Sashe 252
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
dabam dama ba kowa a wurinne zaman kadaici ya isheta shine tafito waje tasha iska don yan matanta sun tafi school a lokacin. Itako hjy yabi harara tabi bayanta dashi cikin kulewa kai kace ba ita bace ke sheka dariya yan mintunan da suka shege ta mayar da fuska tayi murtuk da ita a yanzu don jin da takeyi zuciyanta na mata suya. Karfe biyu da yan mintuna suka fito suka bar haraban gidan don dauriya harda hira take jan hjy murja din tana fadin kinga idan mukai wurin masu kayan fruit sai mu tsaya a saya mashi kada muje hannu sake a raina muna wayau. Hakan akayi don irin ledojin da hjy ta makare da kayan fruits din sai dai Allah ya taimaka don suna tayar da mota take fadin kinga wana namune ni daya ke daya wanan kuma sai mu kaiwa maishi. Sun samu mai jikin da sauki sun fito don basu tsaya ba saboda ba lokaci a hanya sun dan bar asibitin kamar ta tuno da wani abu tace uhumm, ummm a cikin mamaki. Hjy murja din tayi saurin juyowa tana kallonta tace bari ke dai murja zancen Alh na kwanaki na tuna dashi haka kawai ana zaune kalau zaka jajibo dan shege ka shigo muna dashi gida da sunan da. Wani Alh ke nan hjy murja dake zaune a takure ta tambaya tace keko murja Alh mu mana wanan dan nasa da yake son lakakawa kansa a yanzu mana. Ai,wanan zancen ne to amma hjy ai Alh ba jahili bane da zaiyi hakan da kike tunane tunda yace danshine dansane ke nan na sunna ko baya ai an taba maganan danko tunda har su yaya sunsan da zancen agida sunema ai sukaje wurin daurin auren shi wani lokaci. Au dama ke kinsan da zancen ke nan tun a gida itama kallota tayi kamar yadda ta kalleta tace hjy aiko kekin sani nima nasanda zancen balle ke. Dansane kawai don ko kamansu ai ya raba gardama amma kuma ni ban yarda cewa dan sunna bane kamar sauran yaya ta fada tana jan tsoki. Gashi ya fadi yadda sukai aure da mahaifiyar yaron a gaban ki kuma kowa yasanda haka toni ban yarda ba dama nasan bakin ku daya ai dasu . Meye nawa a ciki hjy banyi bakin ciki da dan kowa ba balle wanan da yake shi kadai a uwarshi don haka ni duk daya na daukesu ga baki dayansu yayan Alh ne. Bakaken magana sosai ta fadawa murja din haka suka kawo gida ran kowa a bace bata ko karasa fita daga motan ba ta figi motan ta juya ta bar gidan a fusace. Zaune nake ina rike da kwallon tumfafiyan dake hannuna ina dan juyashi a zahiri zaki dauka dan kwallon iccen nake kallo saidai a kasan zuciyana tunane nakeyi a lokacin. Ba komai nake tunane ba sai yan uwana da mahaifiyata tare da sauran yan uwa ina duban yadda zan haihu a nan babu kowa nawa a kusa dani duk da dije na tare damu amma ai dije bangaren miji take gareni. Cikin irin wanan yanayin na fado kan inna da yan matan ta zancensu da danta na tuna na tambayi kaina wai me inna take nufi danine haka ? A gaskiya dole in fito mata a mutum sak idan ba hakan ba tarihine zai maimaita kasan a iyalina yadda hjy tsohuwa bata kaunar mu haka abinda zan haifa zai taso inna na gwada masa bambaci a gaban kowa. Ba zance yadda uwana ke shan wuyan gidan miji ita da yayanta nima hakan zan iya fuskanta ba don irin kalaman da nakejin master na fadi a kaina duk da hannatu ta ban shawara da kada inyarda da dadin bakin namiji . Lokacin da namiji baida kudi komai yana iya fadi akan matarsa amma da zaran ya fara rike yan canji a lokacin ne wasa zai canza zai fito da kalanshi na gaskiya don haka kada ki sake ga baki daya zahra ki rike kimar ki a cikin tako don mace mataayi gareta. Nakan tsaya nayi tunane wanan maganan in kuma duba shawaran data bani a lokacin inda tace dani abu na farko zahra shine ki rike Allah fiye da komai kada ki yarda da hanyan masu bata. Don kina zagaye dasu ta ko ina zaki iya cewa kema sai kinyi abinda sukai maki kada ki yarda shedan ya rinjayi zuciyar ki ga hakan. Ki zamo mace mai kula da hakkin mijinki ako yaushe ta yarda zaki zamo mowar zuciyarsa bata gida ba kawai don akasari mowar gida na karfi da yajine wasu suke zama hakan. Nan ina nufin ki zamo mai son abinda yake so mai kaunan yan uwansa fiye dashi maj kula da arzikinshi fiye dashi mai damuwa da damuwarshi koda bada saninsa ba duk ki wanan. Sai kin hada da kula da hakkin makwabtaka dana abokansa da ma naduk yan uwa ko yana nan ko bayanan yazamo daya a wurin yan uwasa don watarana zasu fada masa alherin ki ko akasin hakan duk dai wanda kikai masu din. Ki kasa ki tsare gaba da baya na komai nasa ta inda zai rasa gaba ya rasa baya babu wani hanya da kike da rauni dai a gidan nasan kina da tsabta basai na tabo maki nan ba zaki iya wanan fannin amma dai ki kara kulawa kada ki gaza da hakan. Zahra zaki iya nasan zaki iya don ba yawan surutune dake ba amma ki kara kama bakinki akan sirim mijinki da kika sani da wanda kika gani harsai idan kinga zai kaucewa Allah nan kan kina da daman neman sharawa akan haka. Hannatu duk wanan a ina kika sansu ta kwashe da dariya kafin tace kin manta yawan gidajen dana zaunane zahra ina fa ganin komai kuma ina ji don ni yar garice na fiki shiga mutane sosai don haka nasan hakan. Zama na gyara tare da ajiyan zuciya ina lumshe idanuwana nace lalai hannatu tayi gaskiya ya zama dole in dauki shawaranki in fara nuna kaina a cikin dangin miji da nawa yan uwan yanzu.