Sashe 30
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallama nayi part din suna zaune falo sai mamace ke dakinta gaidasu nayi na nufi dakin mama don lokacin banda shamakin shiga dakjn nata don da suke lagos nakan je hutu daga Abuja. Bata nuna mjn banbaci ga komai duk yadda yaranta keyi haka nake mata lokacin wanan ya jawo shakuwa mai yawa a tsakanin mu duk faruwan hakan ya samo asaline bayan dawowan mu gida gusau da mukayi ana zaune wuri daya. Nakai kofan naji muryan mama na fadin ain fada maki Saratu da cewa yarta idan banyi da gaske ba yaron nan musa yana son yafi karfina ne ba halinsu daya da Jafar ba shi sam baya tsorona . Wai shi ya nuna min ya isa zaiyi dalilin saya mata wanan motar mai uban kudi ta hau ita din yar waye datafi sauran jikan tallakawa kawai. Lokacinne nafada dakin duk da kunne yaji hakan ina sallama cikin rawan baki ta dakatar da wayan tana min wani irin kaskantacen kallo tana jifana dashi. Har nakai tsakiyan dakin ta daka min wani uban tsawa daya sani kaduwa tana fadin ke ubanwa yace ki shigo min daki har nan kina ko da hankali kuwa zarah yadda yan uwana ke kirana ranan babu maamah din. Yi hakkuri mama bansan kina busy bane na fada a sanyayye zan juya na sake jin muryanta tana fadin uban mema ya kawo ki nane wai yanzu ? A,a mama dama nazo fada maki zancen motane shine bansan kina busy ba na shigo mota? motar banzan ku can dake da wan naki munafuki inba sakarcin shi ba komu yaga mun shiga irin motar nan ne a garin nan balleke zarah. Na dago kai na kalleta jin yadda take kiran sunana a ranan kai tsaye bayan ita ke fada a da can baya idan yan uwana suna tsokana na da Fatima zarah. Yau wai itace ke fadin haka kai tsaye da bakinta tana kallona a fusace tacigaba da fadin ina key din motar take na bata amsa nima da yana hannun ummah. Jeki zan karba na juya rai bace zan fita daga dakin naji tana fadin kada ki kara gigin shigo min daki daga yau idan kin fita kija min kofana ki kiramin Aisha ko Rukkaiya. Na amsa da to mama na fice mata dakinta tare da jawowa na samesu falo na fada masu sakonta kamar basuji ina magana ba don hakane nima banyi zancen motar dasu ba na fita. Ummah suna falo da yan uwana suna cin abinci na shigo sukuku kamar kwai ya fashe min a ciki kanina ke fadin wai anty zarah gobe ke zaki kaimu school cikin sabuwar motar ki ko ? Zama nayi saman kujera gefen ummah ina fadin kai khalid wace motar motar da mama tace ban isa shigarta ba karban key din zatayi hannun ummah. Karban key fa a hannuna aiko da rashin ta idon hjy maimuna yayi yawa Allah ya kawota tace in bata key din motar zata gane ba salman da nake ba yanzu gidan nan. A,a ummah ki bata tunda dama danta ya saya min kinga ai shike nan dama kafin na shiga naji tana waya da mama saratu tana fadin wai yaya musa munafukine yana son yafi karfinta gidan nan. Waini jikan talla, , , , sai kuma nayi shiru ummah tace ko baki fada ba nasan hakane dama duk bakin cikin ta ke nan a kaina ita din yar waye a garin nan banda Amadu sarkin teloli. Allah ya kawota karban key din nan taga tsiya zan shayar da ita mamaki sosai a gidan nan kuwa mukaji an turo kofan Rukkaiyace ta shigo tsatsaye dinta yadda take ba ladabi tana saye da wani dogon rigan body hook a jikin ta duk ya matseta ga mazaunan ta a fili irin shigan yan Lego's na rashi tarbiya da mutunci shine dabi,an su don ma su yaya na taka masu burkine wani lokaci. Duk idon mu yana kanta ba tare da gaida ummah ba take fadin wai mama tace ki ban key din motar da aka kawo dazun ? Jeki kice mata tazo da kanta ta dauka yana dakina wani kallo ta watsowa ummah din kamar zatayi magana sai kuma ta juya ta fice daga part din daga haka ummah bata kara magana ba sukaci gaba da cin abincin su. Saidai da gani kasan zuciyarta ba dadi a lokacin sosai don yadda fuskanta ya nuna a lokacin yanayin bacin raine karara a fuskan nata. Shiru shiru muna nan zaune muna dakon zuwan mama karban key bamu ganta ba sai ummah data dago kanta tana fadin ba zakici abinci bane ke kina zaune tun dazun. Nisawa nayi irin wanda ke nuna mutum ya shiga zurfin tunane a lokacin nake fadin na koshi ummah tace kin koshi me kikaci ko kin saka zancen nan a ranki ne ko ? To banson sha shanci don maganan nan ba taki bace idan baya kama kiyi ba ki zuba min ido dasu a gidan nan don haka tashi ki debi abinci kici yanzun nan. Kudin aljihunshi ya fitar gaban Dije ya sake lissafawa suna nan yadda suke aje din ya dago kai ya kalli Dije dake zaune ta zuba mai ido yace. Dije ga kudin yanzu yaya zamuyi dasu zamu tabane ko kuwa mu aje har mai akuyan nan yazo ya kama abinshi kafin muyi amfani dasu . Amadi akuya ai ya sayeta ya bamu kudin mu duk sanda ya dawo ga akuyanshi nan a daure ya kama abinshi ya tafi da ita meye namu a ciki yanzu tunda bamu muka sako mashi ita ta dawo nan ba. Nisawa yayi mai nauyi yace dana yanke shawaran zan fara sayen gwanjo ina sayarwa layi layi ranan da ba karatu ko kuma nayi sana,an awo ina shiga kauyu ka ina sayo hatsi ina kawowa nan na kafa dan table a kofan gidan nan ko yaya kika gani. Amadi kudin nan basu isanka wanan sana,an har buhu nawa kudin zai sayo maka da kake wanan zance kaidai fara gwanjon mu gani tukun abinda Allah zaiyi in yaso daga baya idan ubangiji yaima budi sai ka fara wanan din zaifi. To Allah yasa mu dace gobe kafin naje school da safe zanyi asubancin zuwa kasuwa na zabo masu kyau da zasuyi saukin saye na gwada in gani tace Allah yasa albarka a ciki ya amsa da Amin. Kwanon silver ya jawo wanda Dije ke saka mai abinci a ciki ya bude kanzone data gyara shi da ganye ya mike ya wanko hannunshi ya dawo dauke da ruwa cikin tsohon kofi ya zauna yana bissimillah ya fara ci yana tunane. Washegari tunda safe daga masallaci ya wuce kasuwa da kafa koda yaje ya samu an fara bude kaya hakan yasa ya zabo wanduna da riguna na maza ya nufo school dasu duk da yasan ba masayan fili a nan don zasuji kunyar saya. Amma shi ko a jikinshi ya kai wani wuri ya aje ya nufi department din su da sauri don yasan ya gama makara a ranan sai wadda Allah yayi zai samu shiga ajin safe. Ummah ni zan tafi na fada tana tsaye ta juyo tana fadin ba zaki dauki kannen naki bane ki saukesu school sun gama shiryawa fa ummah ta fada tana kallona. Nace Ummah aiba da motan zan fita ba tace don me ba zaki fita da ita ba ko ajewa zakiyi kina kallonta baki shiga ba don shiga aka saya maki ita ba. Wanan kuma yaya zanyi da ita sai na ajeta ummah na tambaya ina kallonta wanan ki bari har Abbah ku ya dawo saiya fadi hukuncin sa a kanta. Su fito mu tafi to na fada kin dauki key din motar ne a, a ban dauka ba kije gun drower mirro yana nan sama sai ki aje min wanan sin wurin. Na juya din na nufi dakin kwanan ummah na dauko na kuma aje mata wanan din na fito naci karo da kannena suna sauri kada in fita in barsu a gida. Tare muka tafi yiwa ummah dake hada miya a kitchen sallama tayi muna Allah ya tsare da fatan alheri a garemu ta kara da fadin in dinga kula Allah ya tsare ya kare na amsa da amin. Hayaniyar da yaran keyi na karadin shiga sabuwar mota yasa Aisha daga window dakin su tana kallon mu taga mun nufi wuri sabuwar motar kai tsaye mun bude mun shiga lokacin ta sake labulen ta juya da sauri zuwa fadawa mama abinda idonta ya gane mata din lokacin. Mama da sauri ta taso tana fadin yau ga yar iska yar banzan yarinya kawai wai ni zarah zata rainawa hankali watau nayi abinda zanyi suke nufi ita da uwarta ko ? Tana fita muna fita daga get din gidan namu sai kwalawa maigadi kira takeyi kada ya bude saboda dan tazaran dake akwai a wurin yasa maigadin baiji me take fadi ba sai kara wagale kofan dayayi muna na sauka na halba kan titi muka bacewa ganin su . Tsuki taja ta nufo shi da fada shima wurin ta yazo yana faduwa yake fadin ina kwana hjy baka da hankali ne ina kada ka bude kofan nan su fita ka bude mata au ya fada yana kallon kofan tare da fadin walle banji hakan ba hjy kimun afuwa don Allah. Tsuki taja ta nufi cikin gida da sauri part din mu ta nufa duk da Tani bata riga da tazo ba amma ko ina a gyare yake kamar ba yara a part din haka sai kamshi turaren wuta dake tashi a ciki. Tun daga kofa take kwalawa ummah kira tana fadin ina Salman take wai maimuna lafiya ummah ta fada kamar yadda ta kira sunan ta babu hjy itama lokacin haka ta kirata dashi gatsau. Maimuna mama ta fada cikin mamaki eh koba sunan ki ke nan ba ummah ta fada tana kallonta tana tsame hannunta da ruwa ya taba a kitchen da kyale. Lafiya kike min wanan kiran tsshin hankalin haka meke faruwane wai Rukkaiya bata zo nan ba jiya tace nace ki ban key din motan nan da aka kawo jiya. Wani kallo ummah tayi mata tana murmushi tace key din motan na maamah za,a baki idan zata fita sai ta tambayeki ke nan ko ko mulkin naki har yakai ki