Sashe 69
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ya fada a dan fusace sai yayan nasa yace ka barshi muji tukuna ai ya kalli Ahmed din don son jin me zai fada masu. Yace kimiya na karanta sana,a kuma saye da saye da sayarwa nakeyi ina shiga kauye ina sawo hatsi in kawo birni in sayar da sauran yan buga bugan zamani da akeyi. Tsaya nan ma hakan ya isa mun gamsu da baya nan ka baba sale ya fada yana gyara zaman shi Abbane ya dago yace. Kai banda abinka da wanan sana,an zaka rike min yata sana,an da ko kudin sabulunta a wata bai kai ba balle zancen sauran bukatan ta na rayuwa. Kai Ahmed din ya dago ya kalli Abba din dake magana ya sake dukarda kanshi kasa don zuciyar shi dake tausan shi saboda su mahaifan zarah din ne a lokacin. Da badon hakan ba yau da suka tayar mai da mikin dake damun zuciyar shi a kullun yana tausan kanshi da hakan yana jajircewa don gudun irin hakan gareshi na tozartawa. Muryan Abbane daya kira sunan shi ya katseshi Abban ke fadin Ahmed daga yau din nan ina son ka nisanci yata zarah a ko ina don yanzu dai nasan kasan cewa zarah ba sa,arka bace ita. Karatune kuma kagama kai yanzu din haka banson jin wani mu,amula kuma kota mutunci ya sake shiga tsakaninka da ita nan gaba zaka iya tafiya yanzu. Kuma kada naji ance ka sake kawo wani abu nan gidan da sunan alheri niko yaushe ina tsaye kan Iyalina ga komai don haka ka nisancesu . Ga wanan dubu hamsin ne ka kara a jarin ka ka kiyaye don ka zauna lafiya Abban ya fada yana kawar da kanshi gefe cikkn takaici. Kai Ahmed ya girgiza tare da fadin a,a Abba ka bar kudin ka nagode aikai mahaifine a gareni ko yanzu ka fadakar dani ga abndana manta cewa nidin mai raunine bai kamata na dinga kai kaina inda Allah bai kaini ba. Ya mike ya tsugunna tare da fadin zan koma nagode kwairai ga hakan yana fadin haka ya mike ya fice daga falon suka bishi da kallo kowa da abinda yake sakawa a zuciyan shi lokacin. Baba Salihu ne yace yaron yaron kirkine alama ya nuna hakan gareshi cewa zaiyi mutumci sosai wallahi saidai dan matsalan nan da aka samu kawai shine cikas din. Kirkin shi bai dameni ba ya rabu min da yata kawai shi nake so a yanzu itama zanyi warning din ta da kakausan murya kan hakan idan ba hakaba ranta zai baci dani sosai a gidan nan kaji na fada maka. Banso ka da hakan ba ana cizawa a hura don bamu san me Allah zaiyi nan gaba ba gara ka bita da addua kawai shine mafita nake gani. Shiru Abban yayi don takaici ya hashi yin magana sai can yace ita kuma shashan daya Aisha wai yaron nan dan kawar uwarta dake Lagos ta lakewa gashi sunja min zubar da mutuncina. Yau nayiwa uwarshi waya take fada min wai yaron bai yarda da hakan ba yace a barshi ya nemo matarshi idan ya tashi kaga ke nan dama a tsakanin uwayen nasu ne sukeson hadin shi kuma yaki. Ai kaji matsalan shiyasa nace ko wanan din kabisu sannu don alama ya nuna cewa suna son junan su saida sun kasa gane hakan suka tsaya a mutunci . Nan dai sukaita tataunawa kan yayan nasu har tsawon wani lokaci kafin Abba din suyi sallama da abokin haihuwan nasa yatafi shi kuma ya fara ganawa da mutanen shi yan maula. Ahmed ko da kyar yaga ya isa gida dakin shi ya shige ya kwanta don bacin rai don ko Djje bata sanda dawowan shi gidan ba lokacin. Ba abinda ke masa yawo a rai sai irin maganganun da Abba ya fada mai masu zafi daba wanda ya taba fada mai su a duniya sai yau saidai baiga laifin iyayyen nawa ba don shima yasa yakai kanshi inda Allah bai kaishi ba lokacin. Wayan shi yai kara ya dauko yana dubawa sunan zarah mayana ya gani a screen din wayan yaji kamar ya share wayan kada ya dauko don shara din Abban daya kidanya mashi. Saidai kuma ya kai hannu da zumar dauka wayan ya katse baikai ga dauka ba haka yasa ya juya ya barta da haskenta na kira kafin can ya sake jin kiran ya koma shigowa again. Wanan karon bai bari kiran ya katse ba ya daga yana fadin Zarah ya akayine daga bangarena nace bakazo gun Abba din bane halan naji banji komai ba. Dan murmushi yayi kafin yace nazo mana me kike son ji halan nace abinda yasa yake neman ka din mana brother don bansan me aka fada mashi ba akan mu. Yace nazo tayi min warning akan kada in kara tsayawa dake ko yaji an gamu tare duk abinda ya biyo baya nina ja yace min. Haba dai nasan Abba ba zai taba fadin hakan ba ai yace yako fada wallahi don iyakan gaskiyata ke nan na fada maki kinsan ban magana biyu ni ai. Yanzu Abba din ya fadama hakan don Allah yace kwarai kuwa don Abba yau yai min tuni ga abinda nina manta a rayuwana duk da ba soyayya mukeyi ba naji dadin maganan wani gefe kuma naji zafi. Don Abba ya fada min jarin hannuna ko sabulun wankanki ba zai saya ba don haka ya yanke duk wani alaka tsakanina dake daga yau kuma ya kafa shedan hakan ga dan uwanshi da muka zauna tare mu uku a falo naku. Kashe wayan nawa nayi domn kada yaji sautin kukan da yazo min a lokacin saidai abinda ban sani ba ya riga da yaji ko hakan yasa yai ta kiran layin nawa ban dauka ba. Don kukan dana rufe kaina a daki ni kadai a ciki inayi lokacin ina maijin zafin abinda Abba din ya fadawa Ahmed don ma bai fada min duka ba ke nan iya wanan din daya fada min ke nan. Twelve misscal nasa na daga waya na gani bayan sallah isha,i danayi na dauko wayan ina duba kiran inda na samu sakonshi cewa don Allah in kirashi idan naga sakon shi. Ban kiba na danna kiran rayin shi ya shiga ya daga ya dauka yana fadin yanzun kin sauko ke nan ko kada wanan maganan ya bata maki rai don Allah. Ni nasan ke din ko Abba bai fada ba keba sa,ata bace zarah don haka muyi hakkuri mu guji abinda zai iya kai ya komo daga hakan. Dama ashe ba sona kakeyi da gaskiya ba nafada a cikin wani murya ina sake kuka lokaci guda naci gaba da fadin ni tunda ummah tayi muna adduan daidaituwa a tsakanin mu naji zuciyana ya kwanta da hakan. Zarah dama kema kina sona ashe kamar yadda nima nake son ki ashe bansan da son juna mukeyi ba sai yau da Abba din yake furta kalman raba tsakanin mu dake.