← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 286 OF 286

Sashe 286

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

a can ai so ba ruwan ku dana nan nagani amma dai bari a dan debo maku wanda ya saura don ni ban ajeba a nan din duk yan buki sunci abinsu. Bansa metaje ta fada ba sai ga inna din ta dako muna sammako a gida fitinanta ya tayar damu da cin mutunci harda zagin iyayyena tana kiran yan uwana da mayuwanta . Hakan ya fito dasu Salima daga dakunan su har hjy murja aka taru ana kallonta ganin bakin fuska baisa ta fasa ba saida Dije tace ke kan yar da wanan halin naki Rashida. A gaban yan uwan haihuwan danki kike tonawa kanki asiri kin dauka wani kike tozartawa a hakan suna maki kallon mahaukaciya a hakan. Lokacin ta fara bin yan fararen yan matan uku da kallo kafin ta juyo kan ita hjy murja din sai taga ta muzanta a gaban su lokacin hjy murja ta fara magana tana fadin. Wanan gaskiya baidace ba ace ana fadan nama a gidan dan alhaji dake da dukiya shanu kamar ya kashesu wanan gaskiya abin kunyane a wurin mu fulani idan sunji. Kame kame ta farayi tana fadin na fada maku fadan nama nazo nazone don wanan yar rainin wayau data algaje min da tana kokarin maidashi danta don samu wurin. Guntun tsoki Salima taja ta juya zuwa ciki haka suka barta nan da guda guda niko ko lekowa banyi ba don nasan suna gidan a lokacin . Kwanan su uku damu suka juya abinsu zuwa Abuja suka barmu nan gusau din nima dana kwana biyu yace mu shirya mu koma Abuja da yara don gidan na can yagi girman biyun wanan da muke ciki. Nasan dai bai wuce umurni Abbansa ne hakan don abinda inna tayi a gaban iyalinshi suka gani zaisa yai masa magana a kaina da zamu tafi na roki Abba da har ya koma nema Abuja din kan zanzo dasu ummah tunda yara suna hutu. Hakan ya bani daman komawa da Ummah Abuja daga lokacin don master yace a nan su kannena zasu tsaya suyi karatunsu shi zai dauki dawainityar komai yanzu. Wanan ya jawo fitina a gidan mu sosai don mama tayi fitina tayi korafi amma Abba ya nuna shi ba ruwansa in itama zata dawo nan din ne ta zauna aisai ta dawo. Taga ba zata iya barin yaranta dake aure a zamfara ba ta koma Abuja da zama zasu sha wahala idan bata kusa dole mama ta hakkura ta zauna a nan zamfara don kawai duniya ta juya mata a yazun . Ta haka rami ya fada da ita a lokacin tayi data sanin dawowa arewa datasa Abba yayi damu dasu gaba daya ta manta cewa haka kaddaran yake muna a rubuce. Inna ko wanan rashin mutuncin da tayi a gaban iyalin Abba ya zama mata data sani a yanzu don dan abinda take samu yanzu da kyat na iya shawo kan master ga kuma Asmau din mijin yaki. Aishane zuwan mu Abujan nan ta hadu da wani suka shirya akai masu aure kafin mu dawo din nan bayan auren ta da wata uku muka bar Nigeria da yaran mu uku muka dawo nan inda master sai ci gaba na alheri ke samunshi a yanzu. Wanan shine labarin tumfafiya uwar kwankwamai don na yarda master lamarin shi a tumfafiya sirin nasa yake mu daraja duk wani abin alheri da muke ganin yana bibiyan rayuwan mu wani lokacin alherine a garemu ma,assalam nagode daga zahra US yar , , , , , , , state.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

YA ALLAH KABA BABY ZAHRA LAFIYA YASA AIKIN NAN DA ZA AI MATA GOBE NA KODA YAZAMA SILLAR SAMUN SAUKINTA YASA YAR TA MORIYACE AMIN NA ALLAH SU TAYAMU DA ADDU,A GOBE NE ZA A SHIGA DA ITA AIKIN ALLAH UBANGIJI YASA AYI CIKIN NASARA AMIN MUN GODE .
SAI MUN HADU LITTAFIN MAI ZUWA MAI SUNA (KARAN DAFI)
Chapter 286 · 0% Book details