya bude kai wanda bakatsina ta haifa a duniya taji dadin ta haka idan bakatsine mahaifin ka ka more uba a wajen kara da mutunci ga ilimin sanin duniya a tare dasu. Don wallahi yana bude ledan farko kifine aka gyara anyi mai gyara na alfarma anyi gunduwa gunduwa dashi an soya mai yawa sosai a ledan haka leda na biyu alkakine ya soyu yaji shuga sosai manyan dauri. Sai na ukkun dambun namane shi din mai yawa sai yaji da kuma naman soyayye kule a wani ledan shima shiru mukayi muna kallon kayan kafin yace ashe yau ba girki ke nan gareki don wanan ya isa muci musha ruwa mu kwanta. Bari na samo wuri na juye sai a dibawa su dije suma su dana da sauri yace ina ni aka kawowa da zaki fara kyautar min da abu yana kokarin jaye ledojin a gabanshi. Aiko bakaba kowa ba ka bari a dibawa dije da inna ko na fada ina fita dana kawo wajen shi da kanshi ya zuba lokacin nake fadin ashe ka sayo kayan miyane dama ? Yace eh shina koma na saya dana fita din nan bayan mun gama fada da inna da sauri nace fada da inna kuma ya karbi robobin a hannuna yana zuba alkaki a ciki yake fadin mun kwasa mana kan nayi mata magana ta bar fada da Dije don Allah . Naga ya zuba komai a ko wani ruban ina tsaye ina kallinshi a fili amma a zuciyana fadi nakeyi cewa su wanan ahalin haka suke kowa ya dinga fada da mahaifinshi . Magana nakeyi fa na dago na kalleshi yace me kike tunane hakan wai nace humm,umm mamaki nakeyi yadda harda kaima kake rufe ido kuyi ba dadi da inna haka. Innace duk ta kawo wanan abinda kike tunane din a yanzu don gaba daya yanzu ta juye ta canza halin ta ya fada ya mike ya fice da kayan a hannunshi na bishi da kallo a raina ina fadin mafarin yaja min zagi gun inna din kuma ke nan tace har aikenshi nakeyi ya kai min abu kamar yarona. Bai fadawa kowa shigowan shi kasan ba sai ganin shi kwatsam duka iyayyen nasa sukayi a lokacin falo ya zube inda ya samu mahaifin nasa yana shan, iska suka tareshi a cikin murna tare da kallon yadda dan nasu ya koma yanzu. Ga dai girma yazo mai ga kuma wayewa son kana ganinsa kaga mazaunin turai ba zaka taba zaton shi din tsatson fulani ba haka uban ya daure zuciyar shi ya nuna farin ciki da zuwan nasa. Hjy murja da bata san da zuwanshi ba shigo falon tayi wurin maigidan don ta tambayeshi abu shine ta samu sunyi bako a gidan wanda rabonta dashi tun tsawon wani lokaci mai tsawo sosai. Duk da baigai da ita ba amma haka ta daure tana fasin wanake gani kamar yasir a gidan nan ya dago kai yai mata kallo guda ya kawar alamun shi bai santa ba a lokacin. Mahaifin nasu yace step mum cefa hjy murja ko baka ganeta bane yace OK itace abinda kawai ya fada ke nan yaci gaba da magana da uban nasa ya fita batunta. Haka bai hana data gama abinci ta sako masa nasa ban ba amma sai cewa hjy yabi tayi da yar aikin ta mayar ta fadawa murja cewa danta yafi karfin ta mallakeshi ta dai tsaya ga ubanshi shidata samu. Sako yazo mata kuwa murmushi tayi tace aiko nayi babban kamu indai na kama uban wake ta yaro ga babba a hannuna don dole dai ace min matar ubanshi ai. Ran hjy yabi ya baci sosai da martanin hjy murja din don haka takai karanta tana haki ko alokacin suna zaune da yaron suna tataunawa akan zaman shi turai. A gaba dan ya aika aka kira hju murja din tazo yake tambayanta abinda yasa ta aikowa hjy yabi da wanan maganan dan murmushi ta sake kafin ta juya ta kalli hjy yabi din tace. Ba aiko mata da bakar magana nayi ba amsa na bayar a fada mata na sakon data ban nan ta kwashe komai ta mayarwa mijin nasu wanan shine farkon abinda dan nata ya fara cin karo dashi don daddy bai bata gaskiya ba. Shima dan ya nuna yana bayan mahaifiyar shi don a wajen ya bude baki yace yes uwarshi nada gaskiya aiba ita bace ya kamata ta bashi abinci. Jin hakan yasa Alh fadin kana nufin ka goyi bayan mahaifiyar kada a zauna lafiya ke nan a gidan nan yace ba haka yake nufi ba idan zasu zauna lafiya duk daya a wurin kawai dai mahaifiyar shice mahaifiyar shi kowa yasani ai. Alh ya gano tsegerancin da dan nasa ke ji dashi a lokacin yasa ya kyaleshi don daga shi har uwar ya shirya yin maganin su nan gaba kadan kuma a yanzu a shirye yake da duk abinda sukazo mai dashi. Tun ranan kuma bai kara saka dan a idonshi ba haka kuma kwana biyu da zuwanshi itama salima tazo garin suka hade hakan ya kara tabbatar mashi da zuwan nasu yana da wata manufa. Shi kuma sanin cewa dan nasa ko a turai dan dabane don irin abokan da yake yawo dasu a can yasa ya karawa gidanshi security bada sanin su ba. Kallon kayan cikin mamaki mama tayi tare da tambaya tana kallon yayan nata dake zaune dukkansu biyu lokacin da aka kawo kayan a part din ta tace . Dama mijjn Zahra ya tafi turaine ban sani ba yaushe har yaje
Chapter 220 · 0% Book details