Sashe 279
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
dakin kuma ba wani gyara amma na kwashe kayan daya cire na zuba a inda muke tara kayan dauda na juya zan fita dakin ya fito yana fadin ki shirya Amir muje jam,i nan kasan mu kadan na amsa da to na fita alwala nayiwa yaron da kaina na saka mashi jallabiya da hula fara uban ya fito ya daukeshi suka fita sun dade a can din nasan isha,i suka jira koda suka dawo yaron yayi barci a lokacin. Nan falo ya shimfideshi shima ya zauna jin ya shigo yasa dije fitowa suka gaisa har lokacin tana masa korafin akan zancen Asmau yace ta barta dashi ai batace ita fitsarara bace ai zasu hadu dashi din. Mama jummai ta gama abinci ta jera muna na fito ina gabatar mashi da abincin ya amsa da gani tafe dama a nan ai ta aje muna aci gaba daya barin dauko mana na fada na kama kwaso kayan yace shi wanan da yayi barci yaya ke nan kuma ? Zai tashi yaci ai nasani barin gama inzo na fada nabada baya naji yana fadin wai dije kinsan tumfafiya ya kara fitowa gidan nan kuma ? Ikon Allah a gidan nan kuma tumfafiya uwar kwankwanmai tumfafiya baki fita a wurin banza dibanki sai da sallama wanan kuma wani baiwane na ubangiji gareku. Tsaya nayi na juyo ina kallonshi cikin mamaki nace wai a gidan nan tumfafiyan ya fito kuma yace nan fa can ta waje idan ka shigo get yana nan a barin gabas ya fito. Zaune nakai ina fadin wai kasan master ina yawan mafalki da wanan itacen kuwa wallahi yana da wuyane ayi sati daya banyi mafalki dashi ba har uwar garke muyi hira sosai kuma da ita kamar mutum. Murmushi yayi yana dan kawar da kai don yaga alaman tsoro a fuskana nace wallahi Allah ko jiyan nan take fada min wai inna zata zo da fada gidan mu Amma mu barta da dije kawai . Naji daje tace ni kubura har dani take ambatowa ya kwashe da dariya yana fadin dije in uwar garke bata ambaceki ba ta ambaci wa abokiyar zaman kice kuma abokiyar fadan ki ko kin mata lokacin data saki zaman daki. Duk aka kwashe da dariya tace bari akuyan nan ai ta gwada min boni a gidan nan Allah dai ya rabani da ita lafiya batayi min illa ba ko sanadin kafan nan nawa fa itace tayi min sanadin shi. Ta bangaje sai yanzu nake tunawa akan nayiwa Amadi fada harda duka ranan ina shigowa tayi baya baya ta kwasheni ta zubar kasa na fadi a baude kashina ya amsa tun lokacin nake fama da kafan nan a rayuwata. Muka kwashe da dariya har Aisha da ta fito ina dariyan nake fadin yanzu nake batun na kiraki muci abinci muka tsaya hiran uwar garke. Amma dije baki fada min ba cewa kikayi kawai an kin fadi kinyi tarmashe tace ina zan fadi ta kara min wani sanadin aidai gashi mun rabu lafiya da ita yanzu ko ? Allah yasa kun rabu din don al,amarin wanan akuyan ai sai ita ni kawai zuciyana na ban cewa wallahi zata dawo wata rana kuma ku bari ku gani din Allah dai ya sauwaka kawai. Aisha ke dube duben tsoro nace aiko gatama tazo duk suka duba a tsorace muka kwashe da dariya munci abinci mun gama nida Aisha muka kwashe kayan don su mama jummai su huta don mutanene suma a ka zauna zaman hira ana rage dare dijece ta fara tashi taje ta kwanta Aisha ta mike ta kwashi yaran zuwa dakina don nan suke kwana tare dasu da master yayi tafiyane nake kwana dasu daki daya a kasa don nafi jin dadin kwanci kasa din. Ranan kuma yana gari yasa zata kwana dasu ita kadai gaskiya Aisha ta dabance ita don halinsu daya da master basu shiga abinda ba a sakasu ciki ba . Washe gari kuma tunda nayi sallah na koma na kwanta don gajiya shima daya dawo jam,i yabi sahuna muka kwanta barcin safe don ana sanyi a lokacin can cikin barci nake jin ana nocking din kofa na bude idona shi naji yana fadin waye muryan Aishace take fadin su innace sukazo yaya tashe in tasheku. Naji yace inna yana daukan wayan shi yana duban lokaci yace basuga hadarin nan bane da wanan sanyin da akeyi suka fito da safen nan haka tashi nayi na zauna ina tunanen meya kawo inna kuma amsa zuciyata ta bani ai gidan dantane . Saida ya shiga bandaki ya kewa ya fito ya zura riganshi dogo a jikinshi ya bude kofan ya fita har lokacin ina zaune jikina ya mutu a inda nake zaune kafin na zuro kafana zan sauko a gadon . Budan kofan da yayi ne na fara jiyo muryan inna sama sama a cikin fada tana maganava hasale nace to fa yau kuma meya faru inna tazo haka cikin fada tunda safen nan haka ? Ban fito ba saida na shiga nayi brush na kewa na fito ina saye da rigan barci na saka hula da cusha gashina a cikin hulan sai zanin atamfa danayi sallah na daure saman rigan barcin. Na bude kofa na fito lokacin na fara jin muryan inna da kyau tana fadin ni gani shasha watau na haifawa wasu da suna cin dadin su suda sukai kudin nasu dawa sukaci ? Don Allah dai inna ki bar fadin hakan ba kyau gaskiya Aisha ce ke fadin hakan cikin damuwa tana tausa muryanta ga mahaifiyan nasu tace rufa min baki kada yanzu in saba maki gidan nan . Karya nafada basu yakewa karyan arziki ba saiko umma dake tare dasu ina jin haka na dan ja natsaya taci gaba da fadin banda umma yanzu wakecin arzikin shi sai ita saiko yan uwan matarshi. Saukin abindai ba fakiriya ya daukoni gidan muba inna inma naci arzikin shi shima daku kunci nawa a baya jin hakan yasa ta juyo tana kallona sai kallon ya koma mata biyu don wai zuwan ranan batama ga ciki a jikina ba haka tsoho sai yanzu din dana fito da zani daure sama rigata tagane. Oh lalai kiyi abinki issasa don yanzu kan mage yaji magi to sai ki sauke rashin kunyar nan naki garesu don ni ban neman komai a wurin uban yarinya. Ai dole yanzu kiga kin isa tunda kina cika masa gida da yayan kwara ba dadin gani ba dole shiko idonsa ya rufe ba ganin kamar gwanewa ne hakan kike nai bai san sallon yaudara kuke masa ba. Hannu master ya daga min ya juya gareta yana fadin lafiya haka inna kika fito gida da wanan uban hadarin da aka hada zuwa gidan nan fada wani abu matata tayi maki ko Dije ko Aisha dake nan ? Ko wanine ya je ya fada maki wani abin don ni ban garin jiya na dawo da yamma na kuma fada maki zanyi tafiya kafin in tafi. Kai rabani da dadin bakin banza sai wani yaje ya fada min zan sani tunda ka daukeni wawuya yar kauye ban san abinda akeyi ba kai shike nan na haifawa duniya kai saidai wasu suci gajiyan ka bani ba. Mena rageki dashi duniya kudin abinci ina turuwa kudin ruwa ina turowa kudin kashi ina turo maki naki dana yayanki ko wani karshen wata hakama sutura inna ki fadi a ina na rageki harda kudin goro kika lissafa min kuma ina baki kince Asmau aure nama kayan daki bayan haka na turo maki da milayan biyu don sha,anin buki a ina na rageki inna ? Amma inna ai kince rabin miliyan ya baki lokacin shegiya yar iska ki rufa muna baki duk waya turota yanzu bake ba ke har kin isa in tura masu aiki gida aimin aiki ki koresu ? Yau din nan basai gobe ba ki tattara ki bar min gidana ba sai gobe ba ki koma gidan ubanki Asmau na gaji nagaji hakana wallahi, , , ,